← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 81

Sashe 44

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Inna gida na koma na ga Fauziya ba ta nan, na je gidansu da niyyar tambayarsu sai mahaifinta ya tambaye ni ya take, kin ga kenan ba ta je can ba. Ga shi dama ba ta tambaye ni ba, ban san inda ta tafi ba."
Kabir ya ƙarasa maganar yana zubar da ƙwallah. Wani takaici ne ya maƙure ziciyar Inna, ta dube shi a wulaƙance tana sakin dogon tsaki ta ce. "Mttssswww amma dai Kabiru ka yi asara wallahi, yanzu a kan mace kake zubar da ƙwalla? Ashe abin da ake faɗa gaskiya ne, yarinyar nan ta gama wanke hannu a kanka."

Inna ta koma bakin gado ta zauna ta cigaba da cewa, "Yo wai ma Fauziyar yarinya ce? Da za ta fice har ka dinga neman saboda ta ka ganÉ—ma lalacewa"

Cikin damuwa Kabir ya ce, "Wallahi Inna ni ne da laifi, ni na ɓa ta mata rai, duk macen da ta ga abin da na yi fiye da haka ma za ta iya aikatawa."
"To ai sai ka yi ta yi tun da wahala ta aure ka, yanzu kuma a ina ta bar yaran?"
Kabir ya ce, "Suna É—akin matar gidanmu."

"Amma wannan yarinya an yi baƙar munafika, haka kawai ina zaune ƙalau ta ɗaga mini hankali. Sai ka fita ka kai cigiyarta gidan radiyo, tun da lalacewarka ta kai haka." Daga haka ta saka hijabinta ta tayar da sallah. Kabir da ya lura zamansa a wurin Inna ba mafita zai kawo masa ba, sai ya miƙe ya fice. Kasancewar Sadiya ta ji duk abin da yake faɗa, sai ta tsayar da Kabir tana tambayarsa. A nan ya zayyane mata duk abin da ya faru, duk da bai fito ya faɗa mata laifin da ya aikata ba. Shiru ta yi tana nazari, amma har cikin ranta take ji Kabir ne bai kyautawa Fauziya ba, domin ta san tana da haƙurin gaske. Saboda damuwa Kabir haka ya dinga takawa a ƙafa, yana tafe yana jimamin halin da take ciki da tsohon ciki a wannan lokacin. A haka har ya ƙarasa gida.

Tun lokacin da Fauziya ta tashi daga bacci ta ji mararta da bayanta suna ciwo, don haka ta yanke shawarar zuwa asibiti. A ranta tana fatan koda haihuwar ce ta zo mata, tana fatan ta kasance silar tafiyarta lahira. Duk haihuwa ukun da ta yi Kabir ne yake kai ta asibiti, daga baya kuma sai ya kira matar mahaifinta ya sanar da ita idan sun je. Amma da yake zuciyarta a cunkushe take da haushin Kabir, ya sa ta ɗauki duk wani kaya da za a buƙata a asibiti. Ta ƙi sanar da Lawisa ne, saboda ta san idan suka tafi ita da Lawisa asibiti babu a inda su Na'ima za su zauna ballantana su ci abinci.
Sai da ta fara biyawa ta gidan Dillaliya ta roƙe ta, da ta ba wani abin daga cikin cikon kuɗin firji, bayan ta karɓi kuɗin ta fice daga gidan.
Fauziya ba ta damu da kallon da mutane suke yi mata ba, tana tafe tana hawaye haka ta dinga tafiyar ƙafa domin ya taimaka mata wurin samun saurin naƙuda. Ta yi tafiya mai nisa sannan ta samu adaidaita sahu ya kai ta asibiti, a lokacin da ta je asibiti ana duba ta aka ga tana 5cm. Wayarta ta ciro ta fara kiran ƙanwarta da suke uba ɗaya ba ta same ta ba, ta kira ta matar babanta ita ma a kashe. Na'ima ba ita ta haihu ba sai bayan sallar magriba, ta haifo jaririyar 'yarta mace kyakkayawa mai kama sak da Kabir.
Ido ta ƙurawa jaririyar tana kallo, saboda tsananin kamar da suke yi da mahaifinta. Wani irin takaici ya kamata sai kawai ta fashe da gunjin kuka, Midwife ɗin da ke gefe ta dafa ta ta ce.

"Maman baby kukan kuma na mene ne? Ai farinciki ya kamata ki yi, tun da Allah Ya raba ku lafiya." Murmunshin yaƙe Fauziya ta yi, sannan ta ciro wayarta ta sake kiran lambar ƙanwarta Shukura. A wannan karon ta ci sa'a an ɗauka, a nan ta sanar da ita asibitin da take. Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba Shukura ta ƙarasa asibitin, bayan an gama duba ta da jaririyarta aka sallame ta suka wuce gida.

Lokacin da Fauziya ta yi sallama da gudu yaranta suka fito daga É—akin Lawisa suna faÉ—in.
"Mami oyoyo."
Turus! Lawisa ta yi ganin Shukra tana rungume da jaririyar Fauziya, tsalle Lawisa ta buga ta ƙarasa gabanta ta ce.

"Wai dama matar nan abin da kika fita kenan? A gaskiya kin shammace ni Maman Na'ima, shi ma kuma Abban Na'ima abin ka da namiji bai ce mini haihuwa kika fita ba.
Barka-barka uwar 'yan'mata, In Shaa Allahu matar gwamna kika haifo mana." Fauziya ta saki murmushi, tana shirin shiga É—aki su A'ilo suka fito suka yi mata barka sama-sama kowacce tana yamutsa fuska.
Sai da Shukura ta yi mata ɗan abin da ba a rasa ba, sannan ta wuce gida. Kafin wani lokaci tuni Lawisa ta ɗora mata ruwan wanka, sai da ta surka mata sannan ta karɓi jaririyar ita kuma Fauziya ta shiga wanka. Bayan Fauziya ta gama Lawisa ta haɗa mata ruwan shayi ruwan bunu. Karamcin da Lawisa ta yi mata ya sa ta dinga zabga mata godiya, har sai da Lawisan ta nuna ɓacin ranta. Sai da ta yi wa su Na'ima shimfiɗa, ta tambayi Fauziya ko akwai abin da za a yi mata ta ce a'a, sannan Lawisa ta yi mata sallama ta tafi ɗakinta.

Lokacin da Kabir ya shiga gidan hango ɗakin ta ya yi a kunne da fitila, wanda hakan ne ya ba shi tabbacin ta dawo gidan. Ƙafarsa har harɗewa take saboda sauri, a haka ya faɗa ɗakin. A zaune ya same ta jingine da gado, yanayin fuskarta babu yabo babu fallasa. A fili Kabir ya sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, saboda farinciki kamar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha.
Fauziya yi ta yi kamar ba ta gan shi ba, sai dai kallo ɗayan da ta yi masa ta fahimci duk ya fita a kamanninsa. Ƙafafuwansa sun yi futu-futu kamar wanda aka tuno daga rami, a gefenta ya zaune murya a raunane ya ce.

"Fauziya!"

Ido ta zuba masa tana kallo sai dai ba ta amsa masa ba, ya riƙo hannunta a sanyaye ya ce.
"Hankalina ba ƙaramin tashi ya yi ba da na dawo na ga ba kya gidan nan, don girman Allah ki yi haƙuri ki saurare ni. Na san na yi kuskure amma don Allah ki yafe mini."
Ajiyar zuciya Fauziya ta sauke tana janye hannunta daga cikin nasa ta ce, "Da a ce ban yafe maka ba, da fitar da na yi ba zan sake tsoma ƙafata a cikin gidan nan ba."

Lumshe ido ya yi cikin farinciki ya ce, "Wallahi wannan yarinyar da kika ga maganarmu ban jima da haɗuwa da ita ba, kuma kin san akwai shaiɗanun mata da suke jan hankali maza. Wannan ne nan farko da ƙarshe, In Shaa Allahu haka ba za ta sake faruwa ba..."

"Wannan ba damuwa ta ba ce Kabiru! Amma ka sani, ka zabtare kaso casa'in da tara na daga cikin yarda, ƙauna da amincin da na damƙa maka. Ka shayar da ni ruwan mamaki Kabir, mamakin da har zuwa numfashina na ƙarshe ba zan daina yin sa ba. A kullum ina son ka dinga tunawa, kai ma uba ne. Uban 'ya'ya matan da kake yunƙurin ɓa ta tarbiyyar 'yar mutane."
Shiru Kabir ya yi yana jin kalamanta suna ratsa shi, ko babu komai ya ji daÉ—i da ta furzo abin da yake cikin zuciyarta. Ya sake marairaicewa ya ce, "Duk abin da kika faÉ—a haka ne, In Shaa Allahu zan kiyaye. Amma don Allah ki daina fushi da ni, wallahi fushinki shi ne abin da ya fi komai É—aga mini hankali."

Kabir ya faɗa yana jiran amsarta, kukan jaririya ya ji a bayanta. Fauziya ta juya ta ɗauko ta tana yunƙurin ba ta mama, wani irin abu ne ya tsarga masa kamar wanda aka yi wa shocking. Da wata irin murya cike da ruɗewa ya ce, "Wai dama kin haihu Fauzina?" Fauzina da ta ji ya faɗa ya sa kalmar ta ƙara ba ta mata rai, ta tuno boyis ɗin da ta saurara wanda ya yi wa Hafsa da ta ji yana cewa, duk duniya bai taɓa yi wa kowacce mace soyayyar da yake yi mata ba. Ganin ba ta za ta ba shi amsa ba, ya sa shi saurin karɓar jaririyar ya rungume a ƙirjinsa.

Kamar mutum-mutumi haka Maman Nana ta daskare a tsaye tana kallon Jafar har ya shige ɗaki, ita abin ma mamaki ya ba ta. Domin tun da suka yi aure ba ta taɓa amfani da gawayi ba, duk da a shekarun baya ƙarfin Jafar bai kai na yanzu ba. Rufa masa baya ta yi cikin ɗakin, yana ganin haka ya sake haɗe fuska.

"Abban Nana wai me yake faruwa? Me ya sa kake son cusguna mini? Me na yi maka duk ka canza kake ƙaƙalo abin da za ka cusguna mini?"
Maman Nana ta yi maganar muryarta tana rawa.

"Me kuma na yi miki?"

"Amma clinder fa ka É—auke mini ka kawo buhunhunan gawayi ka ajiye mini."
Sai da ya É—aura towel É—in wankansa sannan ya ce.

"Su waɗanda suke amfani da gawayin mutuwa suka yi? Ko kuma taɓo ya yi musu a goshi? Am sorry to say na ga ke gidanku ma da itace suka amfani." Saukar kalaman Jafar a kunnenta ji ta yi tamkar an buga mata guduma. Maman Nana ta haɗiyi wani irin abu mai ɗaci a zuciyarta, idonta ya ciko da ƙwalla.

"Gori za ka yi mini Abban Nana? Ko dai ka daina ƙaunata ne? Wane ne yake zuga ka a kan iyalinka ne?"

Jafar ya matsi toothpaste kamar ba zai tanka mata ba, sai da ya je bakin ƙofa ya waiga ya ce.
"Babu ɗaya daga ciki, kawai ke kika yi zargin haka. Yanzun ba ni da ƙarfin saka gas ne..."
Chapter 44 · 0% Book details