← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 81

Sashe 53

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga wannan ranar zaman Fauziya da Inna ya fara ɗaukan sabon salo, sai dai Fauziya tana bakin ƙoƙarinta don ganin wani abu bai haɗo su ba. Duk safiya idan ta yi abinci tana bakin ƙoƙarinta, don ta ga ta ba wa su Zainabu abinci ko yaya ne duk da ciyarwarsu ta koma hannun Inna kacokam.
Kwana biyu da tafiyar Sadiya, har gida Yaya Tas'u ya zo ya ƙarewa Yaya Nura faɗa a kan sakin da ya yi wa Sadiya. Don wani lokacin idan suka yi faɗa tana zuwa ta kai ƙararsa wurinsa, shi kuma sai ya je ya yi masa faɗa. Idan aka yi haka sai Sadiya ta samu sassaucin rashin mutumcinsa, bayan kwana biyu kuma ya ɗora daga inda ya tsaya.

Duk aikin da Sadiya take yi wa Inno sannu a hankali ya dinga dawowa kan Fauziya, lokaci ɗaya ta yi wani irin duhu ga rashin hutu daga wannan sai wannan. Murmurewar jegon da ta yi duk sai ta zuge, a ɓangare ɗaya ga tunanin halin da gininsu yake ciki. Saboda halayen Kabir sun dawo mata sababbi, don tana yi masa magana yake rufe ta da faɗa. Idan Inna ta jiyo sai ta ƙarasa bakin ƙofa ita ma ta cigaba da tofa albarkacin bakinta.
Babban abin da ya fi ɗaga mata hankali, bai wuce yadda ta lura da take-taken Inna tana son fara ɗora wa su Na'ima talla ba. Duk da ba ta fito ta faɗa ba, amma ta lura da yanayin shaguɓen da take yi. Hakan ne ya sa ta shiga takura wa Kabir a kan ya saka su a makaranta, amma sai dai ya ce mata ba shi da kuɗi. Kuma ta rasa wurin da yake zuwa, a kullum ya dawo gida da wuri haka zai buga wankan ƙananan kaya ko manya ya fice daga gidan. Wani lokacin ma sai ta yi bacci yake dawowa, saboda gajiya ta sa ana yin sallar Isha'i take yin bacci.
Watarana suna zaune bayan magriba yana tsaka da shiri ta ce.

"Abban Na'ima!"

"Ina jin ki."

Ya amsa mata yana saka belt É—in wandonsa.

"Wai kasuwar É—inkin ce yanzu ba a samu ko yaya? Zaman yaran nan babu makaranta baya zai mayar da su, don Allah ko Islamiya ce ka saka su."
Sai da ya ƙarasa komai sannan ya ce, "Islamiyyar ma ai ba kyauta ake zuwa ba, ki bari idan na samu kuɗi zan saka su. Kin san dai yadda abubuwa suke ƙara tsada."
Saboda takaici ba ta tanka masa ba, ya gama shiryawa yana fesa turare, a daidai lokacin wayarsa ta kawo haske da yake a silent take. Da sauri ya É—auke wayar ya saka a aljihu har zai fita Fauziya ta ce, "Abban Na'ima ni fa ban gane wannan shige da ficen nan da kake yi ba. Ina za ka je ne da daren nan?"

"Haifata kika yi da za ki tsare ni da tambaya, ina ruwanki da wurin da za ni? Kin san dai yanzu na daina shaye-shaye ballanta ki kafa mini zargi."
Sai kawai ya saka kai ya fice daga É—akin, shiru Fauziya ta yi tana nazari.
"Tabbas ruwa ba ya tsami banza, wallahi akwai abin da Abban Na'ima yake ƙullawa." Ta faɗa a sanyaye, tana jin nadamar ba shi kekenta. Saboda ta san da ko da kuɗin gyaran da take yi ne za ta iya samu ta biya musu kuɗin makaranta, a nan take tunani ya faɗo mata a kan ta fara yin wankau tun da yanzu Sadiya ba ta nan. Sai kuma ta ga sam ba za ta iya wankau ba, don wani lokacin ko wankin yaranta ta yi wuni take bayanta yana ciwo. Sai kuma dabara ta faɗo mata a kan ta fara yin kitso, da wannan shawarar ta bar wa zuciyarta a kan idan gari ya waye za ta shiga maƙota duk ta faɗa musu.

Kabir yana fita daga gidan ya ciro wayarsa ya latsa lambar Surayya yana faÉ—in, "Na fito fa baby."
Surayya ta akashe murya ta ce, "Tun É—azu fa nake ciki da muradin son ganinka gwarzona."
Amsa mata ya yi sannan ya kashe wayar. Adaidaita sahu ya tara kai tsaye ya wuce unguwarsu Surry, waya ya ciro ya kira ta sannan ta fito. Kamar kullum idan za su yi zance a soron gidan suke yi, hakan ce ta sa yanzu ma ta shimfiÉ—a musu dadduma a soro.
Rungumo Surayya ya yi, ita kuma ta kamo bakinsa ta fara sakar masa kiss. Nan take Kabir ya fara birkice mata, ya shiga kai hannunsa cikin sassan jikinta. Jingina suka yi da bango, ita ma Surry ta fara sarrafa shi da hannunta tamkar ƙwararriyar matar aure.

"Baby na gaji fa!"
Kabir ya furta cikin wani irin yanayi.
"Kamar yau ne fa, ba yanzu saura wata goma ba. Ni fa ba don 'yan gidanmu ba, da ko ba lefe tsaf za a sha biki. Don tun lokacin da aka tsayar da rana na so a saka wata shida."

Janye kansa ya yi daga cikin ƙirjinta ya ɗago yana kai hannunsa ciki jikinta sannan ya ce, "Amma kafin lokacin me ya sa ba za ki ɗan dinga rage mini zafi ba dear?"

Surry don ta zolaye shi sai ta ce, "Ba kana da mata ba, ya kake abu kamar wanda bai taɓa aure ba."

"Mtswww."
Ta ji Kabir ya ja dogon tsaki sannan ya ce, "Ana maganar matan da suka cika cikakkun mata, kina sako mini zancan waccan abar. Don Allah ki taimaka mu dinga zuwa gidan can kina yi mini dabaru." Wani irin daɗi Surry ta ji, saboda ta jima da fahimtar matarsa ba komai ba ce a wurinsa. Ta sake maƙale shi ta ce.
"Shi kenan my love, zan yi ƙoƙari na dinga yi wa su Yaya dabarar fita, kasan tun da aka saka ranarmu yake saka mini ido sosai."
Sake haÉ—e bakinsu Kabir ya yi sai da suka ji alamar motsin za a fito, da sauri ya sake ta yana sauke numfashi, Surry ta wayance da cewa.

"Hasko nan mu ga ko can azurfar taka ta yi."

Wayarsa ya zaro ya fara haska mata, kamar masu neman azurfar gaske. Suna cikin haka Yaya Umar ya yi musu sallama ya fita daga gidan. Ya so sake yamutsa Surry ta nuna masa ya yi haƙuri za ta dinga zuwa can gidan, saboda tana tsoron kada yayanta ya sake dawowa ya kama su.

Cike da kewar Surry Kabir ya fito daga soron gidan, yana fitowa babu jimawa ya zaro wayarsa. Misscall É—in Farha ya gani har sau uku, ya latsa layin nata yana karawa a kunne ya ce.
"Ina fatan sarauniya ba ta yi fushi da ni da."

"Idan na yi ma ai ka saba kanainaye zuciyata har ta yi maka afuwa."
Farha ta furta cikin shagwaɓa. Murmushi ya yi yana jinjina baiwar da yake da ita. Kabir irin mazan nan ne masu iya tsara zance da kanainaye zuciyar 'yanmata. Ya ƙwarai sosai wurin iya yaudara da kife mace, kuma yana ɗaya daga cikin maza masu kule-kule da ƙoƙarin dandanlar arzikin jikin budurwa.

"To yanzu dai ayi mini afuwa cajina ya ƙare, zan kira ki da asuba. Ina fatan za ki yi bacci da ni a zuciyarki."
Kafin su yi sallama sai da suka yi musayar kalaman soyayya sannan ya katse.
Lokacin da ya ƙarasa gida tuni Fauziya ta yi bacci, don haka ya ɗauki buta ya faɗa banɗaki ya tsarkake jikinsa sannan ya koma ɗaki.

Sannu a hankali haka rayuwa ta cigaba da tafiya watanni suna shuɗewa, Fauziya ta fara kitso babu laifi tana samun ɗan kuɗin kashewa. Da kanta ta saka yaran a wata makaranta da ake yi boko da Islamiyya, sai dai duk da hakan ba su tsira ba sai da Inna ta fara ɗora musu tallar barkono ranar Alhamis da Juma'a. Tun Fauziya tana kara har ta gagara haƙuri ta yi wa Inna magana, a lokacin faɗa ta rife ta da shi amma da shi ma Kabir ya nuna yaransa ba za su yi talla ba sai ta kawo ido ta saka masa. Fauziya da karanbami har magana ta yi a kan su Salim, a nan ne Inna ta ce daga Kabir har ita ba su isa ba matuƙar ba mahaifinsu ne ya hana ba. Wannan dalilin ne ya ja wa Fauziya da yaranta baƙin jini a wurin Inna, ko fita suka yi tsakar gida wasa ta dinga zaginsu tana hantarasu wani lokacin har da duka.
Daga ɓangaren Kabir shi ma zamansa da ita tuni ya sauya salo, don babu abin da za ta yi masa haka kawai zai ɗauki fushi da ita. Ko kuma magana kaɗan za ta yi masa sai ya rufe ta da faɗa, daga haka ma sai ya ƙaurace mata. Domin a zaman da suke yi sun tafi kusan wata biyu ba tare da wani abu ya gifta a tsakaninsu ba.

Ana cikin haka watarana Kabir ya dawo da daddare a lokacin sha ɗaya saura, a zaune ya samu Fauziya ta yi shiru tana nazari. Tsakin da ya ja ne ya sa ta ɗago tana kallonsa, karaf idonta ya sauka a kan damɓareren jambakin da ke gaban rigarsa har zuwa leɓensa. Ta haɗiyi wani irin yawun takaici, amma ba ta tanka masa. Kamar yadda ta yi tsammani, buta ta ga ya ɗauka ya tafi banɗaki. Ba tun ranar ba, dama ta lura da shi kusan kullum idan ya dawo ya yi wanka ya fita, to bayan ya sake dawowa daga yawonsa sai ta ji ya ɗebi ruwa yana wanka. Ya tafi banɗaki ba jimawa ta ji kira ya shigo wayarsa, a kan windo ta hango wayar jikinta har rawa yake ta saka hannu ta ɗauka. Wannan ce rana ta farko da zuciya ta ingizata a kan ta ɗauki wayarsa, ƙirjinta yana bugu ta ɗauki kiran da ta ga an ributa 'Sec wf' Ɗauka ta yi sai ta yi shiru daga can ɓangaren ta ji an ce.
Chapter 53 · 0% Book details