← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 81

Sashe 23

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin muryar bacci Baba malam ya ce, "Eh suna nan ya aka yi?" Ƙit Daddy ya kashe wayar, ya ɗauko mukullin motarsa da ke kan mudubi da sauri Shukura ta sha gabansa ta ce.

"Wai ina za ka je da tsohon daren nan?"

"Zan je na É—auko iyalina." Daddy ya ba ta amsa.

"Kutumar...! Saboda waccan tsohuwar kilakin za ka fita a tsohon daren nan? Ko ka manta yanzu babu aurenka a kanta? To ko kuma zaman dandi za ku fara..."

Tass! Daddy ya wanke fuskarta da mari, cikin ɓacin rai ya ce.
"Idan kika sake cewa matata tsohuwar kilaki wallahi sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Daga haka Daddy ya fice, ya nufi harabar gidan ya ɗauki mota ya fita.

Hankali a tashe Shukura ta ɗauko waya ta latsa lambar Inna ta kira, daga can ɓangaren ta ji muryar mahaifiyarta cikin bacci ta ɗauka. Kuka da fashe da shi, hankali a tashe Inna ta ce.

"Ke Shukura lafiya, ko jikin ne? Ina Alhajin yake?"

"Inna aikin nan fa ina zargin ya karye."

Shukura ta furta cikin kuka, Inna da ba ta fahimci komai ba ta ce.
"Aikin me kuma?"

"Asirin da muka yi wa Baby da Hajiya Karima mana, yanzu haka ya fice wai zai tafi dawo da ita gidan nan. Da na yi magana fa har da marina." Shukura ta ƙarasa maganar cikin kuka, nan take Inna ta wartsake ta ce.

"Shukura an ya ba mafarki kika yi ba? Kin tabbatar da gaske ne?"

"Wallahi ba mafarki ba ne Inna."

"Ai kuwa mun shiga uku, wallahi zama bai ganmu ba. Bari zuwa safiya zan zo gidan." Inna ta faÉ—a cikin kwantar wa da Shukura hankali.
A wannan lokacin haka ta zauna jigum, ta shiga tunanin nemawar kanta mafita. Don ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba.

ALHAJI UMAR
Daddy gudu yake yi tun iya ƙarfinsa kamar zai tashi sama, duk hanyar da ya bi idan jami'an tsaro suka tsayar da shi sai dai ya ce musu emergancy ne ya fito da shi ɗansa babu lafiya. Da an duba boot ɗinsa da cikin motar idan aka ga babu komai, sai a bar shi ya wuce.
Yana zuwa ƙofar gidan Baba malam ya fara horn da ƙarfi, securities ne suka leƙo suka gan shi. Sai dai saboda tsaro ya sa ba su buɗe masa ba, ɗaya daga ciki ya nufi cikin gida yana ɗan bubbuga ƙofar. Da yake tun tashin Baba Malam da Daddy ya yi idonsa biyu, sai ya fito ya tambayi masu gadin. Yana jin an ce masa Daddy ne ya ce a buɗe masa gidan ya shiga, kamar wanda yake jira ana buɗewa Daddy ƙofa ya kunno hancin motarsa cikin gidan. Ko ƙarasa fakin bai yi ba ya fito ya nufi hanyar shiga cikin gidan, a bakin baranda ya samu Baba Malam a tsaye. Cikin tashin hankali ya ce.

"Sannu da dare Baba malam, dama zuwa na yi na tafi da Karima."

"Wace ce Karima?"

Baba malam ya wurga masa tambaya fuska a haÉ—e.

GIDAN HAFIZ

Kamar yadda suka tsara Hafiz yana tashi daga kasuwa gidansu Bilkisu ya ƙarasa, mahaifinta dattijon arziki ne. Tarba mai kyau ya sa aka shirya musu kamar yadda ya saba duk shekara, sai da suka ci suka sha suka yi ƙat wurin sallar Isha'i sannan ya ɗauko Bilkisu suka taho gida.
A lokacin da suka ƙarasa Amina tana zaune da su Sayyada a ɗakinta, yaran suna ta wasansu a junansu amma kallo ɗaya za ka yi wa Amina ka fahimci tana cikin damuwa. Saboda ɓacin rai ko da aka sha ruwa ba ta iya cin abincin kirki ba, ruwa kawai ta sha sai baƙin shayi. Tana zaune ta ji sallamarsu Hafiz, dariyar Bilkisu ta ji tana faɗin.

"Haba kai kuwa Baby, ai dole kowaye ya ji daɗin abin da ka yi wa su Baba, Allah dai ya bar ƙauna a tsakaninmu."
Zuciyar Hafiz É—aya ya amsa da Amin, saboda shi ya yi tsammanin zuwansa shan ruwa gidan take nufi. Yaran suna jin muryar iyayensu suka fito a kuje suna yi musu oyoyo, rungume su Hafiz da Bilkisu suka yi. Sannan Hafiz ya ce.

"Ina Auntynku ko tana cikin É—aki."

Sayyid ya gyaÉ—a kai ya ce.
"Amma Aunty ba ta ci abinci ba, ruwa kawai ta sha." Da sauri Hafiz ya ce.

"Kul, wa ya tambaye ka? Ba na son faÉ—ar abin da ba a tambaye ka ba, koda wasa kada na sake ji."
Daga haka ya É—aga labulen É—akin Amina ya shiga. Ita kuma Bilkisu ta ja hannun yaranta suka wuce É—aki.

"Maman baby barka da hutawa." Hafiz ya faÉ—a yana zama a gefenta, haÉ—e da É—ora hanunsa a kan cikinta. ÆŠauke kanta gefe ta yi ta ce.
"Barka."

"Ko wani abu ne yake damunki?" Ya sake tambayarta.
Girgiza masa kai ta yi, sai ya saki murmushi ya ce.

"To a kawo mini abinci Gimbiya, kin san cewa na yi ba zan cika cikina ba sai na dawo gida na ci naki."

"Ka kuwa yi wa kanka, don ni ban yi girki da ku ba. Tun da ka je gidan neman suna ai sai ka ci a can, sai dai kuma idan na sahur za ka jira."
Amina ta yi maganar cikin fushi, da mamaki yake kallonta ya ce.

"Ni kike faÉ—a wa haka Amina? Laifi ne don mahaifin Bilkisu ya gayyace ni shan ruwa? Kada ki manta koda ba Bilkisu nake aure ba, yana iya gayyatata tun da mahaifinta abokin mahaifina ne."

"Ni wani abin na ce maka? Ko ka ji na yi maganar alaƙarka da ta mahaifinsu? Tun da dama ai da manufa a zuwan naka, wallahi duk abin da mutum yake yi Allah yana kallo."
Amina ta ƙarasa maganar tana hawaye. Ransa ne ya fara ɓaci, amma ba ya san abin da zai kai ga ya biye mata don haka ya kwantar da murya ya ce.
"Wai me ya sa kike yin haka Amina, ba fa yau mahaifin Bilkisu ya saba gayyatarmu ba. Don Allah kada wannan ya ɗaga miki hankali." A sheƙe Amina ta dube shi cike da takaici ta ce.

"Wallahi bari ka ji Hafiz, Allah É—aya za ka ce mini na yarda. Amma wallahi duk abin da kake faÉ—a sai dai na kalle ka, wai ni za ku yi wa bariki. Ai ita da yake matar so ce, kuma ana mutumta iyayenta ana daraja su ga shi nan ka narka iyayen kuÉ—i ka yi sayayya ka ba ta; ta kai gidansu. Ni kuwa da ke ba ka É—auki iyayena da mutumci ba ko biyar ba ka ba ni ba, ai maganina kenan da na tambaye ka. Amma wallahi ka yi da 'yar halak, In Shaa Allahu tsinke na daina tambayarka." Tana gama faÉ—a ta fashe da kuka tana shigewa É—aki.
Da mamaki ya bi bayanta da kallo, shi kaÉ—ai ya shiga nazari don gabaÉ—aya bai gane abin da take nufi ba. Jin kukanta yake har cikin ransa, har ya yi biris da ita sai ya ji ba zai daure ba, don haka ya shiga cikin É—akin. Janyo ta ya yi jikinta ya ji zafi zau, cikin damuwa ya ce.

"Haba Amina, ya ina yabonki sallah za ki kasa alwala. Don Allah me ya sa kike son É—aga mini hankali muna zaune lafiya ni da ke." Amina ta goge hawayen idonta ta ce.
"Dole ka ce zan ɗaga maka hankali mana Hafiz saboda ba ka ƙaunata, ai dama ba za ka ga rashin adalcin da kake yi ba. Dubi uban buhun kayan da ka turo wa Bilkisu ɗazu, ka ce ta kai gidansu na shan ruwa wai har da ɗan sahu ka turo a kai ta. Ni kuwa idan zan mutu da ciwo, idan za ni asibiti haka zan tafi na tari adaidaiata sahu a hanya." Tana gama faɗa ta ƙara rushewa da kuka. Shiru ya yi yana nazari, da sauri ya miƙe tsaye har zai fita ya dawo ya ce.

"Ni aka ce na aiko da buhun kayan shan ruwa?"

"Zan yi maka sharri ne? Wai Hafiz ni za ka mayar 'yar iska da ban san me nake yi ba?" Amina ta furta cikin fushi, jinjina kai ya yi ya ce.
"Ta so mu je ina son yin magana da ku." Kamar Amina ba za ta miƙe ba, sai ta yunƙura ta tashi da ƙyar.

Kai tsaye É—akin Amina suka shiga, a lokacin ta gama yi wa yara shimfiÉ—a a É—akinsu ta koma É—akinta. Tana ganinsu a cikin ranta ta ce, 'Ai na san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya.'
Amma a fili sai ta ce. "Abban Sayyid kune?"

"Mune Bilkisu, zo ki zauna."

Zama Bilkisu ta yi, Amina da fuskarta ta kumbura suntum saboda kuka ita ma ta zauna tana wurga musu mugun kallo. Hafiz ya dubi Amina ya ce, "Maimaita abin da kika faÉ—a mini." Tiryan-tiryan Amina ta sake faÉ—ar abin da ta faÉ—a masa, ya É—ago ya dubi Bilkisu ya ce.

"Bikisu ni da ke mun yi magana, a kan na aiko miki da kayan shan ruwa?"
Bilkisu ta yamutsa fuska ta ce, "To dama ni na ce kai ka aiko ne, ke Amina hawainiyarki ta kiyayi rama ta. Sharri za ki yi mini ko haÉ—a ni faÉ—a za ki yi da mijina?" Kafin Amina ta yi magana Hafiz ya ce.

"Ya isa haka."

Waya ya zaro ya latsa lambar mahaifin Bilkisu, cikin girmamawa suka gaisa ya yi masa ban gajiya. Hafiz ya numfasa ya ce.
"Baba don Allah wata tambaya gare ni, amma ba wani abu ba ne." Baba ya ce. "Yi tambayarka Hafizu."

"Baba don Allah yau Amina ta kawo maka kayan shan ruwa ne?"
Hafiz ya tambaya yana kallon yanayin Bilkisu da ta yi zuru-zuru. Baba ya ce.
"Eh ta kawo mini kaya masu yawa, ta ce mini yayansu ne ya ba su kuɗi da kaya shi ne ta sayo ta kawo mini. Amma wani abu ne ya faru Hafizu?" Cikin girmamwa Hafiz ya ce, "A'a Baba, wata tattaunawa muke yi da ita ne. Na gode sosai Allah Yaa ƙara girma." Baba ya amsa sannan suka yi sallama. Da mamaki Hafiz da Amina suka dubi Bilkisu da ta yi tsumu, kamar an tsoma kaza a ruwa. Cikin gori Amina ta ce.
Chapter 23 · 0% Book details