Sashe 62
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Au to, sai yanzu na gano! Wato saken da kika samu na zuwa cikin gari, shi ne kika haɗu da siraran karuwai suka koya miki wannan karuwancin ko? To ba a gidana ba, tun wuri ki watsar da abin da yake kanki idan ba haka ba ki ƙara gaba." Shiru Indo ta yi tana share hawaye. Daga can bakin ƙofa Hansatu da Larai suka ƙaraso suna tambayar abin da ya faru saboda sun ji ihun Indo, Yaya Inu bai tanka musu ba saboda har lokacin haushin Indo yake ji. Ita ma Indo ban da hawaye babu abin da take yi, don haka kowacce ta ƙunshe dariyarta cike da ƙeta suka koma ɗaki. Saboda dama haushin Indo suke ji, a kan shan ƙamshi da kallon wulaƙancin da ta dinga yi musu.
A kunyace Indo ta tashi za ta fita Yaya Inu ya ce, "Kuma tun wuri ki gyara mini ɗaki tas, kika ɗebo siraran cinyoyi kamar tsinke ashana. Yo ni akwai wani iya shege da wata figaggiya za ta yi mini?" Takaici ya sake cika Indo, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zare rigar mamanta da ke saƙale a wuyansa. Ta ɗauki zaninta ta ɗaura sannan ta shiga kiciniyar gyaran ɗakin, a cikin ranta ta shiga tsine wa Hajiya Zanni da miyagun shawarwarin da ta ba ta.
Washegari
Tun kusan kimanin ƙarfe huɗun asuba ya farka yake sharɓa kuka, tun yana yin na zuciya har ya dawo yin na sarari. Sautin sasshekar kukan da Baba Sale yake yi ne ya farkar da Uwale daga baccin da take. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa, da sauri ta zaro ƙaramar wayarta a ƙarƙashin filo ta haske ɓangaren da Ɗan Bishir yake bacc. Ganin yana bacci cikin kwanciyar hankali ya sa, ta dubi Baba Sale ta ce.
"Me yake faruwa mai gida?"
A maimakon Baba Sale ya ba ta amsa sai ya sake kallon wurin ÆŠan Bishir ya fashe da kuka. Jikinta ne ya yi sanyi don rabonta da ganin kukansa, tun wata rashin lafiya da ÆŠan Bishir ya yi kusan shekara É—aya da rabi kenan.
"Mai gida don Allah ka cire ni a cikin duhu, wallahi hankalina duk a tashe yake."
Uwale ta furta jikinta yana rawa, don ta ayyana abubuwa da dama a cikin ranta.
Baba Sale ne ya faÉ—a jikinta kamar wani sabon maraya, ya ja majina cikin kuka ya ce.
"Kamar kin manta yau ne za a yi wa ÆŠan Bishir shayi! Yau ne fa wa'adin kwanakin da za a yi masa kaciya ya cika."
Baba Sale ya yi maganar yana share ƙwalla, haɗe da shigewa jikin Uwale kamar wani ƙaramin yaro. Ya ɗago murya a dashe saboda kukan da ya ci ya ce.
"Uwale hankalina a tashe yake, wallahi duk wani abu da zai taɓa lafiyar Ɗan Bishir ba na son shi..."
Kuka ya sake cin ƙarfinsa, takaici ya mamaye Uwale amma gudun kada su fara raba hali tun da asuba ya sa ta ce.
"To ya za a yi, ai dama kowa da haka ya fara. Yanzu dai ka tashi ka je ka yi sallah na ji har an shiga masallaci."
A hankali Baba Sale ya fita yana jan majina, ya ɗauro alwala ya wuce masallaci. A lokacin da ya ƙarasa masallaci a raka'ar ƙarshe ake, bayan an idar ya tashi ya ciko raka'a ɗaya sannan ya yi sallama. Baba Sale hannu ya ɗaga ya fara zazzago addu'a, mutane ba su yi tsammani ba sai ji suka yi ya fashe. Sororo mutanen wurin suka yi, Yaya Ado har zai fita ya koma ya zauna. Duka mutane suka yi carko-carko suna kallonsa, Malam Rabe ne ya yi ƙarfin halin zuwa kusa da shi ya ce.
"Sale me yake faruwa ne?"
Baba Sale ya sharce majina ya fara wata shassheka kamar wanda uwarsa ta mutu ya ce, "Ina buƙatar addu'arku. Domin kowa ya san ɗana ɗaya ne a duniya wato Ɗan Bishir! Kuma ina fatan ya haifa mini jikoki ashirin da huɗu sai dai kash..."
Kuka ya sake cin ƙarfinsa. Gaban su Baba Labaran ya faɗi, don duk wanda ya ci karo da irin kukan da Baba Sale yake yi za ka ɗauka mutuwa aka yi masa. Cikin haɗin baki hankali a tashe duka mutanen cikin masallacin suka ce.
"Sai dai me?"
Baba Sale ya rungumo hannun Yaya Inu ya shiga goge fuskarsa da shi ya ce.
"Ku yi mini fatan a yi a gama wa Ɗan Bishir shayi, an jima Bala wanzan zai zo ya yi masa don ni ba zan iya ba. Ba ni da ƙarfin zuciyar ta guntule Ɗan Bishir."
Jin haka ya sa takaici ya mamaye su, a zafafe Yaya Inu ya fisge hannunsa ya ce.
"Kai dai ka zama gantalalle É—an wahala. Yanzu shayin da za a yi wa ÆŠan Bishir ne kake wannan iskancin, kai Allah Ya tsine iskanci da magoya bayansa. Shi ya sa ka sakar mana murya kamar an kunna generator kana ihu, Allah wadaran naka ya lalace."
Daga haka Yaya Inu ya fice daga masallacin rai a ɓace. Ɗaya bayan ɗaya haka mutane suka watse kowa yana mita, Baba Sale ya koma gida ya sake saka Ɗan Bishir a gaba yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki.
Tun da Ɗan Bishir ya tashi daga bacci Baba Sale ya ɗauke shi ya rungume, hatta abinci a baki ya dinga ba shi. Kimanin ƙarfe tara na safe Bala wanzan da yaransa suka ƙarasa ƙofar gidan, Uwale ce ta iya ɗaukar Ɗan Bishir ta miƙa masa. Domin Baba Sale uwar ɗaki ya shige ya haɗa kai da ƙarfen gado yana kuka. Saboda shekara ta uku kenan ana cewa za a yi masa shayi yana ɗagawa saboda soyayyar da yake yi masa. Yana nan zaune Inno ta aika kiransa, da ƙyar ya iya fita ya nufi sashenta fuskarsa ta kumbura saboda kukan da ya sharɓa. 'Yan'uwansa ya gani gabaɗaya a zaune, ya yi mamki matuƙa don haka ya zauna a gefe yana kallonsu. Inno ta dube su ɗaya bayan ɗaya, sai kuma ta saki wani murmushi zuciyarta fes ta ce.
"Dalilin da ya sa na tara ku a wurin nan ba komai ba ne, illa na sanar da ku wani abin alheri kuma abin farinciki da ya tunkaro mu. Kuma na tabbata za ku ji daÉ—insa, domin cigaba ne da zai iya kai ni aljanna da ku bakiÉ—aya."
Fuskarsu É—auke da fara'a gabaÉ—aya suka furta.
"Ma Shaa Allah, gaskiya wannan abin farinciki ne Inno. Allah Ya sa mu dace."
Inno ta sake washe baki fuskarta wasai kamar gonar auduga ta ce.
"Amin Ya Rabbi."
"Amma Inno wanne abin farinciki ne haka?"
Baba Labaran ya tambaya.
Inno ta rangwaÉ—a kai gefe ta ce, "Dama zan sanar da ku mun gama daidaitawa da Malam, don haka ma na ce zan sanar da ku a É—aura mana aure ranar Juma'a mai zuwa."
Sororo gabaÉ—aya suka suna kallonta cikin mamaki Baba Ibrahim ya ce.
"Inno aure fa kika ce?"
Inno ta haÉ—e rai ta ce, "Eh sunnar Annabi!"
Ajiyar zuciya Yaya Inu ya yi ya ce, "Yanzu Inno tuntuni ba ki yi aure ba sai yanzu? Saboda Allah tun da ƙarancin shekarunki bayan da Baffa babba ya rasu ba ki yi ba sai yanzu da girma ya cim miki? Gaskiya Inno ki yi tunani."
Inno ta yi wa Yaya Inu kallon sheƙeƙe ta ce, "Ka karanta mini aya ko hadisin da Allah Ya haramta wa tsohuwa aure! Yanzu Inusa sunnar Annabi kake ƙoƙarin daƙilewa?"
Yaya Inu ya yi shiru don zuciya ta gama zuwar masa wuya. Saboda dama tun farko jininsa bai haÉ—u da Malam mai Yasin ba.
"Yanzu Inno da za ki ce za ki auri mutumin nan mu da ba mu san asali da tushensa ba, babu wanda muka sani na shi fa. Abu É—aya ne fa ya haÉ—a mu da shi taimakon da muka yi masa a airport, sanadin kamen da aka yi masa wanda har yau babu wanda muka sani a cikin danginsa. Gaskiya ko za ki aure shi sai mun san wani daga cikin danginsa."
Baba Ibrahim ya yi maganar fuska a haÉ—e.
"Wallahi kai ka ma yarda ta aure shi, na rantse da Allah yadda na tsani ƙyamusasshen tsohon can idan ban sheme shi ba Allah Ya tsine mini!"
Yaya Inu ya faÉ—a jikinsa yana karkarwa.
Inno ta yi karaf ta ce.
"To wallahi ku shaida duk wanda na ji ko kallon banza ya yi wa Malam sai na ɗaga masa mamunana. Kuma dama na faɗa muku ne saboda na fita haƙƙinku na 'ya'ya atoh, don kada ku ji muna kashewa da binnewa ni da shi a ɗaki ku fara yi mana ɗan zargi. Duk da dai dama na faɗa masa auren ɗauko buta za mu yi."
Inno ta sake kallonsu É—aya bayan É—aya ta cigaba.
"To ku ban da abinku ace yau uwarku ta mutu da aure a kanta ba ya fi daraja a wurinku ba? Allah na tuba duk haƙurin da na yi da ubanku tsawon shekaru bai wadatar ba? Wallahi da shi ne ma ba zai ɗauki shekarun da na ɗauka bai yi aure ba, a toh a yanzu na samu wanda zai ba ni walwala da kulawa gwargwadon farincikina. Da ku ɗaura mini aure da kar ku ɗaura duk ɗaya, saboda yanzu zan tafi wurin Malam Liman ya zama waliyina shi kuma Malam Ladan ya yi wa Malam walicci ashafa mana fatiha."
Shiru ta ji sun yi ba tare da sun tanka mata ba, ta kalle su rai a ɓace ta ce duka su fice mata daga ɗaki. Nan take duk suka fice, Baba Ibrahim zai fita ya waigo ya ce.