Sashe 76
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"La'ilaha'illa'illahu Muhammadur Rasulillahi, Sallallahu alaihi wasallam. Ɗan Tasi me kunnuwana suke zuƙo mini? Kada ka ce mini Ɗan Bishiriri ya kamu, wayyo Allah Tasi riƙe ni da ƙarfi duhu nake gani."
Baba Sale ya yi maganar yana jin wata irin hajijiya tana yin É—iban karan mahaukaciya da shi.
Da sauri Tasi'u ya riƙe shi yana kiran sunansa da ƙarfi, "Baban Ɗan Bishir lafiya." A hankali Baba Sale ya ɗago duk da ba ya gane abin da Tasi'u yake faɗa sosai ya ce, "Tasi'u maza kai ni ofishin 'yansandan."
Kamar sabon ɗan maye haka suka tafi Tasi'u yana riƙe da shi, don har suka ƙarasa wani irin layi yake yi idanunsa suna yi masa gizo. Su Baba Sale suna zuwa, suka samu Bala Wanzan a tsaye yana bayani.
"Wallahi tallahi yallaɓai ban taɓa sanin Idi Naira yana da cutar abar nan ba, ni ko sunanta ba na son faɗa. Kuma babban tashin hankalina yaran da na yi wa shayi, a ranar da wannan tsautsayin ya afku. Domin su ne masu tasowa ba su mori ƙuruciya ba..."
Wata irin ƙara suka ji gijiiiiiif Baba Sale ya faɗa ta saman kanta, saboda tun a bayanin farko da ya ji Bala wanzan yana yi, ya ji ƙafafuwansa ba za su iya ɗaukarsa ba. Kalaman Bala na ƙarshe suka sa ya ga wani baƙin duhu ta lulluɓe idonsa, numfashinsa ya ɗauke.
"Subhnallah! Waye wannan? Lafiya?"
Wani kurtun ɗansanda ya ƙarasa kansa yana tambaya. Tasi'u ne ya yi musu bayanin abin da ya faru tsakaninsa da Baba Sale, har zuwansu cikin station ɗin. Ruwa aka ɗebo aka zuba masa, a hankali ya farfaɗo yana daga kwance yake kallon mutane ɗaiɗai. Ya yunƙura a hankali ya zauna sai a lokacin komai ya shiga dawo masa.
"Yallaɓai Ɗan Bishir, kun bincika mini Ɗan Bishiriri."
Wani Sergent da ya fahimci Baba Sale, ya dubi Bala Wanzan ya ce, "Kai Wanzan ka yi wa yaron wannan mutumin kaciya ne?"
Da yake a lokacin an mayar da Bala cikin cell, yana daga ciki ya ce. "Eh na yi masa yallaɓ..."
Tun Bala bai gama magana ba Baba Sale ya sake sumewa a wurin, haka suka sake zuba masa ruwa ya sake farfaÉ—owa. Sai dai su kansu abin da ya fi É—aga hankalinsu, yadda Baba Sale yana farfaÉ—owa zai sake suma. Har sun lura ko ya farfaÉ—o ba ya zama cikin hayyacinsa. Don haka suka tattarashi hankali a tashe suka yi asibiti da shi, sai bayan sun je suka saka Tasi'u ya yi musu rakiya har gida aka sanar da Uwale da su Baba Ibrahim halin da ake ciki.
Tun da suka fito daga asibitin yake zabga sauri, cikin sassarfa ta rufa masa baya ganin ya fara yi mata nisa ya sa ta fara ƙwala masa kira.
"Masoyi! Masoyi don Allah ka jira ni saurin me kake yi kamar za ka tashi sama."
"Ya muke da jirgin sama? Na ce ya muke da shi?"
Baba Labaran ya furta a zafafe.
Sororo ta yi tana kallonsa don har tsoro-tsoro ta ji, ganin yana yi mata faÉ—an da ba ta saba gani a tattare da shi ba. Hasali ma ba ta ga abin faÉ—a a maganarta ba.
"Asibiti na uku kenan a yau muna zuwa suna yi miki gwaji, amma duk maganarsu É—aya kamar haÉ—in baki. To magana ta gaskiya na fi son mace a haihuwar fari, saboda magaji nake nema. Haka kawai duka asibitocin sun ce mace suka gani. Wallahi da sake an ba wa mai kaza kai." Da mamaki ta dube shi ta ce.
"Da sake fa ka ce Masoyi? Shin butulci za ka yi wa uabangiji ne? Mutane nawa ne suke neman haihuwar ba su samu ba, mace ko namiji mai albarka ya kamata ka roƙa."
Maimakon ya ba ta amsa sai kawai ya saki tsaki ya yi gaba yana faÉ—in.
"Kanki ake ji, ni na gama faÉ—ar ra'ayina."
Daskarewa Rahinatu ta yi, ta ɗora hannunta a kan ƙaramin cikin jikinta da bai fi wata uku da satika ba. Cikin sanyin murya ta ce. "Dama duk soyayyar da mutumin nan yake yi mini ta fatar baki ce? Haƙiƙa Labaran ya cika butulu."
Daga haka ta fara takawa a hankali, ta rufa masa baya tana jin zuciyarta na suya.
Damuwa haɗe da tarin ayarin tunaninnika ne suka cunkushe masa kwanya, saboda Indo da su Hansatu sun nemi mayar da shi kamar mahaukaci. Don da sun kalle shi sai kowacce ta gimtse fuska, yana bada baya sai su kwashe da dariya. Rumfar Tsalha mai kayan miya nufa, yana zuwa ya yi sallama amma babu wanda ya amsa masa. Kamar haɗin baki, lokaci ɗaya mutanen cikin rumfar suka watse . Turus Yaya Inu ya yi, yana shirin magana ya ji Tsalha ya ce, "A gaskiya malam Inusa ka dakata da zuwa cikin rumfata, saboda ka da ka kawashe mini albarkar cinikayyata. Ba zan ɓoye maka Inusa ka san dai ni abokinka ne, maganar haihuwar zabiyar nan fa ya karaɗe ciki da wajen garin nan don haka ka yi hattara." Daga haka Malam Tsalha ya koma kujera ya zauna yana haɗe rai, don kada Yaya Inu ya samu fuskar zama.
Kamar zakaran da aka tsamo daga cikin ruwa haka Yaya Inu ya fito ya nufi hanyar gida, tunanin Zuly matashin kai ce ta faɗo masa. Ya saki murmushi ya nufi ƙofar gidansu. Ƙaramar wayarsa ya ciro ya kira ta, ba a ɗauki lokaci ba ta fito tana taunar cingam.
"Haskena ashe kaine da yamma haka?"
Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Takanas na shiryo na zo na ganki domin na huce takaicin zuciyata, saboda ke kaÉ—ai ce hasken da ke yaye duhun da ke É—anfare a ciki."
Sai da ta hura kwai da cingam ta ce, "Wani zance nake ji yana tashi, wai an haifar maka zabiya 'yan gidanmu har sun fara bala'i. Ni kuwa na ce duk bala'insu ba zabiya ba, ko rabi mutum rabi aljan aka haifa maka babu wanda ya isa ya han ni aurenka." Farinciki ya sa ta Yaya Inu ya zaro rafa kuɗi har dubu goma ya miƙa mata.
"Ki sha lemo da wannan, masoyiyata kuma hasken zuciyar Inusa."
Alewa ta buɗe ta wurga a baki ta tsotsa, sannan ta zaro ta miƙa masa cike da kissa. Cikin so da ƙauna Yaya Inu ya karɓi alewar, ya jefa a baki ya yi mata sallama. Yana gab da shiga gida ya hango wani mai magani, yana tafe da wata ƙatuwar Mp3 da wani faffaɗan kwando mai ɗauke da magungunan maza a ciki.
"Ina mai matsalar kuzari? Ina namijin da ya rako maza? To ya hanzarta ya zo ga adamalmala. Maganina rabo ne, maganina sa'a ce. Alhaji sai mai tsananin rabo ne zai dace na ba shi, ina mazan da basir ya jima da yi musu illa? Alhaji ba ka nisan zango wurin tuƙa sitiyarin mota? Don Allah ka zo, ga mai adamalmala ya dawo. Idan na bar garin nan ba zan dawo ba, maza kaɗai nake ba wa magungunana domin na fi kishinsu a kan mata. Alhaji ko Malam kada ka ji kunyar karɓa, indai matsalarka a ɓangare iyali ne ta kau. Sabon aure za ka yi ne? Ko kuwa ka rasa gane kan matanka ne? To maza gangaro ka karɓa sadakar ƙalilance, ni dai ba na rowa domin burina na kankaro mutumci a wurin maigida."
Yaya Inu ya tsaya a jikin bishiya ya yafito shi da hannu, Mai maganin ya ƙarasa wurinsa adaidai lokacin Na Balaraba ya ƙarasa ta wurin zai wuce.
"Kai wa nake gani kamar Gambo, ko idanuna ne?"
Cewar Gambo.
Mai maganin ya É—ago yana kallon Na Balaraba da sauri ya ce, "Kai! Wa nake gani kamar Na Balaraba? Dama rai kan ga rai?"
Yaya Inu ya washe baki, "Na Balaraba ka san shi ne?"
Na Balaraba ya furta, "Na san shi farin sani, yanzu ne dai zumunci ya zama yanda ya zama, shekara biyar zuwa shida rabona da shi."
Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Ka ce faÉ—uwa ta yi daidai da zama, dama kiransa na yi zan sayi magani."
Mutumin tun da ya yi tsaye yake ƙarewa Yaya Inu kallo, har sai da gabansa ya faɗi. Amma jin Na Balaraba ya ce ya san shi ya sa ya saki jikinsa.
"Haba ba ka da damuwa Inusa, ka sayi maganinka wannan da kake gani ba na shakku a kansa."
Yaya Inu ya nuna wani magani ya ce yana son saya, Mai maganin ya yi zaraf ya ce. "A'a mai gida bari na ba ka wannan, ai wannan shi ne gagara-badau an buga da kai an barka." Ya ƙarasa maganar yana miƙa masa wata roba ƙarama ya ɗora da cewa.
"Yanzu kana komawa gida tun da magariba ta ƙarato ka shafa shi, sai bayan minti talatin ka wanke da ruwan ɗumi. Ka zuba wa sarautar Allah ido za ka ba ni labari idan na sake dawowa."
Jiki yana rawa Yaya Inu ya zaro kuÉ—i ya biya. Bayan Mai maganin ya tafi Baba Ado da yake gefe ya ce masa.
"Yanzu Allah Yaya, ba za ka raba kanka da gabzawa kanka waÉ—annan magungunan barkatai ba? Haka kawai maganin kare da doki kowa na ka ne, ba ka duba inganci ko ka je wurin masu magungunan gargajiya waÉ—anda suka san kansu ka saya..."
A sheƙe Yaya Inu ya katse shi.
"Kai dakata kada ka yi mini rashin kunya, tuzurun banza da wofi. Wai har da su kaza a cin danƙo? Kai da ko arzikin auren ba ka samu ba, shi ne har za ka zauna kana yi mini fi'ili? Tun da kai 'yan mata aljanu sun gama tsuƙe jijiyoyin jikinka, ai sai ka bar masu raya sunnar Annabi su yi. Da uwar kuɗina nake saya babu wani ƙato da yake saya mini, don haka kada ka sake shiga hurumina."