Sashe 25
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wash cikina, wallahi ji nake kamar zan mutu."
Ta furta tana satar kallonsa ta gefen ido, a hargitse ya sake tallafo ta ya ce.
"Mutuwa Amina? Don Allah ba na so, ba na son ki dinga furta kalmar mutuwa hankalina tashi yake yi." Amina ta ja numfashi ta fesar tana yarfe hannu ta ce.
"Wash! Hasbunallahu wa ni'imalwakil."
A daidai lokacin Bilkisu ta ƙaraso ɗakin a yatsine ta ce.
"Wai wanne irin ciwo ne da za a ce bai tashi ba sai yanzu da asuba."
Ta yi maganar, saboda ta fahimci Amina ƙarya take yi. Don ta tabbata ganinsu tare da Hafiz ne ya sa ta yi yunƙurin yin ciwon ƙarya. A fusace Hafiz ya ɗago ya ce.
"Haba Bilkisu, kina da imani kuwa? Ba ki ga halin da yarinyar nan take ciki ba?"
Amina tana jin haka ta karyar da kai gefe ta ce, "Don Allah ka kai ni asibiti, ji nake É—an cikina kamar zai birtso waje."
A hargitse Hafiz ya ce, "Bari na yi wa maƙocina Habu magana, sai ya kai mu a adaidaita sahunsa." Yana gama maganar ya fice da sauri.
Bilkisu ce ta riƙe ƙugu cikin tijara ta ce, "To munafuka algunguma, wallahi tun wuri gara ki ware. Don na san makircinki ne da munafurci ya sa kika yi ƙaryar ciwo." Amina ta dube ta tun daga sama har ƙasa sheƙeƙe, sannan ta miƙe tsaya ta yi taki biyu ta ce.
"Ashe makiran suna da yawa, wai Bilkisu yaushe za ki sauya hali ne? Wallahi-wallahi zuciya ɗaya nake tare da ke, amma ƙarfi da yaji kin koya mini makirci da munafurci. Ƙiri-ƙiri na ce mu je mu ba wa Habibi haƙuri kika ce mini ba haka ba, ashe ni kika mayar 'yar iska. Tun da dai duk nasihar da ya yi mana ba za ki ɗauke ta ba, ni da ke mu zuba mu gani."
"Ni kike cewa Bilkisu kai tsaye?" Bilkisu ta furta a ƙufule, Amina ta watsa mata harara ta ce.
"Haifata kika yi da ba zan faɗi sunanki ba? Tun asali ina ba ki girma shi ya sa nake sakaya sunanki, amma tun da na lura ba zaman lafiyarmu kike so ba. Wallahi zan tafiyar da ke a yadda kika zo mini." Rai a ɓace Bikisu ta ce.
"Sannu macijiya da ba ta ramin kanta, aikin kenan. Sai kun yi kwantai a gidajen iyayenku ku dinga aure mazajen wasu, ai wallahi na rantse da Allah sai kin yi nadamar auren mijina da kika yi. Saboda Hafiz nawa ne ni kaɗai, ƙaddarar da ta saka kika aure shi ita za ta sa na gasa miki aya a hannu."
"Ai kuwa ni da ke sai dai mu gasawa juna, kuma dama can Hafiz ba mijinki ba ne ke kaɗai. Saboda Allah Ya ƙaddara masa auren mata har huɗu, ke ko yau zai kawo biyu ba zan ɗaga hankalina ba saboda na san kowacce mace da ƙaddararta. Kuma ki bar cika baki, saboda kema kina da 'ya'ya mata, idan Allah Ya ƙaddara musu auren masu mata za mu ga yadda za ki yi."
Amina ta furta a fusace, Bilkisu ta yi saurin shan gabanta ta ce.
"Mugun bakinki ya faɗa kanki, kin ɗauka yadda kika yi kwantai ta ƙare miki kika kasa samun mijinki sai na wata. Kin yi zaton kowa haka yake? Ai indai auren mijin wata ne baƙinciki da ƙuncin gidan miji yanzu kika fara gani."
"Yanzu muka fara gani dai ni da ke, don babu abin da kika fi ni da shi wallahi. Duk tunƙahonki matsayinmu ɗaya, ke matarsa ce ni ma haka." Amina tun ba ta rufe bakiba Bilkisu ta ce.
"Ƙarya kike wallahi, matsayina da na ki har abada ba zai zama ɗaya ba. Domin ni ce matarsa ta farko, ni na ɓare abina sabo kar a leda. Mahaifinsa da mahaifina aminaine, na san duk rintsi babu rabuwar aure tsakanina da shi. Ke kuwa gayyar tsiya arna a Idi, haka aka yayimo ki daga duniya aka kawo mana annoba gida. Ko yanzu zai iya rabuwa da ke, kuma ya zauna lafiya. Don ni da kika gani, na zama ƙadangaren bakin tulu ban fito ba sai da na shirya, na zama ƙasar saman kabari duk taƙamar mamaci sai na raɓe shi. Na zama kujerar zaman gida, ko an ƙi ko an so dole a zauna da ni."
Bilkisu tana rufe baki Amina ta saki dariyar rainin hankali sannan ta ce, "Ai duk na banza ne, tun da kika kasa riƙe shi har ya fita waje ya nemo ni domin ya samu kwanciyar hankali. Da kin isa da isarki ai da kin dakatar da shi daga aurena, ba ki san sakaci na rashin gamsarwa da kulawarki ne ya sa shi auro ni..." A zuciye Bilkisu ta kai wa Amina mari, a daidai lokacin Hafiz ya kawo kai ganin haka ya sa shi shiga ɗakin da sauri ya ce.
"Ke Bilkisu ba ki da hankali ne? Mace da ciki a jikinta kike marinta."
"Na mara É—in, ko za ka rama mata? Ni ka san irin magamganun da ta furta mini..."
Tas! Ita ma Hafiz ya ɗauke fuskarta da mari. Amina da ke kwance a ƙasa ta saci kallon Bilkisu ta sakar mata gwalo, sai kawai ta fashe da kuka ta ce.
"Wayyo Allah cikina za ta kashe ni."
A hargitse Hafiz ya É—ago ta ya ce, "Sannu Amina, za ki iya tashi mu tafi ko na É—auke ki." Kamar tana jira ta ce.
"Jiri nake ji ba zan iya tashi ba, ga shi dukan da ta yi mini cikina ciwo yake mini." Hafiz ne ya ɗauki Amina cak zai fita cikin sauri Bilkisu ta tare ƙofar ta ce.
"Wallahi babu inda za ka kai munafukar nan, kuma wallahi tun da ka mare ni sai na nuna muku É—anyan kai."
"Ki matsa na wuce Bilkisu kada ki ɓata mini rai."
"Ba zan matsa ba." Bilkisu ta ba shi amsa kai tsaye, rai a ɓace ya sake cewa.
"Ki matsa na wuce Bilkisu, wallahi idan kika bari raina ya ɓaci ba za ki ji da daɗi ba."
"Wallahi sai dai ka yi duk abin da za ka yi amma ba za ku fita ba, saboda yau ranar girkina ce babu karuwancin da za ta nuna mini..." Bilkisu ba ta rife baki ba Hafiz ya hankaɗe ta ya wuce, daga can baya ta faɗi ƙasa warwasa don ba ƙaramij buguwa ta yi ba. Hafiz ya wuce da Amina ƙofar gida ya saka ta a Adaidaita sahu, sai da ya koma ya ɗauko katin asibitinta ya rufe ƙofar ɗakinta sannan ya fita suka wuce asibiti.
Bilkisu ta jima a wurin tana kuka, sai da ƙyar ta yunƙura ta shiga ɗaki. Ta sauya kayan jikinta, sannan ta shirya yaranta ta tasa ƙeyarsu gidansu Hafiz.
ALHAJI UMAR
Da mamaki Daddy ya dubi Baba malam ya ce.
"Yaya ina da Karima bayan wacce ka sani?"
Fuska a tamke babu alamun wasa Baba Malam ya ce.
"A da dai na sanka da Karima, amma a yanzu Karimar da na sani ba ka da hurimi da ita."
"Don Allah Yaya idan wasa kake yi mini ka daina, wallahi tallahi hankalina a tashe yake. Ina son na ganta, saboda mummunan mafarkin da na yi a kansu." Daddy ya furta a hargitse. Kallon da Baba malam ya yi masa ne ya sa shi shiga hankalinsa. Ya nuna shi da yatsa ya ce.
"Ni na yi kala da sa'anka ko wanda zai zauna yin wasa da kai? Kai Umaru! Kada ka raina mini hankali, Karima ba matarka ba ce. Ka koma can gidanka ka cigaba da zama da matarka, a yanzu haka tana gab da ɗaura aure. Idan kuma 'ya'yanka za ka karɓa, a yanzu zan shiga na taso maka su ka tasa ƙeyarsu a gaba ka tafi da su." Kafin Baba Malam ya gama magana tuni gumi ya wanke fuskar Daddy, hankali a tashe ya zube a gabansa ya ce.
"Don girman Allah kada ka yi mini haka Yaya, wallahi ni ban saki Karima ba. Yaya ka yi mini rai, wallahi ji nake ba zan iya rayuwa idan babu ita ba."
"Idan ka mutu kwananka ne ya ƙare Umaru, kada ka manta; a yanzu ba ni da uwa ba ni da uba. Don haka babu numfashin wani da zan rasa a yanzu, har ya ɗaga mini hankali. Ruwanka ne ka cigaba da rayuwa, ruwanka ne kuma ka zaɓi mutuwa. Amma ina me tabbatar maka, idan ka sake zuwa da maganar Karima gidan nan wallahi zan ba wa securities umarnin kada su bari ka sake shigowa." Baba malam yana gama magana ya shige ciki, da sauri Daddy ya bi bayansa sai dai kafin ya ƙarasa ya datse ƙofar. Daɓar! Daddy ya zauna a wurin yana jin duniyar gabaɗaya ta yi masa zafi. A nan barandar da Daddy ya zauna, yana nan zaune har aka kira sallar asuba, Daddy yana nan zaune Baba Malam ya fito zai tafi masallaci. A sanyaye Daddy ya ɗaura alwala ya bi shi suka wuce masallaci, sai dai kallon fuskar Baba malam da ya yi ya ji fargaba ta sake mamaye shi. A haka suka yi sallah suka dawo cikin gida, Baba malam yana gab da shiga cikin gida Daddy ya ce.
"Don Allah yaya, don zatin Ubangiji ka..."
"Umaru ba na son damuwa don Allah, yanzu haka kaina ciwo yake tun tashin da ka yi mini ina bacci. Ka je wurin matarka idan na yi nazari zan neme ka." Daga haka Baba malam ya wuce ya bar shi a tsaye. Kamar zai É—ora hannu a ka, haka Daddy ya wuce ya shiga mota ta nufi gida zuciyarsa a dagule.
Lokacin da ya je gida gari har ya yi haske, a lokacin da ya shiga Shukura tana zaune a takure cikin damuwa. Tana ganinsa ta miƙe zumbur kamar marar gaskiya ta ce.
"Baby ina fatan ka dawo lafiya?"
"Eh."
Kawai ya furta a taƙaice ya wuce ɗakinsa. Da sauri Shukura ta bi bayansa har ta shiga rai a ɓace ya ce.
"Get out please, ba na buƙatar hayaniya."