← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 81

Sashe 11

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To na dakatar da kiwon na ki ma gabaɗaya, saboda kawai na ce ki bari har zuwa lokacin da za ta haihu shi ne za ki faɗa mini magana." Baki sake Mommy take kallon Alhaji, ya miƙe ya nufi hanyar fita sannan ya waigo ya ce.

"Zuwa nan da gobe akwai mutanen da za su yi miki maganar kajin, idan kuma ba haka ba ni da kaina zan sa a fitar da su." Har ya saka ƙafa zai fita Hajiya ta bi bayansa da sauri ta ce.

"Ina mai tabbatar maka idan ka fitar mini da kaji wallahi-wallahi sai dai ka zauna da Shukura a gidah nan ba ni ba." Cak! Daddy ya tsaya, rai a ɓace ya waigo ya ce.
"Wato kaji sun fi maganata kenan? Me kike nufi?"

"Ina nufin zan bar gidanka?" Ita ma ta ba shi amsa kai tsaye.

"Saboda kina baƙinciki da abin da za ta haifa? Yanzu dama akwai ranar da za ki ƙi jinina Karima? Saboda kawai na ce ki yi haƙuri zuwa wani lokaci za ki faɗi haka? Wato kin fi son ta yi ɓarin cikin kenan?" Ahaji Ya furta, Mommy da ranta ya gama ɓaci ta ce.
"Idan duniya Shukura za ta haifa maka wallahi ba na baƙinciki ko ƙyashi, saboda na san na wuce ta har abada ni da 'ya'yana ne a gaba. Amma wallahi ba zan ɗauki kowanne irin cin kashi da yarinyar nan za ta yi mini ba."

Kamar Alhaji zai yi magana sai kuma ya fice daga cikin É—akin zuciyarsa tana suya. Can É—akin Shukura ya shiga, tana ganinsa ta tashi zaune ta ce.
"Ya ake ciki ne?"

Dafe kansa ya yi ya ce, "Wallahi ta ƙi amincewa, ni na rasa yaushe Hajiya ta fara musu da ni." Shukura tana jin haka ta fashe da kuka, cikin tashin hankali ya riƙo ta ya ce.

"Don Allah kada ki ɗaga hankalinki, wannan ba abin damuwa ba ne. Wallahi na yi bakin ƙoƙari don ta amince amma fir ta ƙi amincewa. Har tana ce mini za ta bar gidan nan idan aka fitar mata da kaji." Da sauri Shukura ta ɗago ta ce.

"To sai me? Ba sai ka sake ta ba tun da ba za ta bi umarninka ba. Daɗin abin ai ba ita kaɗai ce matarka ba." Da wani irin sauri Alhaji ya fisge jikinsa daga jikin na Shukura, har sai da ta tsora ta. Rai a ɓace ya nuna ta ya ce.

"Ko a mafarki kada ki sake tunanin zan iya rabuwa da Hajiya Karima, wannan matar da kike gani ita ce komai nawa. Kuma ban auro ki saboda na daina sonta ba, ina son matata domin ita ce rufin asirina. Duk wani mataki da kika ga na kai, wallahi ta silarta ce." Alhaji ya gama faÉ—a ya fita daga É—akin a zuciye.

GIDAN HAFIZ

Bayan Hafiz ya watsa ruwa, zama ya yi daga shi sai kayan shan iska.A gefen Amina ya zauna, ya fara bin ta da wani irin kallo. Murmushi ta sakar masa, ya shafo fuskarta ya ce.

"Na yi kewarki Meena."

Cikin zolaya ta ce, "Ba wani nan ni ban ga alama ba." Matse ta yi a jikinsa tsam, ta saki 'yar ƙara kaɗan lokaci ɗaya suka saki dariya. Janye jikinta ta yi ta ce.

"Akwai tea akwai drink wanne za ka fara sha?"

Lumshe ido Hafiz ya yi ya ce. "Da ke zan fara mana." A ɗan shagwaɓe Amina ta ce.

"Habibi ka fiye wasa fa."

Sauka ya yi ƙasa, Amina ta zuba masa ruwan shayi a kofi, ta buɗe fulas za ta zuba masa abinci, daga bakin ƙofa suka ji Bilkisu ta zuro kwano cike da abinci ta ce.

"Idan har kin yi haka don ki kashe ni ko ki kashe 'ya'yana, In Shaa Allahu sai dai ki gani a kanki. Saboda kin É—ebi naki abincin da na Abban Sayyid shi ne mu za ki hala ka mu, ai shi kenan Allah Yana kallo." Daga haka Bilkisu ta bar wurin.
Kallon juna Hafiz da Amina suka yi, a sanyaye ta miƙa hannu ta ɗauko kwanon tana kallonsa, sai dai ko kaɗan ba ta ga komai ba. Abu ɗaya ta ji shi ne wari-warin fetir, Hafiz ya ɗauki abincin ya shinshina ya ce.

"Me kuma ya kawo warin fetir a abinci?" A sanyaye Amina ta ce.

"Wallahi ban san yadda aka yi ba. Lafiya ƙalau na yi girki na gama." Ajiye kwanon ta yi, ta fara zubawa Hafiz shi ma. Yana matso da plate ɗin gabansa ya ji warin fetir ya doki hancinsa, da sauri ya ɗago ya ce.
"Amina wai me yake faruwa ne? Wannan wanne irin wulaƙanci ne za ki saka mana fetir a cikin abinci? Ina ce galan ɗin fetir daban na mai ma daban?" Idanun Amina suka ciko da ƙwalla, ta saka hannu ta share hawaye murya tana rawa ta ce.

"Wallahi ban san komai ba, lafiya ƙalau na gama girki."

"Ƙafa gare shi man ko hannu da zai zuba kansa? Shi kenan sai ki san yadda za ki yi da shi." Hafiz ya furta cikin fushi sannan ya zura doguwar rigarsa ya fice. Bilkisu da ke ɗaki murmushin ƙeta ta saki, ta ɗauko waya ta kira shi tana ji ya ɗauka ta ce.

"Abban Sayyid yanzu ya zan yi da yara? Ga shi suna kukan yunwa."

"Ki dafa musu taliya mana." Hafiz ya faÉ—a a É—an faÉ—ace. Kwantar da murya Bilkisu ta yi ta ce, "Ai ina tsoron ko man ne yake da fetir kada na sake saka musu a koma 'yar gidan jiya." Shiru Hafiz ya yi sannan ya ce.

"Ki fara dubawa kafin ki zuba, idan kin dafa kuma ki zuba mini ni ma a cooler ina dawowa." DaÉ—i ne ya cika Bilkisu, ta amsa masa sannan ta kashe wayar.

Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624

[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.

Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.

SHAFI NA BAKWAI

AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*

***

Bilkisu drower kayanta ta buɗe, ta jima a tsaye tana nazarin waɗanda za ta ɗauka. Wata doguwar riga shara-shara ta ɗauko ta zura, ta shiga ɗakin yaran ta same su har sun fara bacci da yake an yi sallar Isha'i. Shimfiɗa ta yi musu ta ɗauko net ta saka musu, ta koma ɗaki sannan ta ɗauki ragowar taliyar da suka ci ita da yaran wacce ta zuba a cooler ta ajiye. Motsin Amina ta ji, don haka ta yi zaraf ta fito ta ɗauki buta ta yi kamar banɗaki za ta shiga. Amina ta gani ta fito da abincin ta saka a kicin, murmushin ƙeta Bilkisu ta yi ta shiga banɗaki bayan wani lokaci ta fito har za ta shiga ɗaki ta ja tsaki ta ce.
"Aikin banza, haka kawai a jaza wa mutum ɗora girkin dare. Ai shi ma Abban Sayyid ɗin maganinsa kenan, kana tare da matarka cikin rufin asiri ka ci ba ka ci ba babu wanda ya sani. Amma haka kawai rana tsaka a ɗauko maka baƙar ƙaddara ta addabe ka, tun da nake a gidan nan 'ya'yana ba su taɓa kwanciya ba su ci abinci ba sai yanzu."Ta gama faɗar haka ta faɗa ɗaki. Amina da ke durƙushe tana juye abinci a tukunya ta share hawayen idonta, saboda ta yi tunanin duniya ba ta tuna a lokacin da ta zuba fetir a madadin mai a abinci ba. Kuma ko da ta gama girki ba ta ji warin komai ba, a sanyaye cikin damuwa ta koma ɗaki ta zauna. Waya ta ɗauka ta kira layin Hafiz ta ji bai ɗauka ba, abin duniya duk ya dame ta don bai taɓa yin fushi da ita irin haka ba.

Bilkisu tana daga ɗaki wani tunani ne ya faɗo mata, da sauri ta ɗauki waya ta je bakin ƙofa yadda Amina za ta ji ta ce.
Chapter 11 · 0% Book details