Sashe 41
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sabuwar wayar ya ɗauko gal a cikin kqalinta ko buɗewa ba a yi ba, ya miƙa matasa sai kuwa ta saki fukarta ta hau washw baki don ta yi tsammanin ita ya sayo wa sabuwar waya.
"Idan kin fita ki miƙa wa Maman Asiya, idan Naziru ya dawo ta ba shi saƙon sa da ya ce a taho masa da shi."
Murnar Maman Nana ta koma ciki, nan take ta haɗe rai don kusan sati uku kenan ba ta da waya tun da Abdul ya jefa mata wayarta a ruwa. Ta yi nacin Ya sayo mata waya kullun da zancan da zai ɓullo mata.
Gidan Maimuna ta ƙwanƙwasa da yake Maimunan ta san da maganar wayar da sauri ta je ta buɗe ƙofar, tana ganin Maman Nana ta ji wani farimciki ya lulluɓe ta. Wayar hannunta ta miƙe mata, sannan ta ce.
" A É—an sammun gawayi zan yi turaren wuta."
Maimuna ta ce, "Wannan wayar kuma fa?"
"Baban Nana ne ya ce ki ajiye wa Abban Asiya."
Kamar Maimuna ba ta san kwanan zancen ba, ta saki fuska cikin murna ta ce.
"Allah Ya sa Abban Asiya suprise zai yi mini, don bai yi mini zancen za a taho masa da waya ba."
Maimuna ta saka cokali tana ɗiba gawayi ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Wai har yanzu ba ki gama girki ba Maman Asiya? Kai gaskiya masu girkin gawayi kuna ƙoƙari ina zan iya wannan jidalin?"
Wani takaici ya maƙaure zuciyar Maimuna, ta bi bayan Maman Nana da harara a ranta ta ce.
'Ni za ki yi wa iskanci kenan? To wallahi daga wannan karon kema kin daina aiki da gas ɗin, ba dai ni za ki yi wa iskanci ba? Za ki ga muna ƙoƙari ganin idonki.'
Maman Nana tana gama ɗiban wutar ta yi wa Maimuna sallama ta fice, a ta cikin riga Maimuna ta sakaya ledar wayar ta shige uwar ɗaki ta ita. Kayan sakawarta ta ɗaga daga can ƙasa ta tura wayar, ta ciro ƙaramar har za ta saka layi ta kira shi sai ta mayar saboda ta fi son sai zuwa jimawa idan ta sallami yaranta sun yi bacci ta kira shi su sha hira kamar yadda suka saba daddare kafin Nazir ya dawo. Tun da dama can shi Nazirba mutum ne mai dawowa gida da wuri ba, idan ma ya dawo ɗin mafi yawa lokaci hankalinsa yana kan wayarsa bai cika ba ta lokacinsa ba.
Hatta su Asiya sai da suka lura da farincikin da take ciki, amma sai ta nuna musu ba komai. Da yake a ƙage take da ta ji muryarsa, ana idar da sallar Isha'i ta yi musu shimfiɗa. Sai da ta tabbatar da bacci ya kwashe su sannan ta shige ɗakinta ta ciro ƙaramar wayar da suke waya ta kira shi.
A ɓangaren Jafar kuwa tun bayan da ya lura da haɗe ran da Maman Nana take yi, shi ma sai ya yi watsin iska da ita. Hakan kuwa ya sake ɓata mata rai, don haka ta ci alwashin za ta gasa masa a ya a hannun ta cikin ruwan sanyi. Yana gama cin abinci ya fice daa gidan, ya tafi can nesa da layinsu wurim da ya saba waya da Maimuna ya zauna. Ya jima yana dakon flashing ɗinta har sai da ya fara cire rai, sai ransa ya ɓaci da ya ayyana ko dai Naziru ne ya dawo shi ya sa ba ta smau damar kiransa ba.
Yana nan zaune ya ji flashing ɗinta, a fili ya saki ajiyar zuciya. Hannunsa har rawa yake ya latsa layin nata, tana ɗaga wa ya ji ta fashe masa da wani irin kukan kissa. Wani abu ya ji yana zarga masa wanda ya kashe masa ilahirin jijiyoyin jikinsa. Sai da ya yi ƙarfim hali sannan ya iya fisgar maganar bakinsa.
"Wannan shagwaɓar taba gigita ni my Moon, idan ba kya son hana ni bacci a ɗan daga ta da kukan nan haka."
Daga can ɓangaren Maimuna ta sake yin wata shasshekw wace ta sake birkita shi, murya can ƙasa kamar wacce take waya da mijinta ta ce, "Ina kukan farinciki ne my J. Haƙiƙa ka faranta mini rai domɗn wannam wayar ba ƙaramin tsada gare ta ba."
Murmushi ya yi mata ya ce, "Ko nawa zan iya ɓatar mini Moon, fata da burina kawai ki mallaka mini kanki."
"Idan hat ni ce kamar ka samu J, kada ma ka sake wasu-wasi a kan soyayya ta."
Har Jafar zai yi magana Maimuna ta katae shi a shagwaɓe.
"Ɗazu matarka ta ci mutumcina bayan ta zo ɗiban gawayi, a gaskiya raina ya ɓaci domin an daɗe ba a ci zarafi kamar na yau ba. Duk da ba cikin faɗa ta yi mini magaanar ba, amma a wasan dare ta ƙare mini cin mutumci. Har takw yi mini ƙafafa a kan ita amfani take yi da gas."
Sai kuwa Maimuna ta rushe da kuka, kukanta yake ji har cikin ransa. Don ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, cikin rarrashi ya ce, "Ya isa haka baby Moon. Wallahi tun ranar da na fara ganinki ba ki kalar amfani da gawayi ba. In Shaa Allaha na san yadda za a yi na saya muki gas ki daina amfani da gawayi. Ita kuma ki bar ni da ita na rantse miki da Allah daga gobe ta daina amfani da gas gabaɗaya. A yanzu ma don dai dare ya yi, da a daren nan zan siyo masa kurfoti da buhun gawayi."
Ummou Aslam Bint Adam
+2347062062624
[13/02, 21:16] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA BAKWAI
UWAR GIDA, AMARYA HAR MA DA MAI GIDA KU MATSO KUSA.🥳🥳🥳🥳🥳🥳🥳
Ina kuke matan habiby da Habibin kansa ku matso kusa ga kaya nagani na fada wanda habiby xai saka ki kasa gane shi ðŸ˜shin kina neman inda xakisai ma mijinki kyauta ta bazata ? Maza hanxarto musaka labule jallabiya ta gani ta fada da hula mai musulmin kyau wanda xai burge oga 😠akan farashi daidai da aljihunki kundaisan kyauta tana kara soyayya
Kaima habiby ban barka abaya ba hanxarto gurinmu ka mallaki hula da jallabiya qualitatives via +234 816 916 8731
***
Wani irin farinciki ne ya lulluɓe zuciyar Maimuna, saboda dama ba a ranar Maman Nana ta saba zuwa tana yi mata fariya, tana baje mata jin daɗin da Jafar yake yi mata ba. Wani abin ma sai ta lura kamar da gayya Maman Nanan take yi, saboda mijinta duk ya fi ragowar mazajen layin rufin asiri. Wannan ne dalilin da ya sa Maimuna ta ci alwashin sai ta tarwatsa farincikinta, tun da ita ba ta samu kwatankwacin abin da Maman Nana take samu a wurin miji ba.
"Na ji kin yi shiru ko hukuncin da na É—auka bai yi miki ba?"
Jafar ya furta jin Maimuna ta yi shiru, Maimuna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Hakan ya yi Baby J, to amma ta ya ya zan mallaki gas É—in? Ni dai ba sana'a nake yi ba ballantana na cewa mutumin nan saya na yi."
"Wannan mai sauƙi ne Moon, zan san yadda zan ɓullowa lamarin."
Hirar soyayya suka cigaba da yi tamkar ma'auratan da suke nesa da juna, kowanne yana cike da kewa da begen ɗan uwansa. Suna gab da yin sallama Jafar ya ce, "Wayar nan da na aiko ba ta buƙatar caji, na saka mata caji ɗazu. Abin da ya rage kawai don Allah ki ɗaukar mini hotunanki."
Maimuna ta ce, "Sai zuwa gobe idan Nazir ya fita, amma ka ɓoye su ta yadda matarka ko wani ba zai gani ba."
Murmushi Jafar ya yi ya ce, "Kada ki damu akwai folder da nake ɓoye hotuna, a nan zan ɓoye naki."
Yana faɗin haka daga gefensa ya ji Nazir ya yi masa sallama yana daga kan mashin, duk da ya san Nazir ba zai taɓa fahimtar da wacce yake magana ba. Amma sai da gabansa ya faɗi, ya cire wayar daga kunnensa ya ce.
"Ale Nazir barka da shigowa."
Nazir ya É—an rage gudun mashin É—insa ya ce, "Barka dai Alhaji Jafar, ka na nan a bayan fage kana waya ko? Ai sai na aika na faÉ—a mata." Nazir ya yi furucin cikin barkwanci.
"Tuba nake kada ka sa a rufe mini ƙofa." Jafar ya furta yana kama kunnensa, dariya Nazir ya yi ya wuce gida. Ganin ya tafi ya sa Jafar ya ja dogon tsaki yana mayar da wayar kunne ya ce, "Ina tsaka da farinciki wannan mutumin zai datse mini, don Allah Moon ki rage ba shi kula a turaka. Wallahi haka kawai kishinsa yake nuƙurƙusata."
Maimuna da ita kanta haushin Nazir ya kama ta ce, "Ai yau duk bala'insa babu ma abin da zai haÉ—a mu, dama na kwana biyu ina juya masa baya."
Kamar ba za su rabu ba haka suka yi sallama.
Maimuna tana gama wayar ta yi saurin mayar da ita wurin da take, ta yi sauri ta haye gado ta kwanta ta rufe ido. A kan kunnenta Nazir ya shiga gidan, ya É—an jima a falo sannan ya tashi ya shiga É—akin.
"Maimuna! Maimuna!"
Ya furta yana bubbuga filonta, yamutsa fuska ta fara yi tana miƙa kamar wacce ta jima tana bacci.
"Sannu da zuwa."
Ta furta masa tana sakin hammar ƙarya.
"Yawwa sannu ya gida?".
A hankali ta zuro ƙafafuwan ƙasa, ta jinginta kanta da fuskar gadon ta ce. "Lafiya ƙalau."
Ya yi mamakin a 'yan kwanakin nan da Maimuna ba ta yi masa ƙorafi, domin kusan kullum idan ya dawo gida sai ta yi masa ƙorafi a kan kai wa daren da yake yi a waje. Miƙewa ta yi ta fito falo, Nazir ya rufa mata baya. Kayan abincinsa ta ɗebo ta ajiye masa har ta miƙe za ta koma ɗaki ya riƙo hannunta.
"Maimuna kwana biyu na ga duk kin sauya, me yake damunki ne?"