Sashe 15
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Dakata Gambo don Allah, wannan sabgar iyalina ce. Ban ce ka tsoma bakinka a ciki ba, wallahi sai ta fitar da kajin nan tun da Shukura ba ta son warinsu. Idan kuma rabuwarmu ta zaɓa, a yanzu sai na rubuta mata takardarta ta kama gabanta." Yana gama maganar ya wuce fuu har zai fita, sai ya sake waigowa ya ce.
"Kuma daga yau babu kai babu sake shiga duk wata magana ta iyalina, kai ma idan har ka ce za ka bi wani ra'ayin ba na Shukura ba, a shirye nake da na datse duk wata alaƙa da ke tsakanina da kai." Daga haka ya saka kai ya fice.
Daga Mommy har Alhaji Gambo jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, saboda ɓacin rai sai kawai ta fashe da kuka.
GIDAN HAFIZ
"Za ki buɗe baki ki yi mini magana, ko sai ranki ya ɓaci?"
Hafiz ya buga wa Amina tsawa a zafafe, hawaye ta shiga yi baki yana rawa ta ce.
"Wallahi... ban... san yadda aka yi ba, wallahi ban san komai game da wannan layar ba."
Furzar da iska mai zafi Hafiz ya yi, zuciyarsa tana tafasa ya matsa kusa da ita kamar zai tsinka mata mari. Da sauri Amina ta ja da baya cikin matsanaacin tsoro, don ta gama saddaƙar da Hafiz hannu zai kai jikinta. Rai a ɓace ya nuna ta da yatsa ya ce.
"Uwargidana, kuma uwar 'ya'ya ko hanyar gidan malamai ba ta sani ba, haka kawai ina zamana lafiya da matata za ki haukata mini ita. Shi ya sa kullum take yin abu kamar na mai shafar aljanu, ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni. Wallahi idan na sake ganin makamancin wannan shirmen sai ranki ya yi mugun ɓaci. Saboda mugun hali ki zo ki samu mace a ɗakinta kina ƙoƙarin illatata, ba zan juri ki zo ki hargitsa mini gida ba."
Hafiz ya juya ya fita, kai tsaye kicin ya shiga ya ɗauko ashana ya fita da layar ya ƙona a waje. Duk abin da yake faruwa Bikisu tana daga ɗaki tana ji, zuciyarta fes don haka ta cigaba da harkokinta hankali kwance.
Tun daga wannan ranar Bilkisu ta warware tas, ta daina duk wani makircin nesanta kanta da Hafiz. Wannan ya sake tabbatar wa da Hafiz zarginsa na Amina ce ta yi wa Bilkisu asiri, dalilin haka ya ƙara tsaurara tsattsamar alaƙa tsakaninsa da Amina. Suka koma irin zaman cin kunamar ƙadangare, don Amina wani haushin Hafiz take ji a kan abin da ya yi mata. Shi ma kuma haushinta yake ji, don haka ya koma kwanan falo. A kullum idan a ɗakinta yake zai ɗauko filo ya fito falo ya kwanta, saboda idan ya kwanta a kan gadon ma sai dai Amina ta juya masa baya.
A wannan kwanakin Bilkisu sai nannan take da Hafiz kamar ta haɗiye shi, haka shi ma yake ba ta kulawa; saboda yadda ya ga ta saki jiki da shi saɓanin tun lokacin da ya auri Amina. Watarana Hafiz yana ɗakin Amina, har ya yi shirin zuwa kasuwa sai ya shiga ɗakin Bilkisu don ya yi mata sallama. Yana shiga bisa tsautsayi hannunta da manja ya kife masa a gaban riga, a kan dole ya shiga uwar ɗakinta ya cire kayan jikinsa ya ɗaura towel. Da yake Bilkisu ta ɗora ruwan wanka, sai ta ce bari ta juye masa ya sake yin wanka tun da duk jikinsa ya ɓaci. Sai da Bilkisu ta shiga uwar ɗaki ta ɗauro zani, sannan ta je ta juye masa ruwan a banɗaki. Hafiz ne ya shiga banɗaki cikin sauri, saboda ya yi rana bai fita da wuri ba. Bilkisu tana ganin haka ta yi zaraf ta fito tsakar gida, sai da ta je bakin ƙofar ɗakin Amina ta yi ƙasa da murya yadda Hafiz ba zai ji ba ta ce.
"Ban da abin Abban Sayyid ka ce ba ka gajiya da ni saboda Allah, tun da dai ba kwanana ba ne ai sai ka bari sai ka dawo nan ɗin tun da ba guduwa zan yi ba. Ga shi haka kawai za ka saka ni jiƙa kaina ban shirya ba." Da ta tabbatar da Amina ta ji abin da ta faɗa, sai ta ce.
"Koda yake bari na zo na taya ka, tun da shi ma sunna ne."
Ta nufi ƙofar banɗakin tana gimtse dariyar mugunta, tana zuwa cikin sanɗa ta tsaya a ƙofar banɗakin. Saboda ta san ko kaɗan Hafiz ba zai bari ta shiga su yi wanka tare ba, tun da ba ranar girkinta ba ne. Tana jin motsin zai fito ta ce.
"Idan ka gama Abban Sayyid ba ni bokitin ni ma zan yi wanka."Ajiye mata ya yi, sai ya wuce ya shiga É—akin Amina ya sauya kaya ba tare da ya tanka mata ba. Tana ganin ya saka wasu kayan ya fita, ta shiga uwar É—aki ta fashe da kuka. Sai da ta yi mai isarta sannan ta share hawayenta, ta kwanta tana jin gabaÉ—aya zaman gidan ya ishe ta. Uwa-uba ga laulayin da take fama da shi, don a wannan lokacin ko abincin kirki ba ta ci.
Bilkisu tana fitowa daga wanka ta shige ɗaki, sai da ta shirya tsaf sannan ta ɗauko wayarta ta kira Lami mai wanki. Tana ji an ɗauka ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Yawwa Lami na haɗa kayan wankin namu, ki aiko yaro ya zo ya ɗauka. Da nawa da na yara gabaɗaya set goma sha biyar ne, yawwa akwai kuma na Abban Sayyid za ki gansu daban. Su kuma sai ki ba wa Babansu Bala (Mijin Lami) ya wanke ya goge. Idan an gama sai a yi mini lissafi zan bayar da kuɗin." Amsa mata Lami ta yi sannan ta katse wayar, da sauri ta matsa bakin ƙofa. Sai ta latsa ainahin ringing ɗin wayarta ta ware volum, sai da ya yi na ɗan sakanni sannan ta kashe. Sai ta kai shi kunne a zuwan kiranta aka yi ta ce.
"Hello Abban Sayyid, ka yi mantuwa ne?"
Sai ta yi shiru kamar wacce ake yi wa magana ta sake cewa.
"Kai Abban Sayyid yanzu bayan kuɗin makarantar yara da aka ƙara ga hidimar gida har da wanki? To shi kenan, bari na karɓo na wajen nata, Allah Ya ƙara buɗi Habibi." Sai ta yi ƙasa da murya kamar mai kukan gaske ta ce.
"Haƙiƙa samun miji kamarka sai an tona Zauji, Allah Ya kula mini da kai." Daga haka sai Bilkisu ta ƙarasa ƙofar ɗakin Amina ta yi sallama, jin ta amsa sai ta ce.
"Abban Sayyid ya ce ki haÉ—o kayansa na É—akinki za a kai wanki."
A sanyaye Amina ta amsa mata, sannan ta shiga ɗaki ta haɗo kayan wankin Hafiz ta kawo mata. Sai da ta karɓa ta ɗan yamutsa fuska ta ce.
"Ni kam ko ba kya jin daɗi ne Auntyn yara? Na ga tun safe kina ɗaki." Murmushin yaƙe Amina ta yi ta ce.
"Ba na jin daÉ—i ne shi ya sa."
Bilkisu ta rausayar da kai alamun tausayi ta ce.
"Ayya sannu, dama kin san fa sai an rabu ake jin daɗin jiki. Ni na yi mamaki ma, da Abban Sayyid yake fita ba tare da ya yi miki share-sharen ɗaki ba, don lokacin cikin Sayyid hatta moping sai ya yi mini yake fita." Wani zafi Amina ta ji a ranta, tana ayyana wato ita da yake ya daina sonta ko gyaran gado bai taɓa yi mata ba. Bilkisu ta saci kallon Amina a fakaice sannan ta ce.
"Kodayake bari na dinga rage miki wasu ayyukan, ai ban san ba ki da lafiya ba." Tana faÉ—ar haka ta fice, sannan ta É—ebo kayan wankinta ta fito da su tsakar gida ta É—auki waya ta kara a kunne bayan wani lokaci ta ce.
"Hello, Abban Sayyid." Shiru ta yi sai ta sake cewa.
"Ashe Amina ba ta jin daɗi tun safe, na ce ko na karɓi kayanta a haɗa da namu a kai wankin? Tun da ka ga kayana da na su Sayyada ba su da yawa." A wannan karon ma shiru ta sake yi, sai bayan wani lokaci tace.
"A'a don girman Allah ka yi haƙuri, ya za a yi ka ce ka rantse ba za a haɗa da nata ba. Don Allah kada ka yi haka ba za ta ji daɗi..."
"Don Allah ki daina yi masa magiya Aunty, tun da bai yi niyya ba ai shi kenan. Wanki ai ba zai kashe ni ba."
Amina ta furta cikin zafin zuciya, don a wannan karon ta gagara riƙe ɓacin ranta.
Girgiza kai Bilkisu ta yi ta ce.
"Haba ta ina za a yi haka, to ai kuwa nawa ma sai dai a bar shi gaskiya." Jim ta yi kamar mai sauraren abin da yake faÉ—a, sai ta ce.
"To shi kenan, ka yi haƙuri zan bayar da su. Wai dama don kada ta ji babu daɗi ne ya sa na yi maganar, amma tun da maganar kayan na ta ya ɓata maka rai ka yi haƙuri." Bilkisu tana sauke wayar sai ga Habibu ɗan gidan Lami ya yi sallama, kayanta da na Hafiz ta haɗa ta ƙulle ta ɗaura masa a kansa. Amina tana shiga ɗaki, ta ɗauko hijabinta ta zura sannan ta rufe ƙofarta ta fice ko sallama ba ta yi wa Bilkisu ba. Tana jin zuciyarta na zafi, don yadda ta fita daga gidan ta ci alwashin ba za ta koma ba sai dai Hafiz ya kai mata takardar sakinta.
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[17/06, 18:06] Ameera Adam: *DAHUWAR ƘAHO*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GargaÉ—i: Ban amince a sarrafa mini littafi ta kowacce siga, ko a karanta shi a kafar sadarwa, ko É—orawa a wata manhaja ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba, idan ya yi daidai da yanayin labarinki/ka arashi ne.
SHAFI NA TARA
ALL NATURAL PRODUCT💃ðŸ»
Tsumi
Tsumin tighten
Tsumin Sanyi
Tsumin basir
Tsumin 3in1
Kazar Amare yan mata.
Kazar Amare zawarawa.
Kazar Masu haihuwa.
Kazar 3in1
Kazar uwargida ko amarya da suke son burge oga.
Gumbar dabino.
Gumbar kwakwa.
Gumbar Madara.
Garin dahuwar kaza.
Garin dahuwar ciccibi.
Garin dahuwar hanta.
Garin dahuwar kwai.
Garin dahuwar kifi.