← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 81

Sashe 61

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laraba ba ta yi tsammani ba ta ji ya zuba mata bulala a baya, don haka ta taƙarƙare ta fara yi masa wani irin yare wanda ita kansa ba ta san me yake nufi ba. Duk yadda Malam sule ya kai ga mazewa sai da ya kawar da kai ya saki murmushi, sannan ya ce ta fassara da hausa. A nan ma Laraba babu tsiyar da ta tsinana, sai sokiburutsu da ta dinga yi masa. 'Yan ajinsu kuwa suka shiga ƙyaƙyata dariya suna yi mata ihu, Laraba ta ƙulu sosai don haka ta yi kukan kura ta faɗa kan Suwaiba ta rufe ta da duka, don ta fi jin haushinta dama saboda har gwalo take mata tana raɗawa na kusa da ita abin da za su faɗa. Da sauri Malam Sule ya fisgo Laraba saboda ya yi mata maganar duniya ta ƙi ji, ya shiga dukanta da zafafe. Zuciya ta kuma ciwo Laraba ta sake cukumo Suwaiba, tana kai mata naushi a baki har sai da ya fashe. Malam Sule mari ya zabga kata, sai a lokacin Laraba ta ja da baya ta dube shi a haukace cikin ɓacin rai ta ce.

"Kai malam kada ka sake dukana, wai ba kai ne ɗan gidan Bala mai satar agwagwa ba ko an faɗa maka ba mu sani ba." Wani abu ne ya caki zuciyar Malam Sule, saboda bai taɓa tunanin za ta yi masa wannan bankaɗar ba. Cikin borin kunya ya rufe ta da duka, sai da ya zane Laraba sannan ya riƙe hannunta ya dinga bin ajujuwa da ita, yana saka kowanne prefect ya yi mata bulala biyar kuma 'yan aji su yi mata ihu. Ranar zuciyar Laraba ta gama dagulewa, don haka ta ci alwashin ko sama da ƙasa ce zaata haɗe ba za ta ƙara zuwa makarantar ba. Kuma sai ta hukunta iyaye da 'ya'yan da suka ci zarafin, shi kuma Malam Sule ta ci alwashin sai ya yabawa aya zaƙinta a wurinta.

Duk irin zaman doya da manjar da suke yi tsakanin matan Yaya Inu, sai da suka ji jikinsu ya yi sanyi a kan sakin da ya yi wa Abu. Duk da ba baƙon abu ba ne a wurinsu amma irin son da suka san Yaya Inu yana yi mata ne ya ba su tsoro domin ba su taɓa tsammani ba. Hansatu ta fi kowa shiga damuwa saboda duk matan da Yaya Inu yake saki, idan suna da yara ƙarƙashin kulawarta suke komawa, kasamcewar ita ce uwargida a wannan lokacin. Sun jima suna janjantawa da suka ji motsinsa sai kowacce ta shiga aikin gabanta.

A yanzu Indo ita ce matar Yaya Inu ta uku, ita ce take bin Larai. A ƙalla ta kai shekara huɗu a gidansa, 'ya'yanta uku duka maza. Babban ɗanta Uzairu bai fi shekara uku da watanni ba, sai mai bin sa Ya'u mai shekara ɗaya da rabi. Sai kuma jaririn da take goyo mai wata shida Hannafi.
A washegarin ranar da aka saki Abu akwai bikin da matar yayan Indo ta gayyace ta, a wani ƙaramin gari da ke gaban garinsu. Tun safe Indo ta katsa wanka ta ɗauko galleliyar atamfarta yadi ta saka, ta yi wa su Larai sallama tana jin kamar za ta je wata sabuwar duniya. Larai a ranta take jin dama ita ce take da 'yan uwa a birni, da suke biki har ake gayyatarta da ko babu komai ta samu abin yi wa su Hansatu gori.
A gidan kamun bikin da Indo ta je ne, ta tarar da wata mata da aka ɗauko Hajiya Zanni mai gyaran aure tana yin lecture ma'aurata. Matar irin masu safarar magungunan mata daga Kano zuwa Saudiyya ne, ita take koyar da su kissa da dabarun jan hankalin miji wanda zai mallake zuciyar miji. Saboda yadda take yin lacture cikin batsa ya sa mata sai shewa suke, mafi yawa daga ciki suka ƙuduri niyyar yi wa mazajensu daga ciki har da Indo, da take ganin kamar ta mallake Yaya Inu ta gama. Daga ƙarshe Hajiya Zanni mai gyaran aure ta ɗebo magunguna ta fara tallatawa.
Jikin Indo yana rawa ta zaro ɗan canjin jakarta ta sayi wani magani mai suna, kin yi wa kishiya fintinkau da idonka idona. Cike ɗoki Indo ta tafi gida, koda ta je gida haka ta dinga kallon su Larai a sheƙe tana yi musu kallon tausayi, mai tafe da izgilin na yi muki nisa don a yanzu sai yadda na yi da mai gida.

Daɗin sai ya haɗe mata biyu sakamakon ita ce da girki ranar, tun kafin magriba Indo ta gama komai. Ta caɓa wanka, ta ɗauko wani turarenta na Binta sudan, ta bulbule jikinta da shi kamar yadda ta ji Hajiya Zanni ta ce namiji yana son ƙamshi. Indo har ƙaguwa ta yi a idar da sallar Isha'i Yaya Inu ya shigo gida, sai ga shi a ranar ya yi jinkirin shigowa don har kusan goma saura. Haka ta zauna a gefen gado har ta fara gyangyaɗi, sannan ta ji shigowarsa. Da sauri ta ɗauko Hannafi ta kai shi gefen Uzairu ta kwantar da shi, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce ba a zuwa turaka da yara suna takurawa uwargida da mai gida. Turarenta na Binta sudan haɗe da jan miski ta ɗauko ta sake bulbulawa, ta janyo wani fakeken gajeren wandonta a drower shi ma ta shafe shi da jan miski. Ta nufi ɗakin Yaya Inu hannunta ɗauke da tiren abinci, dama daga ita sai ɗaurin ƙirji wanda hakan duk yana cikin lecture Hajiya Zanni. Tana shiga ta ajiye masa abincin a gefe sai kuma ta ja ta tsaya a wurin, Yaya Inu ya ɗago fitilarsa ya haske ta yana shirin yi mata magana sai ya ga Indo ta saki zanin jikinta ya faɗi ƙasa. Saboda duk huɗubar da Hajiya Zanni ta yi musu ta haddace ta kanta. Da mamaki Yaya Inu yake bin Indo da ke tsaye tumɓur sai ɗan kanfai, da wata sakakkiyar rigar mama a jikinta wacce suk ta zuge ta saki kamar gugar jan ruwa saboda yawan sakawa.

"Ke Indo lafiyarki kuwa?"
Yaya Inu tambaya a tsorace.
Indo ta ji daɗi har ranta, don ta ji Hajiya Zanni ta ce akwai wani shauƙi da miji yake shiga idan an yi masa haka. Indo ta fara harba ƙafa tana wani juyi ita a dole rawar India za ta yi a gabansa, Yaya Inu zai sake magana Indo ta wurga masa wannan burgujejen gajeren wandon da ta ɗauko, wanda ta jiƙe shi sharkaf da turaren miski da Binta sudan. Gajeren wandon ya sauka a saman fuskar Yaya Inu, ya yi sakatoto yana bin ta da kallon mamaki. Indo ta yi wani tsalle tana harba ƙafa haɗe da fisge rigar maman jikinta, kusan lokaci ɗaya ta kifar da kwanon miyar abincin Yaya Inu. Kuma a daidai lokacin rigar maman ta faɗa saman wuyan Yaya Inu da ya gama kai wa wuya.

07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[10/12/2024, 19:47] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

SHAFI NA BIYAR

Ko kaɗan Indo ba ta damu da ganin ɓarnar da ta yi masa ba, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce duk cikin sirrikan da ta ba su babu na yarwa indai a ɓangaren mallaka da saye zuciyar miji ne. Don haka ta yi wata girgiza ta cake a wuri ɗaya, ta fara miƙa masa hannu ɗaya irin yadda jaruman india suke yi, idan za su miƙa wa masoyinsu hannu domin su yi rawa. Ta miƙe ƙafa gaba da zummar ta yi tsalle ta dira a gaban Yaya Inu, ta yadda za ta ɗago shi ta manna a jikinta kamar yadda Hajiya Zinni ta kwatanta musu, bisa tsautsayi ƙafarta ta harɗo labulen ɗakin ya faɗo a kanta. Kukan Hannafi ta fara ji sama-sama da alama ya tashi daga bacci, amma sai ta basar ta tunkari Yaya Inu da zuciya ta gama cika shi. Don yadda yake ji ransa ya ɓaci kamar ya tashi ya shaƙe Indo, saboda wannan sabon iskancin da take ƙoƙarin kawo masa. A gabansa ta tsaya tana wani rangaji, iska ta fara kaɗo cikin ɗakin saboda sanyin da ake busawa. Burgujejen gajeren wandonta ya fara kaɗo fuskar Yaya Inu, Indo ta yi masa wani far da idanu ta ƙanƙance murya ta ce.

"Taso mu yi rawa lantarkin zuciyata..."

Kalaman Indo suka katse sakamakon fisgowar da Yaya Inu ya yi mata, ta faɗi ƙasa daɓas! Gwiwoyinta suka bugu da ƙasa.
A tsammanin Indo shauƙin da Hajiya Zanni ta ce maza suna shiga ne ya fara kama Yaya Inu, don haka ta shanye zafin da ta ji ta sake wurƙila idanu da sunan fari tana wani banƙarewa kamar kazar mayu ta ce.

"Na jima ina alla-alla kwanakin girkina su dawo, saboda na shayar da kai romon soyayya..."

Takaici ya sake lulluɓe Yaya Inu, ya ɗaga hannu ya yi wa Indo mahangurɓa a fuska. Wani irin mummunan yanayi ya ratsa ta, don haka a gigice ta miƙe da niyyar ceton kanta. Yaya Inu ya shatalo ta da ƙafarsa ta faɗa kan miyar kukar da ta zubar.
A fusace ya É—aga hannu ya zabga mata mari cikin fusata ya ce. "Wannan iskancin a gidan uban wa kika koyo shi? Wallahi ko kukar bulukiya ce a kanki sai na sauke miki ita."

Indo ta fashe da kuka tana jan jiki gefe ta ce, "Yanzu mai gida duk abin da na yi maka ban birge ka ba, saboda Allah duk wannan kissa da kisisinar..."
Chapter 61 · 0% Book details