← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 81

Sashe 42

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fuska babu walwala ta ce, "Me ka gani?"

"Na ga kwana biyu kamar ba ki damu da ni ba, kuma ni dai na san ba wani abu na yi miki ba."
Nazir ya furta a sanyaye.
"A'a babu abin da yake damuna kawai dai baccin da na tashi ne!"

"Ba haka ba ne Maimuna, a 'yan kwanakin nan ko ƙarfe nawa na dare zan kai ba za ki kira ni ba, idan na dawo kuma ba za ki tambaye ni dalilin kai wa daren da na yi ba. A yanzu ko zan kwana ina chatting uffan ba za ki ce mini ba, ni sai na ga kamar haushina kike ji."

"A'a ni babu wani haushinka da nake ji, ai kowa rayuwar da ya ga dama ita yake yi. Tun da na lura kulawar da nake ba ka ce ta sa kake yi mini wasu abubuwan, don haka na bar wahalar da kaina."
Maimuna ta sake yin maganar tana shirin tafiya.

"Zauna mana, yau fa hira nake son mu yi. To yanzu dai ki yi haƙuri, ga biskit da chocolate nan na taho muku da shi ke da yara."

Ta fahimci sarai hirar da yake nufi, domin dama ba ta cika amfani a wurin Nazir ba sai yana buƙatarta. Sau tari idan hakan ta taso babu wata kulawa da nuna soyayya haka kawai zai afka mata, ta kawar da kai gefe ta ce.
"Ai kuwa sai dai ka yi haƙuri zuwa gobe kaina matsanancin ciwo yake, shi ya sa ma na sha magani na kwanta ɗazu." Tana gama maganar ta janye hannunta ta wuce ɗaki, kamar sakarai haka yake bin Maimuna da kallon mamaki. Ya san dai Maimuna ba shiga gidan kowa take ba, ballanta ya ce maƙota ne suke zuga ta. Kuma ya santa da ƙorafi matuƙar ya ɓata mata rai ko bai san laifin ba za ta fito ta sanar da shi. Da sauri ya tashi ya bi ta ɗakin a lokacin har ta ja bargo ta rufa, ransa ya sake ɓaci amma sai ya saita nutsuwarsa ya ce.
"Magana nake yi miki fa Maimuna kika shigo É—aki."
Tana daga kwance ta É—ago ta ce, "Ni ma ai amsa na ba ka Abban Asiya."
Ƙwafa ya yi ya juya ya fita, ya zauna ya cigaba da cin abincinsa. Sai da ya gama uzurinsa sannan ya shiga ɗakin ya kwanta a gefenta, juyi yake shi kaɗai yana mamakin sauyin halinta. Don haka ya so danne buƙatarsa amma sai ya gagara, hannu ya kai ta janyo ta kamar tana jira ta ture shi tana faɗin.
"Haba Abban Asiya, wai me kake yi haka na ce maka ban da lafiya fa."

"Kin sauya Maimuna, Me ya sa kike son horar da ni ne? Yau rabona da ke kwana nawa, rannan kin ce mini zazzaɓi kike. Shekaran jiya kin ce ciwon baya, yanzu kuma kin ce mini kanki yana ciwo. Idan kina ganin ba za ki iya ba ni haƙƙina ba sai na ƙara aure." Nazir ya furta cike da barazana saboda ya san Maimuna tana da kishi, amma cikin halin ko in kula ya ji Maimuna ta ɗago ta ce.

"Sai me don ka yi aure Naziru? A kaina za ta zauna? Ko ni zan ciyar da ita, ruwanka ne ka ƙara aure kuma ruwnaka ne ka bari na samu lafiya. Idan kuma ƙarin auren ka ga shi ya fi maka mafita wallahi ni ko a gefen takalmina."

Tsoro ne ya kama shi saboda ya ji an ce idan mace ba ta ba ka kulawa, ba ta nuna kishi a kanka kawai zama take yi da kai ba don soyayya ba. Da a ce a shekarun ba ya ne ba zai yi mamakin jin haka daga gare ta ba, amma yanzu da shekarun aurensu suka tura ya lura duk ta zubar da makamanta.

"Au haka kika ce?"

Nazir ya faÉ—a a zafafe.
"Eh haka na faÉ—a, tun da kishiya ba a kaina aka fara ba." Tana gama faÉ—a ta sake gyara kwanciyarta.

Cike da kewar Maimuna Jafar ya nufi gida, a lokacin da ya shiga ƙarfe goma sha ɗaya da rabi. A zaune tunkur ya samu Maman Nana da alama jiransa take yi, ya shiga ɗakin kamar bai ganta ya fara rage kayan jikinsa.

"Abban Nana wato fitar da ka yi gidan su budurwarka ka tafi ko?"
Bai waiwayo wurinta ba ya ce, "In ji wa?"

"Sai an faÉ—a mini?"

"To tunaninki bai harsaso miki daidai ba." Shi ma ya faɗa fuska a haɗe. Hakan kuwa ya sake harzuƙa ta, rai a ɓace ta ce.
"Wai Abban Nana me kake nufi ne? Ka bi ka sauya mini lokaci É—aya na rasa gane kanka, da idan ka shigo gidan bayan sallar Isha'i ba ka sake fita sai washegari. Amma yanzu kana gama cin abinci sai ka fice ba za ka dawo ba sai dare, na gaji fa wallahi na gaji da irin cin kashin da kake yi mini."

"To idan ba za ki iya ba sai ki nemawar kanki mafita."

Ta riski miyagun kalamansa a cikin kunnuwanta, ƙirjinta ya buga da ƙarfi. Cike da tsoro ta dube shi amma sai ta nuna masa ba ta fahimci abin da yake nufi ba ta ce.

"Me kake nufi?"

"Ina nufin idan ba za ki iya zama da ni da ki kama gabanki."

Wani irin dum! Ta ji kamar an kwaÉ—a mata guduma, da sauri ta runtse idonta ta buÉ—e su a kansa. Ta taka gabansa muryarta tana rawa ta ce, "Abin da za ka ce mini kenan Abban Nana? Dama ka gaji da ni ban sani ba?"

"Ko ban gaji da ke ba wulaƙancin da kika tarko ne ba zan ɗauka ba, na lura samu ma yana saka mace ta yi iskancin abin da take so. Amma babu damuwa tun da irin zaman da kike so mu yi shi kenan."

Shiru ta yi kamar ruwa ya cinye ta, ta shiga nazari daga safiyar ranar zuwa dawowarsa ko za ta iya tuna laifin da ta yi masa amma ba ta iya tunawa ba.

"Don Allah ka faÉ—a mini laifin da na yi maka Abban Nana?"

Bai tanka mata ba ya saki tsaki ya ɗauki fulo ya koma kan kujera ya kwanta. Abin duniya ne ya haɗe wa Maman Nana, sai ta ji ya fara ba ta tsoro domin lamarin nasa ƙara yin gaba yake yi. Don haka ta shiga alla-alla gari ya waye ta leƙa gidan Maimuna ko ta ba ta shawarwarin abin da za ta yi.

Washegari

Tun da Jafar ya yi sallar Asuba bai koma ba, gari yana yin haske ya shiga cikin kitchen ya É—auke tukunyar cilinder gas ya fice da ita. Da yake Maman Nana ba ta tashi da wuri ba, saboda a daren bacci bai É—auke ta da wuri ba ko kaÉ—an ba ta san wainar da ake toyawa ba. Sai da ta ji alamun buÉ—e gate ta tashi ta fito, a tsammaninta Jafar fita ya yi kasuwa.
Banɗaki ta shiga bayan ta fito ta shiga kitchen za ta shirya wa su Nana abin breakfast da na makatanta. Amma sai ta ga wayam babu clinder, ba ta kawo komai a kanta ba; sai ta yi tsammanin ko ƙaro musu gas zai yi saboda idan ya ga ya kusa ƙarewa yana ɗauka ya ƙaro mata.
Tana daga ƙofar kitchen ta hango shi yana kokawar shigowa da ƙaton buhun gawayi, sai da ya ƙarasa ya jingine shi sannan ya sake fita gate ya sauke mirgino buhu na biyu. Maman Nana tana tsaye ya gama dire buhunnan gawayin har guda biyar, sannan ya ɗauko kurfoti ya dire a gabanta. Fuska a haɗe ya ce, "Daga yau ga abin da za ki dinga girki da shi, gas ya sake tsada ba zan iya sayensa ba. Cilnder ma na sayar wa mai shagon da nake sako mana gas, sai a ci gaba da malejin rayuwa tun da komai tsada yake sake yi." Jafar yana gama faɗar haka ya shige ɗaki.

Kabir kwance ya yi a kan gado, yana jin haushin kansa a kan abin da ya aikata. Fushin Fauziya ya fi komai ɗaga masa hankali, don Fauziya mace ce mai haƙuri da sauƙin kai. Amma idan ta yi fushi ba ta iya zuciya ba, juye-juye ya fara yi yana hangen ta da take kwance idonta biyu tana hawaye. A hankali ya tashi zaune ya tsugunna a gefenta murya a sanyaye ya ce.

"Fauziya! Don Allah ki tashi mu yi magana, ba na son ki saka kanki a cikin wani hali saboda yanayin da kike ciki."

Ɗagowa ta yi ta dube shi, tana jin sautin muryar martanin batsar da yake mayarwa da Hafse a cikin kunnuwanta. Zuciyarta ta shiga zafi, wani abu ya tokare ƙirjinta. A hankali ta fara jin mararta tana tsira mata, ta cije bakinsa tana girgiza kai.

"Don Allah ki yafe mini..."

"Idan ka sake yi mini magana zan fice daga gidan nan na ba ka wuri."
Ta katse shi da wani irin sauti, kamar sabon munafiki haka Kabir ya ja jiki yana sunne kai ƙasa ya koma kan gadon ya zauna.
A cikin wannan daren daga shi har Fauziya bacci rabi da rabi suka yi, sai bayan Asuba ta samu bacci mai hauyi ya yi awon gaba da ita.
Tun da Kabir ya tashi bai koma ba, saboda ya san ya yi wa Fauziya laifi a hankali ya dinga aiki don kada ya tashe ta. Shi ya dafa wa yara abinci, ya shirya su suka tafi makaranta. Sannan ya shiga ɗakin ya share mata, kwanukan wanke-wanken kuma ya ajiye a bakin rariya zai wanke mata. Lawisa tana sanye da hijabi tana girki a bakin ƙofarta ta hango shi ya tsugunna zai yi wanke-wanke, miƙewa ta yi ta ƙarasa wurin ta ce, "Baban Na'ima ka bari zan wanke mata, ko jikin Maman Na'iman ne." Kabiru ya ɗan sosa kai ya ce, "Eh ta tashi ba ta jin daɗi ne, shi ne ta ɗan kwanta zan rage mata aikin."
Chapter 42 · 0% Book details