Sashe 51
Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Waɗannan mutanen da kika gani ƙarshen butulaye ne, ba su san karamci da hallaci ba Fauziya. Hakan shi ya fi mini alheri In Shaa Allahu."
Sadiya tana gama magana ta miƙe ta shiga ɗaki, kayan jikinta ta sauya. Ta ɗauko wata ƙatuwar jakarta ta loda kayanta a ciki, hijabinta ta saka ta fice daga gidan. Maƙota ta dinga bi tana karɓar kuɗaɗen waukau da take bi, sannan ta ƙarasa titi ta taro Mai adaidaita sahu har ƙofar gida. Kusan a inda ta bar Fauziya a nan ta koma ta same ta, suna ganinta gabaɗaya suka yi kanta cikin sanyin jiki. Ɗaki ta shiga ta jango ƙatuwar jakartata, Salim da Zainabu suka ƙarasa suka rungume ta suna kuka.
"Don Allah kada ki tafi Umma."
"Umma idan kika tafi Inna dukanmu za ta yi."
Suka furta cikin kuka, hawayen da Fauziya take riƙewa ne ya fara zuba. Ta saka hannu ta toshe bakinta tana kuka, Sadiya ta haɗiyi yawu mai ɗaci hawaye masu zafi suka shiga tsiyaya daga idanunta. Cikin tausasa lafazi ta riƙo hannunsu ta ce, "Zan dinga zuwa ina ganinku lokaci-lokaci, Allah Ya yi muku albarka Zainabu."
"A'a mu dai ki tafi da mu."
Zainabu ta faɗa tana hawaye. Da sauri Yaya Nura ya ƙarasa a fusace ya fisge hannunsu yana faɗin, "Duk wanda na ƙara jin muryarsa sai na taka wuyan yaro." Fauziya ta ƙarasa cikin kuka ta ce, "Don Allah ka bari ta yi sallama da 'ya'yanta cikin salama, wannan hawayen da ka ga suna fitarwa har abada ba za su manta da shi ba."
"Da ta san tana ƙaunar yaran take ƙin yin haƙurin zaman gidan ubansu."
Sadiya ta dube shi cike da tsana ta ce, "Kada ki damu Fauziya, ni uwa ce na tabbata duk daren daɗewa za su nemo ni. Hakan da ya yi ba shi zai sa su kankare ni a matsayina na mahaifiyarsu ba, ba don na san halin mugun halin gidan nan ba. Da sai na damƙa miki amanar 'ya'yana, amma na san wacece ke Fauziya da kyakkyawar zuciyarki. Ina fatan Allah ya sada mu da alheri.
Fauziya ta rungume Sadiya tana hawaye, a hankali ta janye jikinta tana jan jaka har ƙofar gida. Ganin haka ya sa su Salim suka saki matsanancin kuka suna ƙwala mata kira. Sadiya ba ta waigo ba sai ma hawaye da take zubarwa, jakar ta saka a cikin adaidaita sahun. Har ta zauna a ciki tana jin ihun Zainabu da take ƙwala mata kira tana ihu, sai kawai ta kifa kanta a kan cinyoyinta ta saki gunjin kuka mai cin zuciya.
GIDANSU MAIMUNA
Shirun da Maimuna ta yi ya sa Jafar ya ce, "Kin yi shiru My Moon."
Maimuna ta ce, "Gaskiya tsoro nake ji, kada tsautsayi ya sa Nazir ya dawo bai same ni a gida ba. Ka san akwai matsala tun da ba barina fita yake ba, ni dai ina ganin mu cigaba da yin video call hakan zai fi." Ba don ya so ba ya narke mata ya ce.
"To ya na iya baby? Amma dai gaskiya ki rage mini kayan jikinki, na fi son na ganki sosai bari ni ma ki ga."
Jafar yana gama maganar ya jingine wayar a gefe, ya zame ragowar ƙananan kayansa. Ita ma Maimuna babu kunya, ta zame rigar jikinta. Ya rage daga ita sai rigar mama, can saman gadonta ta haye sannan ta ɗauki wayar ta ce. "Baby ka gama kuwa."
Ido suka haɗa ta cikin wayar, Jafar ya ji wani irin abu ya tsarga masa. Bakinsa yana rawa saboda shauƙi ya ce, "Mooooonnn." Yanayin yadda ya kira sunanta ya sa ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe ido, sai ta buɗe su tana ƙura wa faffaɗan ƙirjinsa mai cike da yalwataccan gashi da kallo.
'Haƙiƙa dole Maman Nana ta dinga ɓarin zancan a kanka, tabbas! Jafar ba irin ragowar sauran mazaje ba ne.'
Maimuna ta raya a ranta, tana shirin yin magana Jafar ya ce.
"Baby wai dama haka Allah ya zuba miki sura? A gaskiya Nazir ba ƙaramin dace ya yi ba."
Maimuna ta shagwaɓe murya ta ce, "Nazir ne ya yi dace ko Maman Nana? Allah Ya sani ba zan ɓoye maka ba Baby J. Wallahi za a daɗe ba a samu ingarman namiji kamarka ba."
Kalaman Maimuna suka sake kashe masa jiki, ya kwantar da murya cikin shauƙi ya ce.
"Ina ma yanzu haka a tare muke, da na shayar da ke romon soyayyar da ba ki taɓa sharɓa ba. Ina kewarki Moon, ina ƙaunarki komai ina ji a kanki Habibtee."
Maimuna ta saki murmushin jan hankali, suna cikin haka Jafar ya nemi Maimuna da ta cire rigar da ta rage mata, kamar ba za ta iya ba sai sheɗan ya sake ingiza ta. A hankali ta cire komai na jikinta, suka shiga musayar munanan kalaman batsa. Suna nuna wa junansu duka sassan jikinsu, Daga Jafar har Maimuna ba ƙaramin gigicewa suka yi da ganin surar junan ba. A haka har Jafar ya yi galaba a kanta, ta amsa masa gayyatar da ya dinga yi mata magiya. Maimuna ta amsa masa da cewar za ta shiga wurinsa washegari idan Nazir ya tafi kasuwa, tun da yaranta suna makaranta. Ya so ta shiga a ranar amma ta nuna masa yamma ta yi, yaranta za su iya dawowa daga makaranta. Daga ƙarshe suka yi sallama cike da kewar juna.
MAMAN NANA
Tun bayan da ta fita daga gida take tafe tana hawayen baƙinciki, ta biya ta makarantar su Nana ta ɗauke su suka wuce gidansu, yaran sai tambayarta suke yi ta ce musu ba ta da lafiya. Lokacin da ta je gida mahaifinta ya fita kasuwa, ta sanar wa mahafiyarta duk abin da ya faru. Ko kaɗan ba su ji daɗin abin da Jafar ya yi ba, amma ita ma sun yi mata faɗa sosai kuma suka ba ta rashin gaskiya.
Daddare bayan mahaifinta ya dawo, mahaifiyarta take sanar da shi abinda ya faru. Kiran Maman Nana ya yi, ta tunkari É—akin gabanta yana faÉ—uwa.
"Amma ban taɓa sanin ba ki da hankali ba sai yau Sumayya, an faɗa miki miji wasa ne da za ki cakumi wuyansa a kan yana waya da budurwa."
Mahaifinta ya rufe ta da faÉ—a bayan ta zauna.
"Baba marina ya yi fa a kan na ce mata 'yar iska, kuma don wulaƙanci a ɗakina yake waya da ita."
Mahaifinta ya girgiza kai ya ce, "Idan ya yi waya a É—akinki Sumayya, tambarin wayar ne zai fito a goshinki? Tun da kin faÉ—a da baki bai ji ba me ya sa ba za ki bar masa É—akin ba? Kin san maza kowa da irin halinsa ai, wani har ya gama neman aurensa mace ba za ta sani ba. Wani kuma a gabanta zai yi komai, to yanzu da kika yi hakan me ya rage shi?"
Maman Nana ta saka kuka, Baba ta nuna ta da yatsa ya ce.
"Daga yau kada na sake jin kin aikata wannan É—anyan aikin Summaya, idan kin ji yana wayarsa ki bar masa É—akin ko ki kama aikin gabanki. Kuma ko da wasa kada na sake jin ki kira budurwarsa da 'yar iska, ke ba a auren aka aure ki? Namiji ai mijin mace huÉ—u ne, bayan ita ma yana ikon neman guda biyu ya aura."
Cikin shasshekar kuka ta ce, "Baba ba za ka gane ba, Jafar duk ya canza mini kamar ba shi ba. Yanzu fa ko abinci bai cika ci ba, ga shi gas É—in da nake aiki ya É—auke sai buhun gawayi ya dire mini. Da na yi masa magana har gori ya yi mini, wai su Umma ma da itace suke amfani."
"Ƙarya ya yi? Ai ba ƙarya ba ne, ko ɗazu ma da shi kika ga na yi girki ai. Yaran yanzu ba ku ajiye komai ba sai baƙin kishin tsiya."
Mahaifiyarta ta yi maganar cikin faÉ—a.
"Tun da har yana ciyar da ke yana tufatar da ke, duk abin da ya kawo miki matuƙar ba guba ba ne sai ki karɓa, da hannu bibbiyu ki yi godiya ki sarrafa shi. Haba Sumayyan Baba ina ganin ki kamar mai wayo ashe ba haka ba ne, don Allah ki kiyaye gaba. Shi kuma zan kira shi ya zo na yi masa faɗa don a sharuɗɗan aure babu dukan mace a ciki."
Baba ya ƙarasa maganar cikin tattausan lafazi, sai ya ciro wayarsa ya latsa lambar Jafar ya ji ta a kashe. Ya mayar da kallonsa wurin Sumayya ya ce.
"Na kira mijinki wayarsa a kashe, yanzu dai dare ya yi babu damar ki tafi. Amma idan Allah Ya kai mu gobe da safe, ki shirya yaranki ki koma É—akinki za mu yi magana da Jafarun."
Maman Nana ta gyaÉ—a masa kai, Mahaifi da mahaifiyarta sun jima suna yi mata nasiha sannan ta tashi ta koma É—aki.
In Shaa Allah gobe za mu gama free pages, masu son littafin za su biya kuÉ—in karatu 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624
Idan kun ba ni haɗin kai zan yi ƙoƙari na kammala shi kafin Azumi🥹 idan kuma na ga kun wankacalar da ni, sai na bari zuwa bayan Sallah idan muna da yawancin kwana.🥸
Ummou Aslam Bint Adam🌚
07062062624
[20/02, 19:45] Ameera Adam: *NAUSHIN WUTA*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
GARGAÆŠI: Ban amince a sarrafa mini littafi da kowacce siga, ba tare da izinina ba. Yin hakan yana iya kai wa ga matakin Hukuma, don haka a kiyaye.
SADAUKARWA
Tun daga farko har ƙarshe, na sadaukar da wannan littafin ga duk mahaifiyar da ta kasance uwa; ko mai burin zama uwa a nan gaba. Allah Ya saka wa iyayenmu maza da mata da gidan Aljanna Amin.
SHAFI NA SHA BIYU