← Book details Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 81

Sashe 59

Dahuwar Kaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya wai saboda Allah wacce irin rayuwa kake yi haka? Yanzu don Allah kamar su Barau za ka kai birni makarantar allo? An ya kana tunanin goben yaran nan?"
Yaya Inu yaji kamar Baba Ibrahim ya zuba masa ruwan zafi, rai a ɓace ya mayar masa da martani.

"Kai Iro kada ka faɗa mini maganar banza da wofi, ba ɗazu ka gama faɗa mini magana a kan rashin iliminsu ba. Kai za ka faɗa mini na hango gobensu, akwai shege ɗaya a cikin gidan nan da yake ciyar mini da su? Tun da ni na samu kaina a gobena ai shi kenan! Daga yau ma kada wani ƙaton banza ya sake shiga hurumin iyalina." Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana fisgar Idi da ko wando babu a jikinsa ya yi waje da shi. Su Larai suka durƙushe a wurin suna sakin kuka.
Suna nan tsaye suka ji tashin motar, hakan ya sake É—aga hankalansu, a daidai lokacin Yaya Inu ya dawo yana muzurai yana harare-harare.

Bayan Sallar Isha'i

Zaune yake a matsakaicin ɗakin da aka ware masa, daga gabansa wani ƙaton fulas ne cike da farfesun kaji.
Sai da ya zuge tsokar cinyar kazar hannunsa, sannan ya ɗaga ƙaramar wayarsa ya danna wata lamba. Bugu ɗaya ta yi ya ji an ɗauka, ya yi ƙasa da murya ya ce.

"Barka da hutawa 'Yar gwal!"
Malam mai Yasin ya furta yana kurɓar romon naman, amsa masa ta yi sannan ta ce.
"Ni fa na gaji wallahi..."
Da sauri ya katse ta.

"Haba 'Yar gwal, na faɗa miki kwantan ɓauna na yi wa mutanen gidan nan, har na samu na aure tsohuwar nan. Ni na san Inno ba za ta ba ni matsala ba sai dai 'ya'yanta, amma ina aure ta magana ta ƙare. Tatsarta zan ta yi har na tara mana kuɗin da za mu hole, kada ki ji muryata ƙasa-ƙasa har yanzu nuna musu nake ba ni da lafiya."
Daga can ɓangaren 'Yar gwal ta saki dariya ta ce. "Shege Malam Gambo wallahi ko shaiɗan bai kai ka shaiɗanci ba."
Malam mai Yasin ya saki dariyar shakiyanci, suka cigaba da hira sannan suka yi sallama.

Ya kai kusan awa guda a zaune a bakin gadon yana yi mata firfita, saboda ko kaÉ—an ba ya son abin da zai dagula lissafinta. A hankali Rahina ta buÉ—e idanunta ta sauke su a kan mai gidanta Labaran, murmushi ya sakar mata ganin za ta tashi ya sa ya É—ago ta zaune sannan ya rungume ta sakar mata kiss a goshi.

"Barka da tashi masoyiya!"
Labaran ya furta cike da so yana jin kamar zai lashe Rahina. Fari ta yi masa da ido ta ce, "Wai tun da na kwanta kana zaune masoyi?"
"Ina zan matsa daga wurinki ƙaunata. Yanzu dai bari na sirka miki ruwa ki yi wanka. Ya ƙarasa maganar ya fita daga ɗakin."
Rahina ta bi bayansa da kallon soyayya tana jin tamkar ita kaɗai ta yi dacen miji a duniya. Tana nan zaune ya dawo ya riƙo ta, ganin za ta tuɓe kaya ya saka hannu ya fara rage mata.
Rahina ta ɗaura zani ta yafa ɗan kwali a kanta, Labaran ya riƙe mata hannu ɗayan hannun nasa yana riƙe da kwandon wanka suka nufi hanyar banɗaki. Sai da ya ga ta shiga banɗakin, sannan ya koma domin ya zuba mata abincin da za ta ci idan ta fito. Rahina irin matannan ne masu tsayi da ƙiba, shi kuma Labaran ɗan tsamurmuri ne ko tsayin kirki ba shi da shi. Yadda yake son Rahina da kishinta ji yake zai iya aikata komai a kanta.
Malam mai Yasin yana daga zaune a ɗakinsa ta labule ya hango wucewar Rahina, ya jima ransa yana biyawa da ita don haka bayan tafiyar Labaran ya yi zaraf, bayan ya ji ta fara sheƙa ruwa ya nufi banɗakin cikin sanɗa. A hankali ya tura ƙofar banɗakin, da yake dare ne sai Rahina ta yi tsammanin ko Labaran ne ya shiga domin ya tayata wankan. Malam mai Yasin yana shiga da sauri ya wara hannuwansa ya dadumo ta, cike da so da ƙauna Rahina ta ce.

"Wallahi ba don kada na saka son zuciya ba, da sai na ce duk duniya babu matar da ta kai ni sa'ar miji masoyi."
Malam mai Yasin don kar ya yi magana ta ji muryarsa sai kawai ya ce, "Ummmmm!" Ya cigaba daduma hannunsa a jikinsa. Rahina tana shafo fuskarsa ta ji gemunsa da gashin bakinsa sun yi mata ƙababa, a razane ta ja da baya da ta ce. "Wayyooo Allah! Masoyi ka zo kwarto a banɗakin nan."

Da gudu Malam mai Yasin ya fice daga banÉ—akin ya faÉ—a É—akinsa, Labaran da ke É—aki jin ihun Rahina ya sa ya zaro wani kafcecen almakashi irin na aikin gona ya tafi da shi.
Yana zuwa banÉ—akin ya shiga jera mata tambayoyi, ba ta tanka masa ba sai ji ya yi ta fashe da kuka. Ganin ba shi da wata mafitar ya sa shi ma ya rushe da kuka har da majina, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce.

"Kwarto ne ya shigo mini banÉ—aki, kuma tas ya gama lalube ni."
Wani abu ne ya soki ƙirjin Labaran tsananin soyayya da kishinta ya rufe shi.
"Sai da na laluba gemu da gashin bakinsa, na gane ba kai ba ne tun ba ka da shi." Rahina na ƙara faɗin haka ta sakin kuka. Jikin Labaran ne ya shiga karkarwa zuciyarsa tana zafi, cikin huci ya ce.

"Na tabbata Ado ne! A cikin gidan nan shi ne tuzuru sako zaninki ki tafi É—aki, wallahi yau sai na guntule shi da almashin hannun nan nawa. Nan gaba sai na ga da me zai nemi yin kwartoncin."
Labaran yana gama magana ya fita a guje yana wani irin ihu kamar wanda zai tunkari maƙiya a filin yaƙi.

07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[10/12/2024, 16:47] Ameera Adam: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

SHAFI NA HUÆŠU

Kasancewar yaya Ado dawowarsa daga wurin aiki kenan, ya sa ya shiga rage kayan jikinsa domin ya watsa ruwa ya gabatar da sallar Isha'i. Yana daga cikin ɗakinsa ya fara jiyo ihun Labaran, ya girgiza kansa cike da takaici, yana jin haushin yadda gidansu ya zama tamkar gidan haya saboda yadda zuciyar kowa take a kusa. Ihun da Labaran yake kurmawa ne ya janyo hankulan mutane wasu suka fito, wasu kuma suka tsaya suna leƙensa daga window. Yayin da wasu kuma suka rifa masa baya, domin su ga irin wainar da zai toya. Sashen Yaya Ado ya shiga, ya tsaya daga bakin ƙofa yana sauke numfashi cike da zafin rai. Yaya Ado ne ya leƙo da kansa daga shi zai gajeren wando, ya haɗe fuska ganin Yaya Ado da ragowar mutanen gidan a sashen ba tare da sun nemi izininsa ba. Saboda yaya Ado mutum ne mai tsattsauran ra'ayi, kuma yana da ƙa'idoji don haka suke cewa karatun boko ya mayar da shi mai aƙidar yahudawa.

"Me ya sa ka shigo mini ba tare da izinina ba?"
Yaya Ado ya tambaya fuska a haɗe, Labaran ya ji kamar ya watsa masa ruwan zafi mai haɗe da attaruhi, saboda ganinsa da ya yi da gajeren wando kaɗai ya sake harzuƙa shi, musamman da ya tuna Rahina ta ce kwarton yana ta shafe ta a banɗaki. A hankali Labaran ya fara takawa jikinsa har karkarwa yake, hannunsa riƙe da ƙaton almashi. Ganin haka ya sake ɓata ran Yaya Ado, saboda a duniya ya tsani wani ya raɓo ɗakinsa saboda muhimman takardunsa da ba ya son wani ya taɓa masa. A harzuƙe ya tunkari Labaran ya ce.
"Kai Labaran ba magana nake yi maka ba?"
Mutanen wurin carko-carko suka yi cikin mamaki suna kallon Labaran, cikin shammata Labaran ya yi kukan kura ya yi kan yaya Ado yana ɗaga almashin sama, kamar yadda sojoji suke yi a filim yaƙi ya ce.

"Zuwa na yi na halaka ƙasurgumin fasiƙi da wannan almakashin." Yana gama magana ya kai hannu yana ƙoƙarin fisgar gajeren wandon Yaya Ado.

Nan take suka shiga kiciniya, Yaya Ado yana ƙoƙarin kare kansa shi kuma Labaran ƙarfi da yaji yake ihu da kururuwar sai ya guntule shi. Ganin haka ya ɓata ran yaya Ado, ya fusata ya ɗaga Labaran ya damfara shi da ƙasa. Labaran bai daddara ba ya sake miƙewa duk da ya ji zafin buguwar ya ce.
"Wallahi yau ko kashe ni za ka yi sai dai mu kashe juna, ko banza na san zan mutu a fagen shahadar kare mutumcin matata."
Yana rufe baki sai kawai ya saka hannu ya zugo gajeren wandon ƙasa. Matan da suke wurin suka saki ihu suna fita waje a guje, yayin da Baba Ibrahim da Baba Sale suka yi kansu Labaran da gudu ganin da gaske yana shirin aikata abin da yake faɗa.
Fitar Hansatu ya yi daidai da parking ɗin motar Fadil, da gudu da ƙarasa wurinsa cikin kururuwa ta ce.
"Likita don Allah ku taimako wallahi kisa za a yi, Ado ne da Labaran." Cikin izza ya sauke baƙin gilashin idonsa, ya zuge gilas ɗin motar cikin golden voice ɗinsa ya ce.
"Lafiya?"
Ya tambaya saboda bai ji abin da ta faÉ—a ba, sakamakon gilashin motar da ke rufe.
Chapter 59 · 0% Book details