← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 36

Sashe 36

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

BA’A SHAN
ZUMA…
K’ARSHE
BA'A SHAN ZUMA… 112
NA LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
®NWA
Shi da kanshi ya tuko su,
gidansu suka zarce ko da suka
shigo Kd, wanka sukai suka
gabatar da sallar maghriba
wadda tai musu a hanya,
Deedo ta fito cikin wani skinny
long skirt, da yar top dinta,
gashinta, ta tara shi wuri daya
ta daure, kitchen take k'ok'arin
shiga domin ta sama masu
abinci, a dai dai lokacin Nawap
ya fito palon shima cikin blue
din jeans da red din t-shirt,
gabanta ya karaso, ya mika
mata agogon dake hannunsa,
sannan ya miko hannun, yana
kallon ta.
Ansa tayi, tana tura baki tace
"Abinci fa zan girka mana,
kuma ka zo zaka tsaida ni"
Dariyar yadda tayi da bakinta
yayi,
"Gobe kaman haka baza ki
ganni ba, balle har na tsaida
ki"
Ya fada yana langabar da kai,
Itama fuskan tausayin tayi,
tunowar da tayi gobe fa ita
kadai ce; babu yayan ta.
"Yi sauri dauko hijab dinki
muje gaishe da Ummi, can sai
mu samu abinda zamu ci"
Ya fada yana kallon console
mirror din dake makale a palon,
yana gyara collar rigarsa.
"Da gaske Yaa Nawap?" Ta
fada cikin zumudi.
"Zan ce na fasa ko ki wuce
kizo mu tafi"
Da dan gudu ta shige daki tana
fadin "I'm sorry Mon amour",
Bata wani dade ba ta fito
sanye da dogon hijab har
gwiwanta, suka rufe gidan suka
shige mota sai gidan Ummi.
Taji dadin ganinsu sosai, sun
kuma yi sa'a tana zaune a
dining table tana cin abinci,
dan haka ba tare da bata lokaci
ba suka zauna suma, Deedo ta
zuba masu, suka cigaba da ci
suna fira.
Sai wurin goma da rabi,
sannan suka yi mata sallama
suka wuce gida.
A palo suka zauna, firar
yadda zasu yi missing juna
suke ta yi, a haka har sha daya
da rabi, inda Deedo ta fara
hamma, bata ankara ba ta
bingire a wurin ta cigaba da
bacci. Juyowar da Nawap zai
yi ya ganta sai bacci take,
murmushi yayi, don ya zata
baccin karya ne, saboda haka
take mashi, sai ya dauke ta ya
kaita daki sannan ta mik'e.
Shigewa yayi ya gama shirin
baccinsa, ko da ya fito dai a
haka ya tadda ta, dan haka ya
sa6i abinshi suka wuce dakin
baccinsu.
Tun karfe biyar na asuba
suka tashi, wanka suka yi, tare
da alwallah sannan ya ja su
sallah, bayan sun gama suka yi
adduoin da suka saba, Nawap
ya mike ya koma gado, inda ita
kuma ta wuce kitchen ta shirya
breakfast mai sauki, sannan ta
shirya jikinta da jeans wanda
ya matse ta tsaf, ta samo top
dinta mai fadi ta dora, tayi
kyau sosai, sannan ta matsa
inda yake a kwance, lokacin
karfe bakwai dai dai, fuskarsa
take shafawa har ya buda
idonsa,
"7:am har yayi kana bacci, ka
manta akwai aiki yau ne? Nd
flight din karfe takwas zaka bi"
Ya mike tare da salati,
"Ai duk lefinki ne"
Ya fada yana cire kayan jikinsa,
Ta mika masa towel, "je ka
shirya idan ka fito sai kayi
banbanmin" ta fada tana fita
daga dakin.
K'arfe takwas saura suka fito,
jikinta sanye da doguwar
abaya, ta yane kanta da gyalen,
ita ta kaishi har airport, sannan
ta dawo, tana mai cike da kewa
da maraicin mijin ta.
Daga nan ita ma skool ta
wuce domin sun fara lectures
tun satin da ya wuce.
BAYAN SHEKARA HUD'U
Deedo ce ta fito daga babban
asibitin gwamnati na garin
Kaduna, atamfar super wax ce
jikin ta dinkin riga da skirt, sai
dogon hijab dinta, hannunta na
dama sagale da farar riga ta
likitoci (lab coat), yayin da
dayan hannun yake dauke da
jaka, da kuma katon littafin
(text book) mai hoton
kwakwalwar dan Adam a jiki.
Gaban motar ta kirar BMW
M4 ta isa, ta juye tarkacen
hannunta a baya, sannan ta
bude bangaren driver ta shiga
ta bata wuta, ta wuce
hankalinta kwance.
Cikin unguwar rimi ta nufa
dai dai kan alkali road, naga
tayi parking gaban wani asibiti
wanda aka rubuta TAIMAKO
SPECIALIST CLINIC, lab coat
dinta ta buda bayan motar ta
dauka, yayin da ta shige cikin
asibitin kasancewar wayar da
aka mata kan tayi sauri tana da
marassa lafia. Cikin k'warewa
take bin gadajen marassa
lafiyar, a bayanta kuma nurse
ce tana dauke da file na
kowanne patient a wurin.
Gadon wani dan tsoho ta isa,
wanda yake fama da ciwon
zuciya, ta duba file dinshi, ta
juyo da kallonta gare shi
"Baba akwai gwaje gwaje da
zanyi maka, akwai kuma na jini,
sannan kuma zan duba bugun
zuciyarka, amma sai kayi
hakuri fa"
Cikin ciwo tsohon yace
"Kuma duk a nawa zakuyi
wannan aikin? Ni fa wlh ba
kudi ne da ni ba, sai da nace
su kaini na gwamnati, amma
suka kawo ni nan, ni ban san
ya zanyi ba 'yar nan"
Da murmushinta, ta kalle shi
"Kar ka damu Baba, domin
kuwa babban dalilina na bude
asibitin nan ba komai bane, sai
dan na taimakawa marassa hali
irin ka, in sha Allah za ayi
komai, ba kuma tare da ko
sisinka ba"
Ta mik'awa nurse din file
dinshi, sannan ta wuce zuwa
gado na gaba, haka har ta
gama round dinta, ba ita ta bar
asibitin ba sai misalin karfe
biyar na yamma.
[26/04 09:40] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 113
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Tana shiga gidan ta zube a
palo saboda tsabar gajiyar da
ta kwaso, hannuwanshi taji ya
ziro ta kafadarta yana danna
mata su a hankali, lumshe ido
ta fara yi, tana jin tamkar a
mafarki,
"Likita bokan turai" shine
abinda ta ji an fada, wanda
yasa tayi firgigit ta juyar da
kanta tana kallonsa.
"Yaushe a gari?"
Ta fada tana kare mashi kallo,
murmusawa yayi,
"Ko 30 mins banyi da
shigowa ba, na gaji da missing
matata bazan iya daurewa har
sai Friday kafin na ganta ba"
Ya zagayo inda take a zaune
ya zauna a gefenta,
hannuwansa cikin nata.
Bude bakinta zata yi magana
wata kyakkyawar yarinya mai
asalin kama da Nawap, ga dan
banzan wayo, duk da
shekarunta basu wuce biyu ba,
ta rugo da gudu ta fada kanta,
tana shashshekar dariya.
"Mammy sannu da zuwa" ta
fada cikin maganarsu ta yara,
lokacin da ta mik'e ta rungumo
wuyanta, tana mai nuna farin
cikin ganin Mammyn tata.
Sama Deedo ta daga ta,
tana fadin
"Thank you Ummina "
Nawap ya jawosu jikinshi
yace "Ummi har kin manta da
ni ko, dan kinga mammy ko?
Gobe ma zan koma bazan kara
wasa dake ba"
Suka kyalkyale da dariya ita
din da Deedo, yayin da ta
zaunar da ita a tsakaninsu, ta
mika hannu ta rungumo
Nawap, shima haka yasa
hannunsa ya k'ank'amesu yana
jin soyayyar matarshi, da tilon
'yar tasa, har cikin birnin
zuciyarsa.
ALHAMDULILLAH, anan na
kawo karshen wannan labari,
kuskuren da nayi Allah ya
gafarta mana, Allah kuma ya
amfani abinda na fada dai dai,
ya bamu ikon amfani da
darasin da yake ciki.
This is a dedication to a sis
from another mother (FEEDO-
DEEDO) thank you 4 been
there always.
Special thanks to Aysha
Chuchu, Jam33la & Ummu
Ahmad, 4 loving this story like
no one.
Nagode kwarai da hakurinku
akan jinkirin da aka samu kafin
kammaluwar wannan labari. Ku
cigaba da kasancewa tare dani
a labarina na gaba wanda ya
ansa sunan K'ADDARAR
AURENA!
Lubabatu Maitafsir & Benaxir
Omar muke yi maku fatan
alkairi a koda yaushe.

Complied by Princess Aysha Muhammad
Chapter 36 · 0% Book details