← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 36

Sashe 24

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 73-75
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Zubewa shima yayi a kujeran,
ya rasa dalilin rasa
natsuwarshi tun lokacin da ya
ci karo da pic d'in da Deedo ta
tura mashi ta whatsapp.
Zuciyarshi da take wani
tuk'uk'i yake dan bugawa a
hankali yana fadin, "why! Why
this for my lil sis?" Ya dad'e
yana k'aryata zuciyarshi akan
abinda take fada mashi, amma
ina, ya riga ya gama yardan ma
kanshi cewa yana cikin yanayi
na soyayya! Soyayyar ma mai
mugun tsanani, wadda take
tattare da wani mugun kishi
wanda har ya kan rasa inda zai
tsoma ranshi a duk lokacin da
ta taso mashi.
Cikin k'unar zuciya ya furta "I
love yu Deedo, why can't yu
understand? Me sa baza ki
kulan mun da kanki ba? Me sa
kike neman halaka ni da
soyayyarki" ba tare da ya
tantance ba ya ji wata zufa ta
karyo mashi duk kuwa da A.C
dake palon, babu abinda yake
tunani sai hanyar da zai je
Kaduna, tunanin Deedo tare da
son ganinta yana bala'in
azabtar da shi da rayuwarshi.
Kuka sosai Deedo ta cigaba da
yi, ta rasa wannan wace irin
rayuwa ce, ace a matsayinta na
mace kuma 'yar jami'a amma
bata da wani 'yanci nata na
kanta? Tana tunanin tun da ta
bar gidan Goggo tayi
bankwana da bak'in ciki, ashe
ba haka abun yake ba, mutum
baya nan ma amma ya sama
rayuwarta ido, shin wai ya yake
so tayi ne? Jin alamar mutum
na tunkaro palon daga hanyar
kitchen yasa tayi saurin
mikewa ta haye sama, Jan
gado ta fada ta cigaba da rera
kukanta inda a zuciyarta tana
fadin baza ta k'ara bashi
hak'uri ba, tunda dai ba wani
abu tayi ba.
Ta k'ara da cewar "kuma
abinda nake in ba mai kyau
bane ai Ummi baza ta barni
nayi ba, dan haka taje can ta
matse mashi mutum sai fad'an
tsiya" a haka har aka kira
maghriba, sannan ta mik'e ta
shige toilet ta d'oro alwala.
Tana gama sallan taji text ya
shigo wayanta, sai da ta gama
duk abinda take sannan ta
dauko wayan, ga mamakinta
taga ashe Yaa Nawap ne,
gwiwa sake ta bud'a text din
"text me the registration fees"
taga ya turo, shiru tayi tana
k'ara kallon wayan, inda take
tambayar kanta "wai shi wane
irin mutum ne?"
Wurgar da wayan tayi ta mik'e
ta sauka k'asa ba tare da ta
mashi text din kud'in
registration din ba, nan suka ci
abinci, sannan suka cigaba da
firarsu da Ummi. Jin shirun da
Nawap yayi yasa ya kira
number ta har sau biyu amma
shiru, dan haka ya kira Ummi
yana tambayar ko ina Deedon
take. Bayan sun gama gaisawa
da Ummi ta mik'a mata wayan,
sannan ta wuce sama domin
gabatar da sallan isha'i.
Gaisheshi tayi ciki-ciki, haka
shima ya ansa mata yace "baki
ga text dina bane"
"Ban gani ba na bar wayan a
daki"
"Oya kije ki duba, ki mun reply
yanzu, ok?"
"Ok zan duba"
Ba tare da ya kara cewa komai
ba ya kashe wayan, inda
zuciyarshi ta cigaba da jin
haushi da kuma son yarinyar
da bata san ma yana yi ba.
Mik'ewa tayi ta koma d'akin, ta
d'auko wayan, nan tayi arba da
missed calls dinshi, shiru tayi
tana tunanin rashin kyautawar
da tayi wa yayanta mai burin
faranta mata a koda yaushe.
Admission letter dinta ta
d'auko ta duba kud'in
registration din, ta rubuta,
sannan daga k'arshe ta sa "I'm
so sorry big bro, bazan k'ara
ba" ta tura mashi.
Yana kwance ya ji alamar text,
da sauri ya duba wayan, nan
ya ci karo da text din Deedo,
wani lausassan murmushi ya
saki, nan da nan kuma ya nemi
damuwar da yake tare da ita ya
rasa. Bai b'ata lokaci ba yayi
mata mobile transfer ta kud'in
registration din, sannan ya
k'ara mata da 20k, yayi mata
text cewar "in case idan kina
da buk'atar wani abu"
Washe gari ma da wuri ta
shirya cikin turquoise blue din
abaya ta yafa gyalen abayar ya
zauna mata d'as, ta zaro
handbag dinta mai tarkacen
takardunta, ta sanya takalminta
sannan ta k'arasa dakin Ummi.
Ta zauna a gefe ta gaishe da
ita, ta ansa tana mai sanya
mata albarka, tayi mata
sallama, suka wuce tare da
driver.
Ko da suka shiga skool
tunanin abinda zata yi ta fara,
bata san kowa ba bata san ko
ina ba kuma, gashi bata da
number Affan, dan haka ta
wuce office din Dr. Kashim ba
tare da wata damuwa ba. Abin
mamaki tana isa kofan office
din ta jiyo k'anshin turaren nan
da ta ji jiya, ba tare da saninta
ba ta lumshe idanu ta, sannan
ta saki wani kyakkyawan
murmushi, a dai dai lokacin
shi kuma ya bude kofan ya
fito.
Kallonta yayi, ya tabbatar tana
cikin nishadi, dan haka yayi
saurin fadin "Hey beautiful"
kaman daga sama taji
muryanshi, hakan yasa ta kara
sakin wadataccen murmushi,
sannan ta gaisheshi, sai da ya
k'are mata kallo sannan ya
ansa yace "me kika zo yi nan?"
"Neman wanda zai raka ni
registration" ta fada kanta
tsaye. Murmushi yayi, yace "ga
wani kin samu, muje ko?" Ba
tare da tace komai ba, tabi
bayanshi suka fara tafiya. Suna
yi suna dan fira jefi-jefi.
A haka dai da taimakon Affan
da kuma sanayyarshi da
mutane ta samu ta kammala
registration dinta, sai dai 'yan
abubuwan da baza a rasa ba,
wanda koda tana cikin lectures
ne zata iya k'arasa su. Affan
ne yayi mata rakiya zuwa bakin
mota lokacin da driver ya zo
d'aukanta, sai a sannan kuma
ya anshi wayanta, yayi dialling
number shi, sai da ya tabbatar
ta shiga sannan ya mik'a mata,
cikin wani salo yace "I'll miss
you for a while" ba tare da tace
komai ba, ta d'an saki
murmushi, dan ta san itama
har zuciyarta zata missing
dinshi, saboda yan kwanakin
nan da suke yawan kasancewa
tare ta shak'u dashi da yawan
zolayarshi.
Chapter 24 · 0% Book details