← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 36

Sashe 13

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 39, 40
& 41
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Aysha shine sunan dake
rubuce a saman screen din,
sai da ya ja dan siririn tsaki,
sannan ya maida hankalinshi
ga tukinshi. Reverse yayi, ya
fita daga wurin, yayin da wayar
ta cigaba da rera waka alamar
kira yana kara shigowa. Deedo
ganin bashi da niyyar dauka,
tace "Yaa Nawap ana kiran ka"
cikin halin ko in kula yace "ina
ji ai" ganin bai damu da kiran
ba yasa itama ta juya ta cigaba
da kalle kallen ta har suka iso
gida.
Direct ya shige yayi parking
kanshi tsaye, a gefe suka ga
wata sabuwar Audi V10 baka,
ba tare da tunanin komai ba ya
fito, ya bude boot din ya
cigaba da ciro kayan da suka
siyo, yayin da Saude wadda ta
fito tun lokacin da taji shigowa
su ta cigaba da kwasa tana
kaiwa ciki.
Sauran da suka rage Deedo ta
kwasa ta yi gaba yana binta a
baya, da sallama suka shiga
palon, inda suka tarar da Ummi
da wata bakuwa a zaune. Sai
da Deedo ta gaishe da su,
sannan ta haye upstairs da
kayan hannunta.
Karasawa Nawap yayi ya zube
a kujera yana kiran wash.
Ummi tace
"ya dai? Ko ka gaji ne?" Yace
"Wlh yarinyar ki din can ta bani
wahala Ummi"
Ummi ta murmusa, sannan ta
kara da
"Ai sai hakuri dama, tunda dai
ka riga ka zama babban yaya"
ba tare da yace komai ba ya
mike da niyyar barin palon,
Ummi ta dakatar dashi ta
hanyar cewa "wai baka kula da
bakuwar mu bane?" Sai a
sannan ya kai duban shi ga
kyakkaywar budurwar da ke
zaune, wadda tunda ya shigo
ta tattara duk wata natsuwa,
tare da hankalin ta, ta mika
mashi.
A kasalance ya juyo ya kare
mata kallo, sannan ya shafi
sumar shi mai tarin yawa, yace
"Yaushe a gari?"
Wani lallausan murmushi ta
saki, sannan tace "inji maki'
bako kenan" cikin halin ko in
kula, yace "sorry naga call
dinki, I was driving" ta gyara
zaman ta, tace "no p" a dai dai
nan, ta ja handbag dinta,
sannan tayi ma Ummi sallama,
ta mike da niyyar barin palon.
Ita ma Ummi mikewa tayi, ta
nufin wurin Deedo wadda
hankalin ta ke wurin ta tunda
suka shigo gidan.
Shima juyawa yayi, ya bi
hanyar da zata sada shi da
part din shi, ba tare da ya kara
bi ta kanta ba. Aysha ta juya ta
bi bayanshi da kallo, tace
"Nawap"
Ya juyo hankali kwance, yana
mata kallon fadi matsalarki.. Ta
gyara tsayunwanta, tace "amma
kasan saboda kai nazo gidan
nan ko?"
"Ban fahimce ki ba" ya fada,
sannan ya jingine da bango ya
nade hannayen shi yana
kallonta. Takowa tayi a hankali
zuwa gaban shi; tace "har
yaushe ne ranar da zaka
fahimci yadda zuciyata ke
tafarfasa saboda sonka?
Nawap yaushe ne ranar da zan
samu farin ciki daga gare ka?
Shin wai mei yasa baka
tausaya ma zuciyar da ta dade
tana azabtuwa da so da
kaunarka ba? Plz Nawap kaji
tausayi na mana" ta karasa
maganar tana mai marairaice
fuska kaman zata yi kuka.
Kayataccen murmushinsa ya
saki, sannan yace "look Aysha,
ya kamata ace maganar nan ta
wuce tsakanin mu, ya kamata
ace a matsayin ki na mace
kinyi facing reality yanzu, ki
gane abinda kike so ba zai
taba kasancewa tsakanin mu
ba, in fact, kiyi hakuri ki bama
masoyanki dama har a cikin su
Allah yasa ki samu wanda zai
kwanta maki, I'm sorry" yana
gama fadin haka ya juya, ya
cigaba da tafiyar shi..
Hawaye ne kawai Aysha bata yi
ba, sai kukan zuci da take ta
faman yi, zuciyanta yayi baki,
ta rasa menene yake mata
dadi. Juyawa tayi zata fita, a
dai dai lokacin Deedo ta sauko
daga sama, kujeran da Aysha
ta tashi Deedo ta kaiwa kallo,
nan taga iPhone6 dinta a
yashe, da alama ta manta da
ita ne, dan haka tayi saurin
karasawa ta dauka wayan,
sannan ta bi bayanta…
Har ta shiga motan ta zauna, ta
hada kanta da steering, wani
irin zugi take ji a zuciyanta.
Deedo ta karasa tayi knocking
glass din, ta dago ta kare mata
kallo, sannan ta zuge glass din
ta watsa mata kallon raini, tace
"ya akayi ne?" wayan Deedo ta
mika mata, sannan tace "kin
manta wayan ki ne" fisgan
wayan tayi, sannan ta maida
glass dinta ta zuge, ta fara
kokarin tada motan. Ita kam
Deedo da bata fahimci halin da
take ciki ba, ta juya ta shige
ciki abinta.
WACECE AYSHA?
Aysha Sabe Musa, 'ya kwaya
daya tal a wurin iyayenta
wanda suka kasance yan asalin
garin Katsina, amma yanayin
aiki ya dawo dasu garin kaduna
da zama. Suna zaune a
Galadima road inda ya kasance
basu da nisa tsakanin su da su
Nawap. Sunyi karatu tare da
kanwar shi Hafsat a A.B.U
zaria, inda daga bisani ta wuce
Jordan inda ta kammala
masters dinta, ta dawo gida
yanzu.
A kalla Aysha tayi shekara
biyar tana dakon soyayyar
Nawap, wanda son da take
mashi ne ya kara kusancinsu
da Hafsat har zuwa lokacin da
tayi aure, amma saboda shi ta
kan wanke kafa taje gidan su
duk don ta ganshi, sai ta fake
da cewar taje gaishe da Ummi
ne. Sai dai tayi rashin sa'a, har
inda yau take, Aysha bata
samu karbuwa ba a zuciyar
Nawap, asali ma bata jerin
matan da Nawap zai iya so a
rayuwanshi!
Chapter 13 · 0% Book details