← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 36

Sashe 11

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 33, 34
& 35
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Gudu ya cigaba da yi, babu
wanda ya ke ma wani magana,
Deedo dai adduo'in matafiya
take ta faman nanatawa cikin
zuciyar ta. Shirun ya ji yayi
yawa dan haka ya danna
Suratul Room cikin qira'ar
Sheikh Ahmad Sulaiman, ita
kuma ta tattara hankalin ta baki
daya, banda kallon titi ba
abinda take yi, dan yau ne rana
ta farko data fara barin kauyen
Ningi. A sannu a hankali har
suka shigo garin kaduna,
Deedo idon ta kyar, ko alamar
bacci babu, gashi lokacin
kusan karfe 8 na dare, idanuwa
ta baje ta fara kallon street
light da yawan hold up, da
kyawawan motocin da suke ta
rafsa uban gudu a manyan
titinan garin. Wani dadi taji ya
ratsa mata zuciya, a hankali
kuma ta fara samun natsuwa,
dan tunda suka taho hankalin
ta a tashe yake, hamdala ta
yima Allah, sannan cikin
zuciyar ta tace "ko bakomai
ganin wannan kyawawan
abubuwan ma wani abu ne a
rayuwa" daga karshe tayi
addu'ar Allah ya sada ta da
dangin mahaifiyar ta, tunda dai
ta san a garin nan suke. A
haka taga sun shigo wata
hadaddiyar unguwa wadda
babu kowa sai kukan karnuka
da yan tsiraran motoci da suke
wucewa jefi jefi. A bakin wani
makeken gida taga yayi horn,
mai gadin ya fito da sauri ya
bude tafkeken gate din, Nawap
kuma ya tura kan motar shi
hankali kwance. Ido ta cigaba
da zarawa tana kallon flowers
din da suka kayatar da
tsararren ginin gidan. Wuri ya
samu kusa da wasu jerin
motoci ya parka, sannan yace
mata ta fito suje ciki. Haka ta
fito tana ta kalle kalle, yana
gaba tana bin shi a baya, har
suka iso kofar palon, ya tura
kanshi da sallamar shi, babu
kowa sai karan T.V an kunno
tashar BBC WORLD. Deedo ma
bata yi kasa a gwiwa ba ta
biyo shi a baya ta shigo,
sanyin A.C ne ya dake ta,
sannan ta taka wani lafiyayyen
carpet mai asalin taushi, gefe
guda ta samu ta rakube ta
zuba ma screen din tafkekiyar
LED plasma idanuwan ta, yayin
da shi kuma ya haura sama, ba
tare da ta san abinda zai yi
ba…
* **Wata kyakkawar dattijuwa
mai cikar kamala da kwarjini, ta
gani tana saukowa a hankali
daga stairs din yayin da shi
kuma yake biye da ita a baya.
Ido Deedo ta tsura masu, ganin
asalin kamar da suke ne ya
tabbatar mata da cewa matar
jinin shi ce. A tare suka zauna
a kujerun da suka yima palon
ado, sannan matar ta gyara
muryar ta, tace "ta so ki dawo
nan mana yan mata" a hankali
deedo ta mike, tana matse da
dan kullin ta kamar wani zai
kwace mata ta karasa tsakiyar
palon ta zauna kasan carpet, ta
dago domin ta gaishe da matar
sai taga ashe tun da ta taso
idon matar a kanta yake! Nuna
ta matar ta fara yi da hannun
ta, kamar zata ce wani abu, sai
kuma ta fasa tace "ki saki jikin
ki, kinji" ta dukar da kanta, ta
gaishe ta, ita kuma ta ansa
cikin fara'a da jin dadi, sannan
kuma a hankali ta fara
tambayar ta labarin ta, dana
garin su da labarin karatun ta,
da duk wani abu da ya shafi
rayuwar ta. Hankali kwance
Deedo ta rattaba mata tarihin
ta, dana goggon ta, da irin
rayuwar kaskancin da ta yi a
kauyen Ningi! Dam gaban
ummi ya fadi, mikewa tayi ta
karasa gaban Deedo ta mikar
da ita tsaye, kallon ta take
kamar ta samu T.V daga bisani
kuma ta rungume ta, wasu
kwalla masu zafi suka gangaro
mata, Deedo da bata fahimci
komai ba, ta fara zara idanu,
Nawap ma da yake gefe a
zaune mikewa yayi, yazo gaban
su yana cewa "ummi lafia?"
Kuka sosai ummi ke yi, tace
"Nawap ita ce wlh, yarinyar da
nake kwana da tunanin ta nake
tashi da shi a ko wace rana"
tasa hannu ta kara rungume
Deedo, tace "Firdausi dama
kina raye? Ashe da rabon zamu
gana dake" Nawap yace "ummi
ban fahimce ki ba fa" sakin
Deedo ta yi, sannan ta kamo
hannun ta suka zauna a kan 3
seater, ta juya tana facing
Nawap, tace "ita ce yarinyar da
kanwa ta Rukayya ta rasu ta
bari, wadda har naje dauko ta
amma goggon ta ta hana, ashe
dama don ta azabtar da
marainiyar Allah ne" ta karasa
maganar tana matse kwalla,
Nawap kan shi sai da kafafun
shi suka kasa daukan shi,
karasawa yayi ya zauna sannan
ya fara tunanin ashe dama
yarinyar nan jinin shi ce, no
wonder ya ji tausayin da yake
mata ya banbanta da na sauran
mutanen da yake taimakawa,
Allah mai iko! Shine kawai
abinda Nawap ya iya fada a
bayyane..
* *Ummi ta kama hannun Deedo
ta rike gam, kallon ta take
tamkar marigayiyar yar uwar ta
Rukayya, yarinya tubarkallah
amma wahala ta kashe ta, cikin
zuciyan ta take cewa zan kula
dake Deedo, in maki gatan da
banyi ma diyar dana Haifa ba,
zan mayar da ke abin
kwatance, in inganta rayuwar
ki, sannan in tallafa maki har
sai kin cika burin ki na zama
kwararriyar likita. Deedo banda
kuka babu abinda take yi, yau
itace ta samu matar da ke
consoling din ta, har ta yarda
ta zauna kusa da ita! Ashe
dangi ma wata rahama ce a
rayuwar dan adam, Nawap ya
katse su ta hanyar saukar da
ajiyar zuciya, sannan yace
"well, faduwa tazo dai dai da
zama kenan, tunda dai yau ga
diyar ki ta dawo hannun ki ai
shikenan, ita kuma goggo
akwai Allah, zai yi ma Deedo
sakayya" ya mike, ya kara da
cewar "bara na shiga ciki, ko
sallan maghriba ba mu yi ba"
ummi kai kawai ta daga mashi,
dan yau wani farin ciki take ji,
gata ga diyar ta. Kallon ta tayi,
sannan tace "da izinin Allah,
wahalar ki tazo karshe Deedo,
ki saki jikin ki, dan baki da
mahaifiyar da ta wuce ni, idan
kin kwana biyu kin huta, zan
kaiki kiga dangi su ma su
ganki, zan baki duk wani farin
ciki wanda ya kamata uwa ta
bai wa diyar ta, kinji? Tashi
muje in kaiki dakin ki, kiyi
wanka kiyi sallah, sannan ki
sauko muci abinci" dagowa tayi
da jajayen idanun ta, tace
"nagode ma Allah da ya nuna
mun wannan rana a rayuwa ta,
nagode ma Yaa Nawap wanda
yayi silar sada ni da ku ummi,
Allah ya yi maku sakayya da
mafificin alkairi" hannu ummi
tasa ta rufe bakin ta, tace
"kyautata maki ya zama dole a
gare mu, saboda mune dolen
ki a rayuwar nan, kar na kara
ganin hawaye a idanun nan
kina jina?" Ta daga mata kai,
sannan ta mike ta dauko kullin
kayan ta, ummi na gaba tana
binta a baya har suka haye
sama, dakin da ke opposit na
ummin ta bude mata, anyi
painting dakin da pink nd
purple, yayin da komai da yake
cikin dakin ma pink nd purple
ne, baki Deedo ta sake tana
kallon haduwar wurin, hannun
ta ummi ta ja ta gwada mata
komai, haka ma toilet ta gwada
mata, da yadda za tayi amfani
da komai, ta dauko towel mai
mugun taushi ta bata, tace ta
daura ta shiga tayi wanka.
Yayin da ita kuma ta juya ta
fita, ta rufe mata kofan dakin.
A bakin gado Deedo ta zauna
tana kare ma dakin kallo, bata
taba tunanin akwai irin jin
dadin nan a wannan duniyar
ba, hawaye suka yayyafo mata,
tasa hannu ta share, sannan ta
mike ta cire kayan ta, ta daura
towel din ta shige wanka…
Chapter 11 · 0% Book details