← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 36

Sashe 20

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 61, 62
&63
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Cikin kankanin lokaci idanuwan
nan suka juya, suka sauya
launi daga fari zuwa jaa, da
sauri zuciyarshi take harbawa,
Deedo da take zaune a gefe
hankalinta yayi kololuwa wurin
tashi, a tunaninta wani mugun
abun ne ya faru ganin mood
din Nawap ya canja lokaci
guda.
A zuciye ya balla murfin motan
ya fita, inda a hankali Aysha ta
fara rage full light din da tayi,
cikin isa da gadara itama ta
buda murfin tata motan ta fito,
sannu a hankali ta fara takowa
zuwa inda yake.
Kallonta yayi cikin tsananin
bakin ciki yace "so it's yu?"
Murmushi ta saki mai tattare
da rainin hankali, ta nade
hannuwanta, ta jingine jikin
motarshi, sannan ta kalleshi
tace "yup, it's me" wata
muguwar harara ya watsa mata,
sannan ya juyar da kanshi
yace "dame kike son a kira
sunan abinda kika yi?"
Murmushi ta kara saki, tace
"duk abinda ka kira shi" sai da
ya dai dai ta tsayuwanshi, yayi
facing dinta yadda ya kamata,
sannan yace "Aysha abinda
kike shirme ne, kauyanci ne,
kuma rashin wayewa ne! I told
yu ki fita hanya ta, otherwise
zaki gane kurenki, dan na lura
abin naki na neman ya zama
raini, ni bana ciki da rainin
hankalinki.. "
Wata kibiyar bakin ciki ce tayi
suka ta caki zuciyar Aysha,
kallonshi kawai take don ta
rasa ta cewa, babban bakin
cikinta shine Deedo tana
sauraren duk abinda sukeyi,
kasancewar a bude ya bar
motan, wasu yan kwalla suka
yayyafo mata, juyawa tayi cikin
salo na gogaggun yan mata ta
dan share, a lokaci guda kuma
ta cigabada kallon Nawap tana
dan murmushi, sannu a hankali
ta taka zuwa gabanshi tace
"Nawap sonka a cikin jinina
yake, dashi nake rayuwa, idan
har kana tunanin akwai ranar
da zan daina sonka, to ka tafka
babban kuskure, domin da
sonka nake numfashi, da shi
nake kwana da shi kuma nake
tashi a ko wacce safiya,
harkanka kuma da kake
magana, yanzu na fara
shigarta, dan haka mu zuba
nida kai.. "
Juyawa tayi da sauri da niyyar
ta shige motan ta, hannunta ya
finciko tun karfi, ta dawo da
baya, kallonta yayi ido cikin ido
yace "idan mafarki kike gara ki
farka Aysha, domin bakya jerin
kalar matan da zan iya so a
rayuwata, baki da quality kwara
daya da zan iya so a wurin
mace, sannan kuma rashin
kunya na daya daga cikin
abubuwan da nafi komai tsana
a tsarin rayuwata, dan haka ki
natsu, ki gane cewa ruwa ba
sa'an kwando bane!" Yayi
wurgi da hannun sannan ya
koma ya shige motan, yayi
reverse ya koma cikin gidan.
Wani tiririn bakin ciki ne ya
cigaba da fita daga zuciyan
Aysha, kallon motan tayi, inda
wasu hawayen bakin ciki suka
gangaro saman fuskanta, a
hankali ta furta "zaka san ka
wulakanta ni Nawap, ba dai
akan wannan tsinanniyar
yarinyar bane kake yi mun
abinda kaga dama, wallahi sai
tayi dana sanin shigowa
gonata da tayi" dakyar ta ja
kafanta ta koma cikin motan,
gidan da bata shiga ba kenan,
domin jin zuciyanta take
kaman ana tafasa ruwan zafi a
ciki.
Parking Nawap yayi, ya juyo ya
kalla Deedo wadda itama shi
din take kallo, ji yayi tamkar an
zuba mashi ruwan sanyi,
kyawawan idanunta kadai, sun
tafiyar da kunci da bakin cikin
da yake ciki, murmushi ya
sakan mata, wanda na tabbata
bai san lokacin da ya subuce
mashi ba, a hankali yace "ki
shiga ciki, da safe zan je na
duba maki jamb din kinji?" Ba
tare da tace wani abu ba, ta
buda motan ta fita, shi kuma
ya bita da idanu har sai da ta
shige ciki.
Ummi ta samu zaune tana
kallon Sunnah T.V da
murnarta, tace "ba dai har kun
dawo ba?" Sai da ta zauna,
sannan tace "bamu je bama,
yace da safe zai je ya duba
mun, wai dare yayi" tace "ba
laifi ai, Allah yasa dai muga
alkairi " "amin" ta fada, sannan
ta mike ta haye sama, zuciyarta
fal da tunanin wannan bala'i
irin na Aysha. Namiji yace
baya son ki amma ke kin nane
mashi sai kace mayya! A fili ta
furta "Allah dai ya kyauta
wannan rayuwar wahalar."
Alwala tayi sannan ta gabatar
da sallan isha'i, tana gamawa
ta cire kayan ta da niyyar shiga
wanka, wayanta ne ya fara ruri,
karasawa tayi inda wayan take
taga bakuwan number, da
sallama ta daga wayan ta kara
a kunnenta, daga dayan
bangaren taji ance "dan Allah
ina neman Deedo ne" wani
mugun dadi ne ya ziyarci
zuciyanta, domin ko a mafarki,
baza ta taba manta mai
wannan muryan ba.
Nan da nan suka barke da fira
ita da Hally, ba tare da bata
lokaci ba ta zayyana mata
dangantakar dake tsakaninta
da Ummin Nawap, ta kuma
bata labarin result dinta da
yadda rayuwa ke tafiyan mata
cikin jin dadi.
Murna sosai Hally tayi, ta kara
da cewar "mahakurci mawadaci
Deedo, dama ai haka rayuwa
take, idan wani ya kika wani
zai so ka" da haka suka yi
sallama, inda Deedo tai mata
alkawarin kiran ta da safe in
sha Allah
Nawap ya dade zaune cikin
motan yana tunanin abinda ya
faru kaman a mafarki, daga
karshe dai ya fito ya shiga
palon bai ga Deedo ba sai
Ummi kawai a zaune, kunnuwa
ya baza yana sauraren yaji
abinda zata ce game da abinda
ya faru tsakaninsu da Aysha
amma yaji tsit, don a
tunaninshi ko Deedo ta fada
mata. Haka ya karaci zaman
shi, inda daga bisani ya mike
yayi mata sai da safe ya wuce
side dinshi.
Da safe kamar yadda yayi
alkawari, haka ya fita around
10, cafe din da yayi mata
registration ya nufa ya siya
scratch card ya duba mata, yaji
dadi sosai ganin ta ci kusan
250, bai bata lokaci ba yayi
printing result din ya fito,
straight KASU (Kaduna State
University) ya wuce, gaban
faculty of medicine yayi
parking, sannan ya ciro
wayanshi ya kira wata number.
Cikin yan mintuna wani
matashi wanda shekarunshi
basu wuce 30 ba ya fito ya
karaso gaban motan Nawap.
Fitowa yayi, ya mika mashi
hannu suka gaisa, sannan
suka jera zuwa cikin faculty
din. Office din mutamin da naji
ya kira da Kashim Yarima suka
nufa, bayan sun gaisa ne
Kashim ke ce mashi "wlh baka
da kirki Nawap, zumuncinka
yayi karanci ko?" Nawap yace
"kasan abubuwa sai a hankali,
yanzu ma wata sis dita ce
nazo yima follow-up, ta cika
nan skool din ban sani ba ko
zaku dauketa"
Dariya Kashim yayi, yace "me
zai hana indai nan din ta cika,
kuma tana da abubuwan da
muke bukata, zuwa end of this
month ma zamu fitar da 1st
list na admission in sha Allah"
Nawap yace "plz kayi mun
kokari, komai tana dashi,
medicine take son karantawa,
dan Allah kar ku bata course
din da ba shi take so ba" ya
kara da "bara na baka sunanta
idan kun fitar da admission din
sai ka duba mun please" wata
paper ya mika mashi ya rubuta
details din Deedo ya bashi,
sannan sukai sallama, inda yai
mashi alkawarin kiran shi da
zaran sun fitar da list din..
Chapter 20 · 0% Book details