← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 36

Sashe 31

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 99&100
BA'A SHAN ZUMA… 99
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Cikin sigar shagwaba kamar
wanda yake kallon ta ta turo
dan bakinta, sannan ta fara
rubuta ansar da zata bashi "if
yu really mean ur words, me
zai hana ka bayyana kanka?"
Ta tura, yayin da ta rungume
wayar tana jin sabon yanayi na
daban a cikin jikinta.
Murmushi yayi wanda har sai
da kyawawan hakoransa suka
bayyana, a lokacin da yayi arba
da sakonta, ba tare da wata
fargaba ba, ya mayar mata da
ansar "ok, ki shirya gani na da
misalin karfe bakwai na daren
yau."
Ihun murna ta saki, inda ta
fada da baya ta kwanta, ta
k'ank'ame wayan tana tunanin
abinda ya dace tayi kafin
lokacin haduwarsu. Da sauri ta
mike ta wangame wardrobe
dinta, sannu a hankali take bin
kayan ciki da kallo, amma bata
ga wanda ya dace da ita a rana
irin ta yau ba, rufewa tayi,
sannan ta bude dayan gefen
wanda yake dogayen riguna ne
zallah jere a cikin wardrobe
d'in, a hankali take duba su
daya bayan daya, inda a
k'arshe ta sauke idonta akan
wata English gown kalar lemon
green, murmushi ta saki
sannan ta zaro rigar, wuyanta
irin rufaffen nan ne (tuttle
neck) yayin da hannun rigar
yake dogo, sai dai ya matse
daga k'arshe, doguwa ce har
k'asa, in banda kyakkaywan
(shape) da aka yi mata daga
sama.
A samar gado ta aje rigar,
sannan ta bude inda
gyaluluwanta suke, ta samo
wani madaidaicin jan gyale
wanda ta san tabbas zai hau
da rigarta, haka ta gama hada
duk wani abu da zata sa,
sannan ta sauka kasa zuwa
kitchen.
Saude ta tarar tana aiki, ta
kalleta tace "je ki huta Saude,
bar ni da aikin kitchen din nan
yau" godiya Saude tayi ta
wuce, duk da ta fuskancin
yanayin farin cikin da uwar
dakin nata take ciki.
Tana tsaka da aiki, ta juya
bayan ta Nawap ya shigo
kitchen din, ya buda fridge ba
tare da ya san ita ke aiki wurin
ba. A hankali ta dago idanunta,
inda ta sauke su a kan nasa,
amma yayi kicin-kicin da fuska
shi dole ga big bro, baya son
ta gane da shi tayi musayar
text dazu.
Murmusawa tayi, sannan
tace "har ka tsorata ni wlh, me
zaka dauka na kawo maka?"
Basarwa yayi, yace "eyya, ban
san kina nan bama ai, ruwa ne,
na riga na dauka ma, kiyi aikin
ki kedai" tana kallonshi tana
dariyar yadda yake faman
bonewa, tace "ok, ehnmm" ya
juyo yace "ya dai?" "Daman zan
ce ne anjima ina da bako, yace
zai zo nan dan kada kace ban
fada maka ba" ta karashe
maganan tana mai karantar
yanayin da yake ciki. Cikin
borin kunya ya shafi kanshi,
"lokacin da kika fara
soyayyanki dama kin nema
izinina ne?" Ya fada yana fita a
kitchen din, biyo shi tayi tana
fad'an "ni fa ba wani soyayya
Yaa Nawap, aboki ne kawai" da
murmushi ya juyo, sai kuma ya
daure yace "naji, kije kiyi
aikinki"
"to bakon nawa fa? Baka ce
komai ba"
Ido ya kura mata, yana mata
kallon kece rayuwa ta, nan da
nan yake neman sanya ta a
wani hali, domin bugun zuciyar
ta taji ya karu, ba tare da tace
komai ba, ta juya ta koma
kitchen din zuciyarta fal da so
da k'aunar Yaa Nawap.
[20/04 20:56] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 100
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Lokacin da ta gama girkinta har
karfe shida saura kwata, a
gurguje ta jera komai a dining
table, lokacin Ummi na
saukowa ta kalleta sai zuwa
take tana dawowa tsakanin
kitchen da dining area, ga
fuskanta a sake da alama tana
cikin farin ciki sabanin
kwanakin baya da ko kasan ta
daina saukowa, kullun tana
daki kaman bokanya.
"Ba dai ke kika yi girkin yau
ba auta" Ummi ta fada dai dai
lokacin da ta karaso gabanta.
Da murmushi ta kalla Ummi
tace "yau special na hada
mana Ummi, har sai kunne yayi
motsi idan aka ci" bubbuda
coolers din Ummi take yi, inda
wani kanshi ya daki hancinta,
tace "lallai naga alama, amma
menene sirrin?" Ta fada da
sigar tsokana.
"Ba komai fa Ummi" Deedo ta
fada tana rufe fuskanta da
hannu, "sai dai ehnmmm"
"mene?" Ta tambaya tana
kallon ta. "Ina da babban bako
anjima Ummi, idan ya zo zai zo
ya gaishe ki ma" ta fada tana
dariya. "Bako Deedo?" Ummi ta
fada cikin karaji,
girgiza kai Deedo tayi, "zaki
ganshi Ummi, kuma in sha
Allah zaki yaba dashi" "Allah
yasa" ta fada yayin da take
wucewa zuwa palo ba tare da
ta ji dadin maganar Deedon ba.
"Yanzu shikenan yaron nan
yana gani zai yi rashin mace
kamar Deedo? Duk dan saboda
dan banzan kishi irin nasa,
kuma yana son ta ba wai baya
son ta ba." Sababin da Ummi
ke ta faman yi kenan a cikin
zuciyarta, har aka kira
maghriba, ta mike ta haye
sama domin bada farali.
A bangaren Deedo ko bayan
ta fito wanka ta bada sallar
maghriba, sannan ta cigaba da
yan shafe-shafenta, sassaukar
kwalliya tayi kasancewarta ba
ma'abociyar dam6are-dam6are
ba, sannan ta ja rigarta ta
sanya, ta gyara gashinta ta
faka shi a tsakiya, inda tayi
amfani da jajayen kananan yan
kunne, ta daura bracelet ja,
tana kokarin feshe jikin ta da
turare, taji alaman message ya
shigo mata, da sauri ta duba
"Ina cikin gidan ku, zaune a
palon baki, just waiting for my
princess" shine abinda ta gani
rubuce a message din.
Chapter 31 · 0% Book details