← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 36

Sashe 32

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BA’A SHAN
ZUMA…
101-103
BA'A SHAN ZUMA… 101
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Dariya mai sauti ta saki, a fili
ta furta "Yaa Nawap kenan"
sannan ta rubuta mashi ansa
"hmmmm, ina zuwa yanzu" ta
tura masa, sai da ta karasa duk
abinda zata yi, ta janyo wasu
red plat shoes ta saka, ta yafa
gyalenta sannan ta fita. Dakin
Ummi ta fada, ta tarar da ita
zaune tana jan casbaha, ta
zauna gefen gado tana wasa
da hannunta. Har sai da tayi
addu'a duk suka shafa a tare
sannan Ummi tace "har ya iso
ne?" Kanta a kasa ta girgiza
kai alaman "eh"
"To ki tashi kije, ki dai kula
da kanki da mutuncinki" "in sha
Allah Ummi" Deedo ta fada
lokacin da take mikewa, a
zuciyarta tana mai cewa "Ummi
da ta san ko waye da ba
wanda zai kaita jin dadi, shaaa,
zanyi surprising dinta ne" ta
wuce hankalinta kwance,
domin yadda take jin son
Nawap yasa ta rage fargaban
haduwa dashi.
Zaune yake ya bama kofa
baya, in banda kanshin
turarensa na Tom Ford Velvet
Orchid, babu komai da yake
tashi a wurin sai fa sautin T.V
inda ake nuna labaran kasa a
tashar TVC. Da sallama ta
shigo, kanta a kasa ba tare da
fargaba ko mamakin ganinsa
ba, haka ya dago kansa yana
kallon yanayinta, me sa bata yi
mamakin ganin shine ba? Anya
babu wani abu da ta sani
tuntuni? Kawar da tunanin da
yake yayi, sannan ya ansa
sallamar yayin da take
karasowa tsakiyar palon.
Kallonta yake tamkar yau
ce rana ta farko da ya fara
ganinta, tayi mashi kyau sosai
wanda bai taba tunanin tana
da shi ba. Nesa dashi ta
zauna, ta dago a hankali tace
"Ina wuni Yaa Nawap"
Cikin rashin kuzari ya ansa ta,
nan wani dogon shiru ya ratsa
tsakaninsu, muskutawa Nawap
ya yi, cikin k'arfin hali, sannan
yayi gyaran murya yace "ke
haka ake taran bako ko ruwan
sha babu?" Shiru tayi kaman
baza ta ansa ba, can dai ta
nisa tace "bakon nazo nema,
but unfortunately sai na ganka,
kunya ce ta hana ni tambayar
ko ka kasan inda yake?"
Ido ya tsare ta dashi har
saida ta gama maganarta, inda
ya cika bakinsa da iska, a karo
guda ya furzar dashi, ya rasa
ta ina zai fara mata bayani, ga
so da k'aunarta na matuk'ar
azabtar dashi, amma yana
tunanin halin da zai tsinci
kanshi matuk'ar bata ansa
tayin soyayyar shi a karo na
biyu ba.
Fuskantarta yayi, yayin da ya
dawo daga duniyar tunanin da
yake, cikin wata irin murya ya
kira sunanta "Firdausi" ta dago
a hankali ta yadda taga
fuskarsa ta san he's damn
ready nd serious. Domin tunda
take dashi sau daya ya taba
kiran ta da ainahin sunanta,
ranar da ta fara ganinsa a
duniya.
Kwantar da kai yayi, sannan
ya fara magana "Bazan so na
zama mai son kai ba, haka
zalika kada kiyi tunanin
dangantar dake tsakaninmu,
ina son ki dauka baki taba sani
na ba, ta yadda baza ki sha
wahala wurin yanke hukunci a
kaina ba. Shekaru ukku da
suka wuce na nemi sanin
takamaiman abinda ke
zuciyarki dangane da ni, amma
Allah bai nufa zan samu ansa
ta, ta inda tafiyar gaggawa ta
same ni, gashi kuma nayi
alkawarin bazan neme ki ba,
har sai ke da kanki kin neme ni
da ansar tambayar da na miki"
sai da ya dan tsagaita, yana
mai cigaba da kallon yadda ta
dukarda kanta, tana wasa da
yatsun hannunta, sannan ya
cigaba…
BA'A SHAN ZUMA… 102
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
"Ina mai rokon Allah yasa yau
ta kasance rana ta k'arshe da
zan san matsayina a wurin ki"
yayi shiru yana mai cigaba da
kallon ta yana kuma rokon
Allah yasa ya dace a wannan
rana.
Shirun da tayi har na tsawon
mintuna kusan bakwai yasa ya
cigaba da magana "idan har na
saka ki a rudani, ina son ki
gafarci zuciya ta wadda take
bugawa a ko wacce sa'a da so
da k'aunar ki, wadda take
azalzala ta, ta ke kuma hana ni
sukuni a duk tsawon shekarun
dana sanki, ba laifi na bane
Deedo, ba kuma ni na dorawa
kaina ba, Allah ne ya jarabce ni
da son ki, me sa baza ki
taimaki yayanki ba? Me sa
baza ki gane farin cikin da zan
samar maki ba, matuk'ar kika
yarda da ni a matsayin uban
ya'yanki, ina son ki sosai,
wanda bazan iya dainawa ba,
domin kuwa kece mace ta
farko da na fara so, haka kuma
kece ta karshen da zan tafi ga
mahaliccina da k'aunarta koda
baki yarda kin so ni ba."
Yana gama fadar haka ya
mike da niyyar fita, domin
zuciyarsa ta gama karyewa,
gashi Deedo ta ki tace komai,
asali ma ko kallon yanayin da
yake ciki bata yi.
Har sai da ya kai bakin kofa
sannan ta samu damar dago
da jajayen idanunta, wanda
suka rine da ruwan hawaye
tace "Yaa Nawap" juyowa yayi
da sauri jin raunanniyar
muryarta na kiran shi, ganin
hawaye na zuba daga
kyakkyawar fuskarta yasa yayi
saurin dawowa da baya yace
"no please lil sis, don't be like
this kinji, na fahimci kina son
Affan ko? Me sa zan shiga
rayuwarku, na hakura zan
danne son da nake maki,
amma bazan iya jurar ganin
hawayenki ba, it's ok kinji"
yayin da yasa hannu ya zaro
handkerchief ya mika mata.
Ansa tayi ta toshe bakinta
dashi, sannan ta saki kuka mai
sautin, wanda ya gigita Nawap,
har ma ya rasa ta ina zai
lallasheta, da ya san haka ne
da bai zo mata da maganar
nan ba.
Katse mashi tunani tayi ta
hanyar cewa "Yaa Nawap kaine
mutun na farko wanda ya kalle
ni a matsayin mutun kamar
kowa, kai ka daga darajata, ya
cika mani gurin rayuwa ta,
sannan kaine mutun na farko
wanda zuciya ta ta mace
saboda son shi, ban taba son
wani kwatankwacin son da
nake maka ba, amma na rasa
me sa baka fahimci hakan ba,
har kayi fushi da ni, tsawon
shekaru ka barni ina dakon
sonka ka manta da ni, me sa
Yaa Nawap? Kasan halin tashin
hankalin da na shiga?" Ta k'ara
fashewa da kuka mai tsuma
zuciyar masoyi, wanda yasa
Nawap dafe kanshi da duk
hannayensa biyu.
Ya ma rasa menene
yanayin da yake ciki, shin farin
ciki ne ko kuma haushin
kanshi yake ji yadda bai
fahimce ta ba tun asali. Kasan
carpet din ya zauna shima ya
dago fuskanta ya share mata
hawayen, sannan yace "I'm so
sorry lil sis, azaban kishi ne ya
hana ni fuskanta inda kika sa
gaba, I promise baza ki taba da
na sanin kasancewa tare da ni
ba, zan faranta maki dai dai
gwargwadon iko, zan kula
dake, in tarairaye ki fiye da
yadda ARCH. SADDIQ ya
tarairayi LAILA (Rabon ka ko
yana bakin kura na Chuchun
Gaye) zan shayar dake
madarar farin ciki fiye da
yadda FU'AD ya shayar da
MEELA (WATA RAYUWA) ki
yarda da ni my lil sis, ki bani
aron zuciyarki, ni kuma na
maki alkawarin I'll never ever
let yu down…."
BA'A SHAN ZUMA… 103
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Murmushi ta sakan mashi
yayin da hawayen suka cigaba
da zarya akan kuncinta,
"shhhh.." ta fada lokacin da
take dora dan yatsanta akan
bakinta, nan take yayi tsit, tare
da aika mata sakon kallo mai
alamar nayi missing dinki,
langabar da kai tayi, itama tana
kallonsa, sannan a tare suka
sa dariya kamar ba ita ce
wadda tasha kuka yanzu yanzu
ba.
Cikin dan k'ank'anin lokaci
suka dinga aika ma juna da
kalamai masu dadi da kwantar
da hankalin masoyi, har sai da
suka gama aminta da junansu,
inda daga k'arshe Nawap ke
tambayar ya akai bata yi
mamakin ganin shi yake aika
mata sakon text ba, nan ta fada
mashi tayi amfani da
TrueCaller ta gane shine.
Dariya yayi, sannan yace
"Ooops, na manta akwai
wannan fa" dariyan tayi itama,
gani take kaman ba Yaa Nawap
din da ta sani ba, ashe dama
ya iya soyayya?
"Tashi muje ka nema izini
wurin Ummi, dan idan ba kai
mata ba nima zan hakura da
kai" wara idanunsa yayi "da
zaki hakura ai da yanzu kin
mance dani, yarinya ko Ummi
bata yadda ba ni ba yadda za
ayi dani, dole a so ni,"
Sannan ya mike ya bi bayanta
tana dariya suka fito, suka
k'arasa cikin gidan.
Ummi zaune saman dining
table suka shigo fuskokinsu
dauke da murmushi, kallon
Nawap tayi tace "Kai kam ina
ka shige ina nemanka ka taya
ni cin abinci?" Sosa kai yayi,
yace "naje neman aure ne"
Ummi sake da baki tace "to fa!
Babbar magana"
Ganin Deedo na bin shi a
baya tace "ke kuma ina bakon?
Ko har ya tafi?" Dariya ta
kwace mata, ta karasa kujerar
da take kusa da ta Ummi ta
zauna, yayin da shi kuma ya
zauna a wadda take kallonsu,
tana kallon Ummi tace "ga
bakon na kawo ya gaisheki"
tana yi tana nuna Nawap da
yatsa.
Shiru Ummi tayi, yayin da
take k'are masu kallo duk
kowannensu da fara'a dauke a
fuskarsa, tace "kai ku dakata,
ban fa gane ba" duk suka sa
dariya, inda Nawap yace
"Ummi zaki bani autar taki ko
na nema wata?" Duk da kanta
ya kulle da sha'anin yaran
zamani, amma matuka tayi
farin ciki, taji dadi fiye da
misali, inda ta kai kallonta ga
Nawap tace "akwai sharudda
dai, wanda matuk'ar ka kiyaye
su to zan baka ita"
Ya buda ido yana kallon
Ummi, yace "tohm a jero su ina
ji" ya fada lokacin da yake sai
ta kunnensa garesu.
Dariya ya basu, dan haka suka
kyakyale gaba dayansu,
sannan Ummi tace "banda
yawan takuri, sannan bana son
yawan la6e, ana kiraye mun
auta, kuma idan ka shirya ka
turo da magabatanka dan dama
na gaji da ciyar da gauro a
gidan nan"
Sosai ya ji dadin
maganganunta, "zanyi yadda
kike so Ummin mu" ya fada
yana kallon Deedo da ta dukar
da kanta tana murmusawa…
Chapter 32 · 0% Book details