← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 36

Sashe 19

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BA’A SHAN
ZUMA…
57,58,59&60
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Gudu sosai ya cigaba da yi
kaman wanda zai tashi sama,
ya rasa abinda ke mashi dadi,
gurin shi daya, ya saita
idanunshi kan yar kanwarshi
wadda yake ta faman tunani da
son jin muryanta.
Ba shi ya shiga Kaduna ba sai
wurin karfe biyar da rabi na
yamma, dan haka bai tsaya
bata lokaci ba, gida straight ya
wuce ko dan ya samu natsuwar
zuciyanshi.
Da sauri mai gadi ya bude
mashi bakin gate din, inda a
lokaci guda ya tura kan
motarshi ciki, mikewa yayi
sosai da niyyar ya samu wurin
parking, amma numfashinsa ne
ke shirin daukewa lokacin da
ya hango ta zaune saman
wasu fararen kujeru. A gabanta
wani dan table ne fari, tana
sanye da bakin skinny jeans da
wata red din t-shirt mai dan
tsawo, saman kanta wani royal
blue din veil ne, tayi daurin
torchlight..
Kunnuwanta makale da
earpiece, ta dora kafanta
saman table din dake gabanta,
idanuwanta a lumshe, da alama
wakar da take sauraro tana
shigarta yadda ya kamata.
Wani gwauron numfashi
Nawap ya ja, a lokaci guda
kuma ya fara yan kalle kalle,
daga gefe ya hango Idi dake ta
faman gyaran flowers din shi,
can gefe kuma Mal. Habu
driver ne zaune yana sauraron
radio.
Wani mugun abune ya ji ya
cakan mashi zuciya cikin dan
kankanin lokaci, yaji
numfashinshi na shirin
daukewa, tunani ya fara yi ko
Deedo ta samu tabin hankali
ne, tana ganin gardawan
mazan nan amma take zaune a
haka, lallai yau zata yaba ma
aya zakinta!
Da sauri ya balla murfin motan
ya fito, har yanzu tana nan
yadda take. Wurin da take
zaune ya dosa, bai yi wata
wata ba ya fincike earpiece din
dake kunnenta, cikin kaduwa
da razana tayi saurin bude
idonta, tana shirin artawa a
guje, ganin mutum tayi kamar
wanda aka jefo daga sama
yana ta faman huci kamar
mayunwacin zaki..
Idanuwan nan sun canja launi
zuwa jaa, yanayin data ganshi
ya bala'in firgitar da ita, dan
haka ta mike da gudu tayi
hanyar cikin gidan, mikewan da
ta yi, yaji kaman an caka
mashi kibiya a kahon
zuciyarshi, ashe da tana zaune
bakomai ya gani ba kenan,
lallai yarinyar nan zata gane
kurenta. Bai yi kasa a gwiwa
ba shima ya bi bayanta da
gudunshi. A palo ya cimmata,
kunnenta ya damka ya murda
tun karfinshi, ihu ta saka
wanda yasa Ummi karasowa
cikin palon da sauri.
Ganin halin da suke ciki yasa
tayi saurin matsawa ta warce
Deedo daga rikon da Nawap
yai mata, kallonshi take cikin
fushi, tace "malam lafiya daga
zuwan ka zaka hau dukan mun
yarinya?" Idonshi sunyi zuru
zuru sai huci yake, yace "watau
Ummi ke baki ma ga laifin da
tayi ba kenan?" Tace "me tayi
fa, ince a zaune ka sameta a
waje, ko wani abun tayi?" Kara
kallonta yayi, gyalen da ta
daura ya sabule, gashinta ya
bazo saman fuskanta, gani
yayi tayi wani mugun kyau
kamar aljanna, yadda ta rakube
a bayan Ummi tana raba ido
abin sai ya birge shi, nan da
nan yaji kunyar abinda yai
mata, Ummi ce ta katse mai
tunani da cewa "ina saurarenka
inji laifin da tayi"
Cikin borin kunya ya dan shafi
sumarshi da ta kwanta luf luf,
kallonta ya kara yi, sannan ya
dan tsuke fuska yace "kar na
kara ganin kin fita haka ba tare
da kinsa hijab ba, baki ganin
akwai gardawa a cikin gidan
ne?" Kara kallon kanta tayi, ita
dai bata ga matsalan shigan ta
ba, asali ma lokacin da ta fita
babu kowa a wajen, ba tare da
ta kara kallonshi ba tace "kayi
hakuri, ba zan kara ba" wani
murmushi ne ya kwace mashi,
bai san lokacin da yace "that's
my lil sis" Ummi kam tabe baki
tayi, tayi gaba tana banbami
"mutum daga dawowa ko
hutawa bai yi ba amma ya fara
takura mana" a haka ta shige
kitchen ta bar su nan tsaye
kaman bishiyar da aka dasa..
Dukar da kanta tayi, ta rasa
menene abinda ya kamata tayi,
shin ta tafi ko ta tsaya? Bata
yanke shawaran abinyi ba, taji
ya tako zuwa inda take, a
hankali ya fara magana yana
kallonta, har yanzu dai kanta a
kasa yake, "I'm sorry lil sis,
nayi laifi ko?" Bata ce komai
ba, sai kanta da ta girgiza
alaman a'a, murmushi ya saki
kaman tana kallonshi, yace
"kece ai baki ji, wato tunda na
tafi haka kike fita gaban masu
gadi ko?" Da sauri ta girgiza
kanta, "wlh yau ne kawai, kuma
lokacin da na fita ba kowa a
wajen.."
Yace "issokay to, kada ki kara
kinji?" Dagowa tayi, da niyyar
bashi hakuri, idanuwanshi
kyam akanta, da sauri ta juyar
da fuskanta, tace "I'm sorry,
bazan kara ba" "kalle ni" yace
da ita, ta juyo idanuwanta
masu tafiyar da imaninshi ta
dora su kan nashi, wani abu
yaji ya tsirga saman kanshi, ya
sauka har zuwa babban
yatsanshi na kafa, sai da ya
tattara natsuwar shi, sannan
yace "promise?" Wani dan
murmushi ta saki tace "promise
Yaa Nawap…"
Murmushin ya saki shima yace
"that's my dearest sis" da sauri
tana yar dariya ta juya ta ansa
foodflasks din da suke hannun
Ummi ta jera su a dinning, shi
kuma ya karasa gaban Ummin
yana dariya, yace "na sameku
lafiya Ummi?" "Lafiya lau" ta
fada a takaice, sannan ta
karasa cikin palon ta zauna
saman 3seater, nan ma kara
biyo ta yayi ya zauna a
gefenta, yace "Ummi duk
gajiyan da nasha na kula baki
murnan zuwana ma" juyowa
tayi ta kalle shi tace "ina fa
zanyi murnan zuwanka, kazo
ka hau mun 'ya da jibga"
"Ayi hakuri Ummi, bazan kara
ba, kuma ma har mun shirya
da 'yar taki fa" kallon Deedo
tayi wadda take jera plates,
tace "wai haka auta?"
Murmushi tayi, tace "haka ne
Ummi" sai a sannan Ummi ta
sake, suka cigaba da firansu,
inda daga bisani ya mike ya
wuce side din shi, dan ya
samu yayi wanka, ya sauke
sallolin da suke kanshi..
Shiryawa yayi tsab cikin
kananun kaya, black jeans nd
white t-shirt, kirarshi ta fito
sosai, hannunshi daure da
makekiyar agogo mai tambarin
GUESS anyi mata ado da
stones din diamond, kafarshi
daure da bakaken sneakers.
Sumar nan tayi kwance luf sai
sheki take, a haka ya karaso
cikin palon, hannunshi rike da
doguwar envelope kalar ruwan
kasa.
Saman dinning ya karasa, nan
ya ja kujera ya zauna, sannan
ya dubi Deedo yace "taimaka
mun da abinci" ba tare da tace
komai ba, ta mike tayi serving
dinshi, ta mika mashi, duk
abinda take idonshi a kanta ko
kyaftawa baya yi, murmushi ya
sakan mata yace "thanks my lil
sis" itama murmushin tayi, ta
koma ta zauna ta cigaba da cin
abincinta. Envelope din da ya
shigo da shi ya mika ma
Ummi, yace "kinga rashin
kokarin da autarki tayi" ya
fuske ya ci gaba da kwasar
abincinshi. Ummi bata ce
komai ba ta ansa ta aje a
gefenta, saida suka gama cin
abincin sannan ta buda, ga
mamakin ta, taga ko C babu a
result din Deedo, daga A sai B,
da murmushinta ta mika mata,
ta kalli Nawap tace "ai dama
nasan auta ta ba daga nan ba"
inda ta kai dubanta kan Deedo
tace "you deserve to be a
Doctor my dear, Allah yi maki
albarka ya sanya alkairi a
rayuwanki"
Wani mugun farin ciki ne ya
lullube Deedo wanda yasa ta
fara hawayen jin dadi, ta dade
tana neman wanda zai na
appreciating dinta a duk
lokacin da tayi wani abun
kwarai, Allah mai iko yau itace
ake sama albarka saboda ta
samu sakamako mai kyau, bata
ma san da bakin da zatai ma
Ummi godiya ba. Mikewa tayi
ta fada jikinta, tana kukan farin
ciki, Ummi ma kwalla ne suka
yayyafo mata, tasa hannu ta
share, tace "ya isa haka, bana
son kukan nan kina jina"
murmushi ta saki ga kuma
hawaye na bin fuskanta,
sannan ta fara daga kanta
alaman baza ta kara kukan ba.
Nawap dake gefe kallon su
yake yana mai jin wani farin
ciki na yawo a jikinshi, dan
haka ya tako zuwa inda suke,
Deedo ya kalla yace "lil sis
shirya ki raka ni unguwa" cikin
zakuwa ta mike ta haye sama,
inda Ummi ta kalleshi tace "ina
zaka kai mun ita kuma muna
tsaka da jin dadin mu?"
Murmushi yayi, yace "zamuje
duba jamb dinta ne Ummi" tace
"aiho, na zata yawo zaka kai
mun ita ai" a haka Deedo ta
sauko sanye da bakar abaya
yar Dubai, ta tattara gashinta a
tsakiyar kanta ta daure, sannan
tayi rolling gyalen abayan,
kafanta sanye da bakin plat
shoe na Gucci, sai wani kanshi
mai dadi yake tashi a jikinta.
Ido Nawap ya kura mata kamar
zai cinye ta, ya rasa mai yasa
yake ganin kyaun yarinyar
yanzu, wanda shi a da bai taba
sanin tana da shi ba, gashi ta
wani goge ta waye kaman
wadda ta shekara goma a
birni. Karasowa tayi cikin palon
tace "Ummi zamu tafi" "sai kun
dawo auta" Ummi ta fada, ta
juyo tana "Yaa Nawap na
shirya fa" nan taga yadda ya
ware idanunshi yana kallonta
kaman bai santa ba. Basarwa
yayi, yace "muje mana" inda
yayi gaba tana bin shi a baya.
Zaune take a gefenshi, shi
kuma yana seat din driver,
sunyi bala'in kyau abin ba'a
cewa komai. Dai dai lokacin
da yake kokarin fita gate din
gidan, motar Aysha ta kunno
kai, ganin Nawap tare da wata,
yasa ta saki wani uban full
light wanda ya kashe masu
idanu gaba dayansu..
Chapter 19 · 0% Book details