Sashe 2
Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BA’A SHAN
ZUMA… 03
NA
LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
Tsakanin ta da shehu kuwa
banda kyara da hantara tare da
wanke mai kayan fitsari babu
abinda ke hada su, duk da
lokacin ya kai shekara 9,
amma haka yake miqewa ya
sharta fitsarin shi a gado, ba
ruwan goggo, balle tayi qoqarin
hana shi.
Bayan Deedo ta cigaba da
zama a gidan goggo cikin
kuncin rayuwa da ukuba,
dangin mahaifiyar ta suka
samu labari, Dan haka Fatima
babbar yayar umman ta, tazo
da niyyar tafia da ita, amma
goggo ta rufe ido ta furza mata
ruwan rashin mutunci, ta qara
da cewa ita ce dolen Deedo,
tunda mahaifin ta bashi da
kowa wanda ya wuce ta, dan
haka kuma babu wanda ya isa
ya karbe wannan yarinya daga
hannun ta. Haka Ummi
kasancewar haka yaran ta suke
kiran ta, ta tattara ta koma kd
cike da tunanin halin da Deedo
take ciki..
* ***
Ana tashi daga makaranta ta
sabo jakar ta, ta fara bunguza
sauri, dan ta San halin goggo
sarai, ta riga ta mata warning
muddin Hadiza ta riga ta
dawowa gida, sai ta yabawa
aya zakin ta. Hally kawar ta,
tana ta kwada mata kira, amma
ina ta riga tayi nisa, da gudu ta
karaso gaban ta, tana cewa
"wai ke Deedo goggon nan taki
sai kace mala'ika, baki so ki
bata mata rai ko kadan" ta
murmusa tace "Hally kenan, kin
fa san komai, amma sai kina yi
kaman baki sani ba, ina zan
tsaya in sha na jaki, yau ma
tunda asuba da shi na karya"
suna haka suka kawo kwanar
gidan su Deedo, hally kuma tai
mata sallama ta mike hanyar
gidan su.
Tana shiga ta tarar da goggo a
kofar dakin ta, ta karasa ta
gaishe ta, bata ko kalli inda
take ba, balle ta ansa, tace "sai
yanzu kika ga damar dawowa
dan uban ki? Wlh in kika yi
wasa sai kin daina zuwa
makarantar banzar nan, ke
dama kwakwalwa irin ta uwa,
babu komai ciki sai majina" ta
saddar da kanta, tace "kiyi
hakuri goggo, in sha Allah
bazan qara ba" tace "munafuka
wadda tayi gadon munafunci,
tashi wuce ki bani wuri kin
mun tsuru da idanuwa kaman
na mujiya" simi simi Deedo ta
miqe tana matse yar kwalla, ta
shige dan akurkin dakin ta, ta
cire uniform dinta, ta canja
kaya sannan ta fito tayi alwala,
goggo sai hararar ta take, ta
koma ta fara sallah, sai a
sannan Hadiza ta dawo. Goggo
ta washe baki tana "Dijangala
ta mai gari, ita kuma tana wani
yatsina, ta isa gaban goggo ta
zauna, tace "ena abinci na" ba
gaisuwa ba komai, abin ka ga
ba tarbiyya, goggo tace "jeki
kitchen indomie tana nan dana
dafa muku keda shehu ki
dauko" tana mikewa, shima ya
shigo ya dawo daga
makarantar, nan suka zauna
suka kwashi indomien su, suka
cire uniform din su, goggo ta
kwada ma Deedo kira, ta fito
da gudu gudu, ta duka gaban
ta, tace "gani goggo" kafin
goggo tace wani abu, Hadiza
tace "ke kwashe kayan nan ki
wanke su tas, kuma wlh kika
mun wankin da bai fita ba sai
naci uban yarinya" shehu yace
"niko kinsan hali na, dan in
zubarwa yarinya da hakora ba
wani aiki bane a wuri na
muddin kikai mun wankin da
bai fita ba" bata ce komai ba,
ta tattara kayan ta wuce wurin
wankin, ta jawo roba zata diba
ruwa, Goggo tace "dakata
munafuka, in baza kije ki debo
ruwan wankin ba, to ki kwashi
kayan ki wuce can wurin
famfon ki wanke su, ke ga yar
iko ko? Har zaki diban mun
ruwa kiyi wanki da shi" bata ce
komai ba, ta koma daki ta
dauko hijabin ta, tazo ta dauki
katon bahon nan, ta wuce
borehole.
A hanya ta hade da hally zata
tafi islamiya, kasancewar tahfiz
take yi, hally na ganin ta, tace
"ke Deedo ina zaki da wannan
katon bahon kamar yar ga
ruwa" kwallan da take boyewa
suka gangaro mata, tace "Hally
na gaji da wannan rayuwar da
nake ciki, kullun cikin bauta
kamar baiwar da aka ciyo a
yaki" Hally ta kalle ta, tace "kiyi
hakuri Deedo wata rana sai
labari" ta goge hawayen tace
"haka ne hally, bari naje kar na
kuma yin wani laifin" hally tace
"in tambaye ki mana" tace "ina
ji" tace "wai ina dangin umman
ki? Ki gudu wurin su mana"
Deedo ta zaro ido, tace "suna
kaduna fa, kuma saida suka zo
tafiya dani goggo ta hana,
kuma ni kinga ko bauchi ban
taba zuwa ba balle kaduna"
hally tace "shikenan, Allah ya
saka maki cin zalin da ake
maki" tace "amen" sukai
sallama, ta wuce ta fara buga
famfo, kasancewar babu kowa
a wurin, ta cika bahon, ta
kinkima ta dora akai, ta cigaba
da sauri zuwa gida.
BA’A SHAN
ZUMA… 04
NA
LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
Ta na isa ta tarar ba kowa a
tsakar gidan, can ta jiyo waka
tana tashi daga palon, hakan
ya tabbatar mata kallo suke yi,
ta wuce ta sauke ruwan,
sannan ta fara wanke kayan, ta
gama ta shanya, sauran ruwan
da ta gama wanke masu ta
dauko nata uniform din ta cuda
a ciki, ta gama ta gyara wurin
ta share, sannan tayi alwallar
la'sar.
Palon goggon ta shiga tayi
sallama, ta rakube a bakin
kofa, tace "na gama goggo" ta
juyo a qufule tace "to uban mi
kuma zan miki? Iyii?" Tace
"bakomai" har ta miqe, goggo
tace "ni wlh wannan bala'in ya
fara isata, ace wannan
shegiyar yarinyar kullun ni zan
rinka cida ki, bazan iya wannan
abu ba, ke ba uban komai kike
mun ba, sai dai kizo ki
tsugunna mun kice in baki
abinci, na gano ki munafuka,
mai mugun hali irin na uwar ta,
wuce ga sauran kosai can na
safe da shehu ya kasa ci ki
dauka, dan ni dai ba abinda
zan baki gare ni ba" ta mike
tana tunanin wai wane irin hali
ne uwar ta take dashi, wanda
kullun goggo ta tashi sai tace
mata mai mugun hali irin na
uwar ta, kwalla suka kawo wa
kuncin ta ziyara, tasa hannu ta
share, tace "ya Allah kayi
gafara ga iyaye na" ta shige
kitchen din ta dauko sauran
kosan dan wata muguwar
yunwa take ji, ta tuttura shi, ta
bi da ruwa, sannan ta mike ta
bada sallar la'asar, ta dauko
Qur'anin ta, ta fito.
Palon ta kara komawa, tace
"Hadiza zaki je islamiya ne?"
Tayi banza da ita ta qyale, bata
yi kasa a gwiwa ba ta kara
nanata tambayar, ta mike daga
shingidar da tayi, tace "yau
naga bala'i, wai ke ko dai
mayya ce? Shin in ma zanje
islamiyar tare dake nake
jerawa? Ko ni tsarar ki ce da
zaki zo da wani guntun
munafuncin ki kina tambaya ta"
Tace "Allah ya baki hakuri,
naga kamar baki san lokaci
yayi bane" ta mike ta fita,
goggo ko da yake itama ba
ilimin addinin ya wadace ta ba
ko kala bata ce ba, haka suka
maida hankalin su ga kallon
su, babu wanda yayi kokarin
motsawa bare yayi sallah, daga
gani ma babu wanda yayi ko
da azzahar a cikin su.
Sauri take tayi dan ta riga ta
makara, tasan kuma dole ne ta
anshi hukunci, tana isa Allah
ya taimaka ta an gama taran
yan makara, ta silale ta shige
ajin su, nan ma malam bai
shiga ba, nan fa yan ajin suka
yo mata caa akan ta biya masu
karatun da akayi jiya, domin
yau za a anshi harda, kuma da
yawan su basu iya ba. Ba tare
da bata lokaci ba ta fara
kwararo qira'a cikin muryar ta
mai zakin sauraro, duka ajin
aka yi tsit ana sauraren ta,
haka ta gama biyawa, sannan
kowa ya cigaba da nanatawa
cikin ran shi, har malam ya
shigo aka fara gabatar da
darasi.
Ana tashi daga Islamiyar bata
tsaya bata lokaci ba ta kamo
hanyar gida. Tana dab da
shiga layin su, wasu yan
samari suka tarye ta, suna tai
mata magana amma ko kallon
su bata yi ba, daga bayan ta
taji ana cewa "ke Deedo dan
kin samu ana kula ki shine har
wulakanci kike wa samari ko,
wlh bara naje gida sai na hada
ki da goggo" juyowar da zata yi
taga ashe shehu ne yake binta
a baya ya dawo daga kwallo,
kafar shi tayi budu budu kamar
an tono shi daga rami. Ta
tsaya tace "in ka fasa fada din,
wadannan tsamayen mei zasu
bani da zan tsaya in bata ma
kaina lokaci a wurin su" ta juya
ta cigaba da tafiyar ta. Aiko
shehu ya daga kwallon dake
hannun shi ya daddage ya seta
keyar ta, ya halba kwallon, tayi
tangal tangal ta zube a kasa,
da samarin da sauran yaran da
suke wurin suka dau ihu suna
mata daria, wasu na cewa
"katuwa ta sha kasa" wasu
zafafan hawaye suka zubo
mata, ta mike tace "wlh yau sai
na rama, sai dai duk abinda
zai faru ya faru, shiru shiru ai
ba tsoro bane" ta samu wani
dan dakali ta dora Qur'anin ta,
sannan ta rugo ta cafki shehu,
suka fara dambe, nan dai
dakyar wasu dattijai suka raba
su, ana rike shi yana cewa
"shegiya mai mugun hali irin
na uwar ta, yar tsintuwa kawai"
ita kuma tace "na ji din, dadin
abun dai ni bani fitsarin
kwance, kuma in ka Kara ce
mun mai mugun hali saina
fasa maka baki wlh" wani
dattijo yace "ke Deedo kyale
shi da Allah, shehu ai ba sa'an
ki bane" da yake Allah yasa ita
yarinya ce mai girmama na
gaba da ita, haka ta juya ta dau
Qur'anin ta, ta wuce ta bar
shi…
ZUMA… 03
NA
LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
Tsakanin ta da shehu kuwa
banda kyara da hantara tare da
wanke mai kayan fitsari babu
abinda ke hada su, duk da
lokacin ya kai shekara 9,
amma haka yake miqewa ya
sharta fitsarin shi a gado, ba
ruwan goggo, balle tayi qoqarin
hana shi.
Bayan Deedo ta cigaba da
zama a gidan goggo cikin
kuncin rayuwa da ukuba,
dangin mahaifiyar ta suka
samu labari, Dan haka Fatima
babbar yayar umman ta, tazo
da niyyar tafia da ita, amma
goggo ta rufe ido ta furza mata
ruwan rashin mutunci, ta qara
da cewa ita ce dolen Deedo,
tunda mahaifin ta bashi da
kowa wanda ya wuce ta, dan
haka kuma babu wanda ya isa
ya karbe wannan yarinya daga
hannun ta. Haka Ummi
kasancewar haka yaran ta suke
kiran ta, ta tattara ta koma kd
cike da tunanin halin da Deedo
take ciki..
* ***
Ana tashi daga makaranta ta
sabo jakar ta, ta fara bunguza
sauri, dan ta San halin goggo
sarai, ta riga ta mata warning
muddin Hadiza ta riga ta
dawowa gida, sai ta yabawa
aya zakin ta. Hally kawar ta,
tana ta kwada mata kira, amma
ina ta riga tayi nisa, da gudu ta
karaso gaban ta, tana cewa
"wai ke Deedo goggon nan taki
sai kace mala'ika, baki so ki
bata mata rai ko kadan" ta
murmusa tace "Hally kenan, kin
fa san komai, amma sai kina yi
kaman baki sani ba, ina zan
tsaya in sha na jaki, yau ma
tunda asuba da shi na karya"
suna haka suka kawo kwanar
gidan su Deedo, hally kuma tai
mata sallama ta mike hanyar
gidan su.
Tana shiga ta tarar da goggo a
kofar dakin ta, ta karasa ta
gaishe ta, bata ko kalli inda
take ba, balle ta ansa, tace "sai
yanzu kika ga damar dawowa
dan uban ki? Wlh in kika yi
wasa sai kin daina zuwa
makarantar banzar nan, ke
dama kwakwalwa irin ta uwa,
babu komai ciki sai majina" ta
saddar da kanta, tace "kiyi
hakuri goggo, in sha Allah
bazan qara ba" tace "munafuka
wadda tayi gadon munafunci,
tashi wuce ki bani wuri kin
mun tsuru da idanuwa kaman
na mujiya" simi simi Deedo ta
miqe tana matse yar kwalla, ta
shige dan akurkin dakin ta, ta
cire uniform dinta, ta canja
kaya sannan ta fito tayi alwala,
goggo sai hararar ta take, ta
koma ta fara sallah, sai a
sannan Hadiza ta dawo. Goggo
ta washe baki tana "Dijangala
ta mai gari, ita kuma tana wani
yatsina, ta isa gaban goggo ta
zauna, tace "ena abinci na" ba
gaisuwa ba komai, abin ka ga
ba tarbiyya, goggo tace "jeki
kitchen indomie tana nan dana
dafa muku keda shehu ki
dauko" tana mikewa, shima ya
shigo ya dawo daga
makarantar, nan suka zauna
suka kwashi indomien su, suka
cire uniform din su, goggo ta
kwada ma Deedo kira, ta fito
da gudu gudu, ta duka gaban
ta, tace "gani goggo" kafin
goggo tace wani abu, Hadiza
tace "ke kwashe kayan nan ki
wanke su tas, kuma wlh kika
mun wankin da bai fita ba sai
naci uban yarinya" shehu yace
"niko kinsan hali na, dan in
zubarwa yarinya da hakora ba
wani aiki bane a wuri na
muddin kikai mun wankin da
bai fita ba" bata ce komai ba,
ta tattara kayan ta wuce wurin
wankin, ta jawo roba zata diba
ruwa, Goggo tace "dakata
munafuka, in baza kije ki debo
ruwan wankin ba, to ki kwashi
kayan ki wuce can wurin
famfon ki wanke su, ke ga yar
iko ko? Har zaki diban mun
ruwa kiyi wanki da shi" bata ce
komai ba, ta koma daki ta
dauko hijabin ta, tazo ta dauki
katon bahon nan, ta wuce
borehole.
A hanya ta hade da hally zata
tafi islamiya, kasancewar tahfiz
take yi, hally na ganin ta, tace
"ke Deedo ina zaki da wannan
katon bahon kamar yar ga
ruwa" kwallan da take boyewa
suka gangaro mata, tace "Hally
na gaji da wannan rayuwar da
nake ciki, kullun cikin bauta
kamar baiwar da aka ciyo a
yaki" Hally ta kalle ta, tace "kiyi
hakuri Deedo wata rana sai
labari" ta goge hawayen tace
"haka ne hally, bari naje kar na
kuma yin wani laifin" hally tace
"in tambaye ki mana" tace "ina
ji" tace "wai ina dangin umman
ki? Ki gudu wurin su mana"
Deedo ta zaro ido, tace "suna
kaduna fa, kuma saida suka zo
tafiya dani goggo ta hana,
kuma ni kinga ko bauchi ban
taba zuwa ba balle kaduna"
hally tace "shikenan, Allah ya
saka maki cin zalin da ake
maki" tace "amen" sukai
sallama, ta wuce ta fara buga
famfo, kasancewar babu kowa
a wurin, ta cika bahon, ta
kinkima ta dora akai, ta cigaba
da sauri zuwa gida.
BA’A SHAN
ZUMA… 04
NA
LUBABATU MAITAFSIR
&BENAXIR OMAR
Ta na isa ta tarar ba kowa a
tsakar gidan, can ta jiyo waka
tana tashi daga palon, hakan
ya tabbatar mata kallo suke yi,
ta wuce ta sauke ruwan,
sannan ta fara wanke kayan, ta
gama ta shanya, sauran ruwan
da ta gama wanke masu ta
dauko nata uniform din ta cuda
a ciki, ta gama ta gyara wurin
ta share, sannan tayi alwallar
la'sar.
Palon goggon ta shiga tayi
sallama, ta rakube a bakin
kofa, tace "na gama goggo" ta
juyo a qufule tace "to uban mi
kuma zan miki? Iyii?" Tace
"bakomai" har ta miqe, goggo
tace "ni wlh wannan bala'in ya
fara isata, ace wannan
shegiyar yarinyar kullun ni zan
rinka cida ki, bazan iya wannan
abu ba, ke ba uban komai kike
mun ba, sai dai kizo ki
tsugunna mun kice in baki
abinci, na gano ki munafuka,
mai mugun hali irin na uwar ta,
wuce ga sauran kosai can na
safe da shehu ya kasa ci ki
dauka, dan ni dai ba abinda
zan baki gare ni ba" ta mike
tana tunanin wai wane irin hali
ne uwar ta take dashi, wanda
kullun goggo ta tashi sai tace
mata mai mugun hali irin na
uwar ta, kwalla suka kawo wa
kuncin ta ziyara, tasa hannu ta
share, tace "ya Allah kayi
gafara ga iyaye na" ta shige
kitchen din ta dauko sauran
kosan dan wata muguwar
yunwa take ji, ta tuttura shi, ta
bi da ruwa, sannan ta mike ta
bada sallar la'asar, ta dauko
Qur'anin ta, ta fito.
Palon ta kara komawa, tace
"Hadiza zaki je islamiya ne?"
Tayi banza da ita ta qyale, bata
yi kasa a gwiwa ba ta kara
nanata tambayar, ta mike daga
shingidar da tayi, tace "yau
naga bala'i, wai ke ko dai
mayya ce? Shin in ma zanje
islamiyar tare dake nake
jerawa? Ko ni tsarar ki ce da
zaki zo da wani guntun
munafuncin ki kina tambaya ta"
Tace "Allah ya baki hakuri,
naga kamar baki san lokaci
yayi bane" ta mike ta fita,
goggo ko da yake itama ba
ilimin addinin ya wadace ta ba
ko kala bata ce ba, haka suka
maida hankalin su ga kallon
su, babu wanda yayi kokarin
motsawa bare yayi sallah, daga
gani ma babu wanda yayi ko
da azzahar a cikin su.
Sauri take tayi dan ta riga ta
makara, tasan kuma dole ne ta
anshi hukunci, tana isa Allah
ya taimaka ta an gama taran
yan makara, ta silale ta shige
ajin su, nan ma malam bai
shiga ba, nan fa yan ajin suka
yo mata caa akan ta biya masu
karatun da akayi jiya, domin
yau za a anshi harda, kuma da
yawan su basu iya ba. Ba tare
da bata lokaci ba ta fara
kwararo qira'a cikin muryar ta
mai zakin sauraro, duka ajin
aka yi tsit ana sauraren ta,
haka ta gama biyawa, sannan
kowa ya cigaba da nanatawa
cikin ran shi, har malam ya
shigo aka fara gabatar da
darasi.
Ana tashi daga Islamiyar bata
tsaya bata lokaci ba ta kamo
hanyar gida. Tana dab da
shiga layin su, wasu yan
samari suka tarye ta, suna tai
mata magana amma ko kallon
su bata yi ba, daga bayan ta
taji ana cewa "ke Deedo dan
kin samu ana kula ki shine har
wulakanci kike wa samari ko,
wlh bara naje gida sai na hada
ki da goggo" juyowar da zata yi
taga ashe shehu ne yake binta
a baya ya dawo daga kwallo,
kafar shi tayi budu budu kamar
an tono shi daga rami. Ta
tsaya tace "in ka fasa fada din,
wadannan tsamayen mei zasu
bani da zan tsaya in bata ma
kaina lokaci a wurin su" ta juya
ta cigaba da tafiyar ta. Aiko
shehu ya daga kwallon dake
hannun shi ya daddage ya seta
keyar ta, ya halba kwallon, tayi
tangal tangal ta zube a kasa,
da samarin da sauran yaran da
suke wurin suka dau ihu suna
mata daria, wasu na cewa
"katuwa ta sha kasa" wasu
zafafan hawaye suka zubo
mata, ta mike tace "wlh yau sai
na rama, sai dai duk abinda
zai faru ya faru, shiru shiru ai
ba tsoro bane" ta samu wani
dan dakali ta dora Qur'anin ta,
sannan ta rugo ta cafki shehu,
suka fara dambe, nan dai
dakyar wasu dattijai suka raba
su, ana rike shi yana cewa
"shegiya mai mugun hali irin
na uwar ta, yar tsintuwa kawai"
ita kuma tace "na ji din, dadin
abun dai ni bani fitsarin
kwance, kuma in ka Kara ce
mun mai mugun hali saina
fasa maka baki wlh" wani
dattijo yace "ke Deedo kyale
shi da Allah, shehu ai ba sa'an
ki bane" da yake Allah yasa ita
yarinya ce mai girmama na
gaba da ita, haka ta juya ta dau
Qur'anin ta, ta wuce ta bar
shi…