← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 36

Sashe 14

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 42, 43
& 44
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Cigaban Labari
Cikin gida Deedo ta koma inda
ta tarar da Saude tana jera
abinci a dinning, taimaka mata
tayi har suka gama, sannan ta
wuce tayi sallah, ta gama ta
shiga dakin Ummi ta sameta
zaune saman sallaya, gefe
guda ta samu ta zauna har ta
gama, sannan ta juyo da
murmushin ta, tace "auta ta ya
aka yi ne?" Ta murmusa tace
"lafia lau Ummi, abinci ne ya
zama ready" ta kara fadada
murmushinta, tace "kuma autar
Ummi na jin yunwa ko?" Ta
dukar da kanta tana 'yar daria,
sannan tace "a'a nazo na fada
maki ne kawai" daria Ummi
tayi, tace "to tashi muje kasan"
a tare suka mike, inda Deedo
ta tattara hijab da sallayan da
Ummi ta gama sallah ta ninke,
ta mayar da su wurin su,
sannan ta bi bayan ta suka
sauka kasan.
Nawap suka gani zaune da
jallabiya a dinning area yana ta
kwasan girki ba ji ba gani,
Ummi ce tayi gyaran murya, sai
a sannan ya lura da zuwan su.
Daria suka sanya shi da
Ummin, inda ita kuma Deedo ta
dukar da kanta tana tata
dariyar a boye.
Karasawa sukai suka zauna,
Ummi ce ta umarci Deedo da
tayi serving dinsu, dan ta lura
akwai abubuwa da dama da ya
kamata ace Deedon ta iya, dan
haka ma ta kalleta, ta kara da
cewar "yau fa da girkinki zamu
yi dinner, dan haka sai ki
shirya" murmushi tayi, yayin da
ta cigaba da zuba abincin, tace
"to shikenan Ummi"
Kallon ta Ummi ta cigaba da yi,
tana mai tunano 'yaruwarta,
wani so da tausayin yarinyar
taji ya kara tsirga zuciyarta,
wasu yan kwalla suka feso
mata, inda tasa hannu ta share
ba tare da ta bari sun lura da
ita ba.
Kallonta, ta mayar kan Nawap
wanda ya tada plate din fried
couscous yana korawa da
kunun aya mai gardi, tace "wai
kai yaushe zaka koma office
ne? Ko har yanzu hutun bai
kare ba?" Yayi gyatsa tare da
hamdala, sannan ya dan shafi
sumarshi yace "Jibi zan wuce
in sha Allah" tace "ai gara kazo
ka tafi dan ka kusa cinye mana
abincin gida" yace "kin dai gaji
da ni tunda kin samu diya
yanzu" tace "har ma da hakan"
yace "yawwa yanzu naji batu
Ummi" haka suka cigaba da
firan su cikin jin dadi, Deedo
da bata cika saka baki a firan
ba, sai dai tayi dan murmushi
kawai. Jin ta take a wata
duniya ta daban, yay ita ce ta
samu 'yanci. Hamdala tayi
sannan ta yima Allah godia da
ya nuna mata wannan
kyakkaywar rana…
A tare suka mike bayan sun
kammala con abincin, inda
Deedo ta tattara wurin ta
kimtsa komai, sannan ta wuce
da kwanukan kitchen.
Tana kokarin shigowa palon
taji Ummi na cewa "yanzu
Nawap kana ganin rayuwa zata
yi a haka? Ka tuna kai fa ba
yaro bane, ya kamata ace
yanzu ka aje iyali fa, kuma ni
ita yarinyar can Aysha ban ga
abinda ta rasa ba da baza ka
so ta ba, ko dai kana da wata
matsala ne?"
A hankali ya fara magana, "wlh
bata da komai Ummi, kawai dai
ba zan iya rayuwa tare da ita
bane, amma kar ki damu in
sha Allah zan nemo mata in
dai hakan zai faranta maki rai"
tace "shikenan, Allah ya
taimaka" ya ansa da amen,
sannan ya mike ya bar palon.
Karasawa Deedo tayi, ta zauna
a kasan carpet tana dan matsa
kafan Ummi.
Kanta Ummi ta dafa tace "auta
ya akayi ne?" "Lafia lau" ta fada
tana dan murmushi, ita ma
Ummi murmushin tayi, tace
"gobe dai in sha Allah zamu je
kiga danginki, kiga yar
tsohuwar kakarki da kowa da
kowa" dadi ne ya ratsa ta, ta
rasa abinda zata ce ma Ummi,
nan da nan hawaye suka fara
bin fuskarta, a hankali ta fara
magana "Ummi kinyi mun
komai a rayuwa, kin mayar da
ni mutum a lokacin da kowa ya
ke kyamata, bani da bakin yi
maki godia, sai dai ina addu'ar
Allah yayi maki sakayya da
mafificin alkairi, ya sa ki gama
da dunia lafia"
Nan take itama Ummi hawayen
suka gangaro mata, mikar da
ita tayi ta rungume ta sosai,
tana shafa bayanta alaman
rarrashi. A sannu a hankali ta
daina kukan, mikewa duk suka
yi zuwa sama domin gabatar
da sallan la'asar.
Suna gamawa suka wuce
kitchen, inda Ummi tare da
Saude suka cigaba da taimaka
ma Deedo har ta gane yadda
zata yi amfani da abubuwan
kitchen din, cikin raha da
annashuwa suka gama komai
suka jera a dinning, sannan
suka wuce domin bada farali..
Misalin karfe sha daya na safe
Deedo ta fito daure da towel a
jikinta, a hannunta dan karamin
towel ne tana tsane
yalwataccen gashinta. Gaban
mirror ta zauna, ta shafa mai
tare da Dan simple makeup. Ta
gyara gashinta sannan ta mike
zuwa wardrobe domin ta samu
kayan sakawa.
Daya bayan daya take bin lodin
kayan da kallo har ta rasa
wanne zata saka a ciki. A
karshe ta jawo wata super
peach nd coffee brown dinkin
skirt and blouse ta saka, ta
buda kallabin tayi mashi wani
mugun dauri kamar ta kifa
turmi. Kallon kanta tayi a
mirrorn dake jikin wardrobe din
taga kaman ba ita ba, a fili ta
furta "lallai sutura ita ce
mutum" murmushi tayi, sannan
ta jawo bakin gyale ta buga
abinta.
Wurin takalma ta matsa taga
duk high hill ne, ita kam ta san
ko za a sa mata wuka ba zata
iya tafia da su ba. Wani
maroon ta gani shine mai dan
tudu kuma bai cika tsawo ba
dan haka ta jawo abinta, ta
dora ta sauka zuwa palo inda
Ummi ke jiranta.
Nawap ne ya fara kallonta,
daria taso kwace mashi, amma
ya fuske yace "Ummi ga fa
autar ki ta faso"
Juyawa Ummi tayi ta kare mata
kallo, gata dai tubarkallah, kaya
sun ansheta sai dai wani
bahagon daurin kallabi da tayi
da kuma color riot din da ta
buga. Murmushi tayi sannan ta
mike tace "eyyeh! Lallai auta ta
tayi kyau, sai dai matsala daya"
taja hannun ta suka koma
sama.
Wardrobe din ta bude ta dauko
mata peach din gyale, ta bata
peach din takalmi, sannan ta
dauko mata handbag coffee
brown, ta zaunar da ita ta
gyara mata daurin kallabin
sannan tace "tashi ki gan ki"
mikewa tayi ta kare ma kanta
kallo, lallai gyara shine mace,
ta dan rufe fuskanta alaman
kunya, Ummi tace "tashi muje
kar muyi rana" ta mike ta bi
bayanta, a hankali take takawa
kasancewar bata iya tafia da
high hill ba, amma abin sai ya
bada wani style na daban…
Dagowan da Nawap zaiyi, tsab
suka hada ido, da sauri ta
dukar da kanta, inda shi kuma
ya kasa dauke idonshi a kanta,
Tubarakallah Masha Allah ya
dinga furtawa a zuciyanshi,
lallai yarinyar mai kyau ce.
Ummi ce ta katseshi da cewa
"muje mana" cikin jin kunya ya
dan sosa kai, sannan ya mike
suka wuce, amma hankalin shi
kaf yana gun yadda Deedo ke
takawa a kasaitance..
Chapter 14 · 0% Book details