← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 36

Sashe 16

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

BA’A SHAN
ZUMA…
47,48,49 &50
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Ranan wata Juma'a da misalin
karfe biyar da rabi na yamma
Deedo ta fara takowa a hankali
zuwa babban palon gidan,
sanye take da wani blue skinny
jeans, tare da wata armless
tshirt yellow mai dan fadi, an
rubuta LISTEN TO YOUR MUSIC
& SONGS. kunnenta makale da
earpiece, ta tattara yalwataccen
gashinta tayi parking dinshi a
tsakiyar kai.
A hankali take bada step, tana
dan latsa wayanta yayin da
take saukowa zuwa kasa. Duk
wanda ya kalleta sai ya kara,
saboda asalin kyaun da tayi,
tayi fes fes abinta, kaman irin
tashin birnin nan tun asali.
Karasawa tayi inda ta samu
Ummi zaune, a gefenta kuma
matar nan ce ta ranan nan,
wadda ta tabbatar da cewar
itace taji Ummi ta kira da
Aysha.
Karasawa tayi ta zauna a kasan
carpet dai dai inda Ummi take,
dagowa tayi da niyyar ta gaishe
da bakuwar amma taga idonta
kyam a kanta har lokacin da ta
zauna. Cikin siririyar muryanta,
ta kara duban Aysha tace
"aunty ina wuni"
Kallonta Ayshan ta kara yi,
sannan ta saki wani dan
murmushi yayin da tace "kina
lafia?" "Lafia lau" ta bata ansa
a takaice, inda ta maida
hankalinta akan game dinta da
take yi na candy crush. Kanta
Ummi ta shafa, sannan tace
"auta ya akayi ne?" Sai da ta
murmusa sannan tace "lafia
lau Ummi na" "Masha Allah"
Ummi ta fada, inda ta maida
hankalinta kan wayanta da take
ringing a gefenta.
Wayan ta daga da sallamarta,
tace "ai mun zata laifi muka yi,
yau kusan kwana ukku kenan
babu kai babu labarin ka"
Daga dayan gefen Nawap ya
dan yi daria, sannan ya gaishe
da ita, ya kara da "Ummi ai kin
yaye ni yanzu tunda kinyi
sabuwar 'ya" tace "to kai banda
abinka, ina zan tuna da kai ina
busy kula da autata" ta kara da
cewar "idan ka ganta baza ka
gane ta ba yanzu"
cikin raha da jin dadi suka
cigaba da firan su ta da' da
mahaifi, inda daga karshe ya
shaida mata cewar principal
din su Deedo ya mashi waya
cewar result din su ya fito, dan
haka zuwa Monday zai je ya an
so mata, daga nan zai biyo ta
kadunan. Hamdala Ummi tayi,
sannan tace "to Allah ya sa
muga alkairi" "amen" ya fada,
sannan ya kara da "a gaishe da
kowa" tace "ga autata nan, bara
ta gaishe ka" Ummi ta mika
mata wayar, ta ansa ba don
ranta ya so ba, a kunnenta ta
kara wayan, tace "Yaa Nawap
ina wuni"
Sai da ya ja wani gauron
numfashi, sannan ya ansa da
"kina lafia Autan Ummi?" Tace
"lafia lau, ya aiki?" Yace"Lafia,
Ummi ta fada maki result dinku
ya fito ko?" Tace "a'a, tana da
bakuwa ne yanzu, nasan
anjima zata fada man" yace
"ok, zanje Ningi on monday, ko
zaki je ne?" Ya fada cikin sigar
wasa, murmushi ta dan yi,
sannan tace "ka manta goggo
tace kada na koma koda ganin
gida ne?" Daria yayi sosai,
sannan yace "to shikenan,
zanje in ce kina gaishe da ita"
tace "to shikenan, amma ina da
sako dan Allah" yace "ki kira ni
idan na fita office sai ki fada
man"
A haka suka yi sallama ta mika
ma Ummi wayan, sannan ta
mike tace "Ummi bara na taya
Saude girki" yayin da take tafia
zuwa hanyar kitchen din.
Wani kallon tsana Aysha ta bita
da shi, har saida ta daina
ganinta sannan ta kyaleta,
juyon da zata yi karaf, suka
hada ido da Ummi wadda take
kallon duk abinda ke faruwa.
Murmushin yake tayi, sannan
ta dan fara kame kame, tace
"Ummi wai dama Hafsat na da
sister ne?" Murmushi Ummin
tayi itama, sannan tace "mai
kika gani?" Tace "naji kina
kiran yarinyar can da autarki,
kuma ni ban taba saninta a
gidan nan ba, ko ba nan take
zaune bane?" Ummi ta dan
muskuta, tace "owh wai Deedo
kike nufi? 'Ya ta ce 'yar
kanwata, amma Allah yayi wa
maman nata rasuwa, shine ta
dawo hannuna da zama"
Wani malalacin murmushi ta
saki, sannan tace "Allah sarki,
Allah ya jikan musulmi" Ummi
ta ansa da "amen" yayin da
Aysha ta kimtsa inata inata ta
kara ma bujenta iska.
Tana fita gidan, wayan Nawap
ta kira ya kai sau biyar amma
bai ansa ko daya daga cikin
calls din ba, haka ta hakura, ta
shilla kan motarta saman titi, ta
bata wuta..
Deedo na gama sallan
maghriba, tana zaune saman
sallaya taji wayanta ya fara
ringing, hannu tasa ta zaro
wayan, sannan ta kalla number
da take kiranta, Yaa Nawap ta
gani a rubuce dan haka tayi
saurin dagawa ta gaishe da
shi, cikin baby voice dinta mai
dadin sauraro.
Kwance yake saman 3seater,
bai san lokacin da idonshi ya
lumshe ba, a hankali ya bude
su, sanna yace "ya muka yi
dake? Ko kin fasa bada sakon
ne?" Yadda yayi maganan duk
sai ya daburtar da ita, ta fara
magana tana in'ina, "ehmm,
wlh, I'm sorry Yaa Nawap, na
shiga kitchen ne ban dade da
fitowa ba shi yasa" yadda tayi
maganan ya bala'in birge shi,
nan take idanuwan suka kara
lumshewa, ba tare da ya bude
su ba yace "idan kin gama
abinda kike zaki kwanta, ki kira
sai ki fada mun, sauran kuma
ki kara mantawa, kiga yadda
zanyi dake"
Da sauri tace, "ba zan manta
ba in sha Allah" ba tare da ta
jira abinda zai ce ba ta kashe
wayan, sannan ta mike tayi
sallan isha'i wadda taji an kira
a masallacin kofar gidan..
Rungume wayan yayi a
kirjinshi, wani irin abu ne ke
mashi yawo gaba daya jikinshi,
ya rasa tantance wane irin
yanayi yake ciki, a hankali
fuskantan ya fara yi mashi
gizo, muryanta yake ji cikin
tsararren turancinta ranan da
suke debate, a hankali ya
hango fuskanta mai cike da
damuwa a ranan da ya fara
magana da ita, sannan ya
hangota ranan da ta buga
daurin kallabin nan mai kama
da turmi, sannu a hankali
kyakkaywar fuskanta tai mashi
walkiya a ranan da suke
dawowa daga unguwa, yanayin
farin cikin da take ciki, da
yanayi na gushewar duk wata
damuwa da take tattare da ita,
shi ya bashi damar sakin wani
yalwataccen murmushi.
A hankali ya furta,
"Alhamdulillah Allah daka cika
mani burina, Allah nagode
maka daka bani damar cika
alkawarin dana dauka na
samowa marainiyar ka farin
cikinta… "
Kira ne ya shigo wayanshi,
wanda yayi sanadiyyar
katsewar tunaninshi. Da sauri
ya jawo wayan dan a tunanin
shi Deedo ce, ganin sunan
Aysha a rubuce yasa gwiwoyin
shi sakewa, inda ya daga
wayan a kasalance.
"Kina lafia?" Ya tambaya, inda
daga bangarenta, ta fashe da
wani irin matsanancin kuka
mai tsuma zuciya. Mikewa yayi
daga kishingidar da yayi,
sannan ya fara tambayar
"Aysha lafia? Ya akayi ne?"
Tambayoyi ya dinga jera mata,
amma ta ki ta bashi ansar ko
daya, kuka kawai take yi kaman
wadda aka fada ma sakon
mutuwar uwa ko ta uba! Jin
kanshi yayi ya mashi nauyi,
duk da ba son Aysha yake ba
amma yana jin kukanta har
cikin zuciyarshi, kasancewar
shi mutum mai tsananin
tausayin mace, wanda ko
kadan baya son yaga mace a
cikin wani hali.
Haske wayan ta fara yi call
waiting na shigowa, dago
wayan yayi daga saman
kunnenshi inda yaga sunan
Deedo a rubuce saman screen
din…
Chapter 16 · 0% Book details