← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 36

Sashe 27

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 83&84
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Nan da nan hankalin mutanen
da suke wurin ya dawo kansu,
kafin kace wani abu wuri ya
cika mak'il da mutane iyayen
son jin k'wak'waf. Juyowa
Nawap yayi idon shi ya
k'ank'ance, kallon Deedo yayi
cikin wani irin yanayi yace "I'm
disappointed in you, abinda
kika koma yi kenan? Irin
tarbiyyar da aka baki kenan?
Who's this guy?" Ya fada da
wata irin tsawa, wadda tasa
'yan cikin Deedo kadawa a
lokaci guda. Cikin muguwar
tsawar da tafi ta dazu yace
"I'm talking to you, kin tsaya
kina mun shirme, me sa kika
zubar da k'ima da darajarki ta
'ya mace? Me sa kika yi watsi
da hudubar da na dade ina yi
miki? Me sa baki fahimci
abinda nake ji game dake ba?
Me sa baki kulan mun da kanki
ba? Me sa kika kasa gane
cewar duk abin da nake ina yin
shi ne sabo da SO da
K'AUNAR da nake miki? I LOVE
YOU DEEDO y can't you
understand!?"
Numfashin Deedo ne ya fara
k'ok'arin sark'ewa, cikin tashin
hankali ta d'aga kai ta kalle
shi, sai a sannan abinda ya
fad'a ya fara yawo a kanshi,
"damn it" ya fad'a tun
k'arfinshi, sai kuma a lokacin
Affan ya samu bakin magana,
ya k'araso gabanshi, ya kalle
shi ido cikin ido, yace "malam
kai kuma daga ina? Me
hadinka da matar da zan aura?"
Wani mugun kallo Nawap ya
watsa mashi, a yayin da ya
dunk'ule hannunshi yana shirin
kai wa bakinshi naushi, ko me
kuma ya tuna, kawai ya saki
hannun ya juya, a fusace ya
fara tafiya.
Aysha da kuka ya k'wace mata,
ta bi bayan shi, da sauri ta tari
gabanshi tace "Nawap nice mai
sonka, wadda take k'aunarka,
zan iya jure ko wane irin cin
fuska in dai daga gare ka ne,
me sa baza ka bani dama na
nuna maka irin yadda nake son
ka ba? Ka taimaki rayuwa ta
Nawap!" Gefenta ya bi, ba tare
da yace mata uffan ba, ya
shige motarshiya tada da wani
irin k'arfi, ya wuce ya bar
wurin..
Kuka sosai Deedo ta saki
ganin Nawap ya ja motarshi ya
tafi, Affan ya matsa gabanta ya
fara lallashinta, yana fad'a
mata kalamai masu dad'i
wanda suke tafiya da ita da
imaninta. A sannu a hankali ta
samu natsuwarta, ta kalleshi
tace "ka fitar dani bakin gate
na samu abin hawa, nasan
driver ba zai zo ba" "no, bazan
iya barinki ki tafi ke daya ba,
muje na kaiki gida" dak'yar ya
lallabata, ta tashi, inda yayi
parking motar shi suka isa, ya
bude mata gaba ta shiga,
sannan ya maida murfin ya
rufe, ya zagaya ta mazaunin
driver ya shiga ya tada suka
tafi.
Baby Labo da akaje da niyyar
dambe, can na hange ta, taja
k'afafun nan nata masu kama
da na sauro ta k'arasa gaban
k'awarta, tana bata baki,
dak'yar Aysha ta mik'e saboda
kukan da take, haka dai ta
kamata suka shige motarsu
suma suka kama gabansu, ta
inda suka fara tunanin canja
shiri akan na dukan Deedo da
suka zo dashi.
Har sai da Nawap ya kawo
gida, sannan ya fara tunanin
halin da ya baro Deedo, amma
dakewa yayi, ta inda yake
ganin koma me yayi mata,
itace ta ja wa kanta, dan haka
bai shiga gidan ba, yayi
parking nesa kadan da
gidansu, yana jiran yaga yadda
za ai ta dawo gida.
Kusan mintuna ashirin ya
share yana jiran zuwanta
amma shiru, dan haka ya tada
motar da niyyar ya shige gida,
sai kuma ya hango wata ash
din Toyota Supra na k'ok'arin
danna kanta a gate din gidan
su.
Dakatawa yayi, har motar ta
shige, sannan ya bi bayan ta
shima ya shigar da tashi, nan
ya ci karo da Affan ya fito, ya
bude wa Deedo k'ofa yana aika
mata da wani sak'on kallo mai
tattare da so da kuma k'aunar
juna..

BA’A SHAN
ZUMA… 85&86
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Fitowa yayi zai shige kaman
bai san da halittar mutane
agun ba, a zahiri kuma
zuciyarsa tafasa takeyi, tana
ingizashi da yaje ya kama
Affan da duka, can kuma har
zai shiga daga ciki wanda
Affan jikinsa yayi sanyi ganin
cewa cikin d'aya ko yayanta ko
dan'uwanta bai ankara ba yaji
Nawap na cewa maigadi
"yaushe ka fara barin samari
suna shigo mana cikin gida?"
Dasauri mai gadin ya nufi inda
Affan yake tare da cewa "mai
gida don Allah kad'anyi hakuri"
Wani k'ullutun bak'in ciki yaji a
zuciyarsa yana kallon Nawap
anma rashin sanin wayeshi yafi
komi 6ata mishi rai, ya kalli
Deedo wacce duk ta rikice tana
neman madafa yace "ki shiga
zamuyi waya" tayi shiru kaman
zatayi magana saikuma ta
shige, motarsa yaja yafice
yayinda shikuma Nawap
yashige palo ya zauna, yana
ajiyar zuciyar kamar wanda
yafito daga filin daga.
A hankali take tafiya zata wuce
yace "zo nan" jikinta na bari ta
zo ta tsuguna kanta a kasa,
cikin mugun gushi yace
"Inaso kigayamun wanda
yabaki izini kiyi saurayi" shiru
bata amsa ba illa hawaye da
yake kokarin zubowa, ganin
hawayenta yafi komi cimasa rai
anma haka yarufe ido ya fara
zuba mata yayyafin masifa ta
inda yake shiga ba ta nan yake
fita.
Muryarsa Ummi tajiyo tafito, a
yadda yake masifan kaman uba
ya kama 'yarsa tana zina, abin
ya matuk'ar bata mamaki sanin
cewa bata taba ganinshi
awannan yanayin ba, idonsa
yayi jajur ya cicciko, ya kalli
Ummi sannan yace "Ummi da
wani fa na ganta"
Sai da ta nemi wuri ta zauna
sannan tace "toh daka ganta
da wani shi ne yazama laifin
me? Wayeshi kekuma?"
Kuka take sosai yayinda ta
goge hawayenta tace "wanda
ya tayani registration ne"
Nawap ya katseta da cewa
"ohhhh shine kuka hau
soyayya, Ummi can u imagine
har yana ce mun ni waye meya
had'ani da matar da zai aura"
Abun yabawa Umma dariya
ganin yadda Nawap karara
yake nuna kishinsa.
Anan tace wa Deedo ta tashi ta
shiga ciki, shikuma tace "
kamata yayi in sonta kakeyi ka
fad'a mata, baka fito kana
takura mata ba, zata tsaneka,
mu mata bama son takuri
munfi gane lallab'i inka bincika
lallab'ata yakeyi shima wancen
din" fuskarshi cike yace "Ummi
yaro ne fa, irin chewing gum
boys din jami'a"
Dariya tayi sannan tace "ahaka
kuma ya take ka agun nema
ba, dole ka koyi sassauci ka
koyi danne zuciyarka idan
mace kakeso, kacire maganan
dizgi da takuri karka kara yiwa
y'ata tsawa haka, ji yadda ka
sata zubar da hawaye" tana
gama fad'in haka ta mike ta bi
sawun Deedo wacce ko da taje
d'akin ma fad'awa tayi akan
gado tana kuka, har ranta
bataji dadin yadda Nawap ya
mata ba, sai dai ta wani fannin
kuma ji tayi kaman ansauke
mata dutse a ranta ganin yau
ya furta mata da kanshi cewa
yana sonta..
Chapter 27 · 0% Book details