← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 36

Sashe 21

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 64, 65
&66
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Yana karasawa gida wanka
yayi yanufi masallaci, bayan ya
fito ne yashigo cikin gida anan
ya ga feedo kwance akan
doguwan kujera, sanye take da
riga da wando, kanta ba
dankwali ta tattare gashin ta
baya ta daure, sai da ya kare
mata kallo kafin yayi sallama,
da sauri ta mike ta zauna tana
kokarin nemo hulanta wanda
dama ya fadi ne ta baya, "ina
wuni"tace dashi, ya ansa, ya
kauda kansa sannan yace "ki
shirya gobe muje in kaiki
saloon" ta ce "toh, dama dazu
ummi ta gama maganan" ruwa
ya dauka a fridge sannan ya
fice.
Washegari karfe goma ta
shirya tsaf tana jiransa, yazo
suka gaysa da ummi inda ya
mata bayanin cewa yaje
maganan admission din Deedo,
taji dadi sosai sannan yace
Deedo ta fito su wuce, ta shiga
motan sannan ta rufo, yajasu
suka fice, bai tambayeta inda
zai kaita ba kawai taga ya nufi
wani saloon da ita, Tripple D
Beauty and Care saloon taga
an rubuta, saloon din ya hadu
sosai domin babu abinda basa
yi ajikin board din takaranta,
nan ya ciro dubu biyar ya mika
mata tare da cewa "inkin gama
ki kirani"
shigewa saloon din tayi,
tasamu mutane biyu agabanta
don haka tazauna jira, har
akazo kanta, anwanke mata kai
ana kokarin sata a dryer saiga
Aysha da kawarta sunshigo, da
farko murmushi take tana
dariya, ganin Deedo yasa ta
dauke annurin fuskanta tamkar
taga malaikan mutuwa, taja
wani mummunan tsaki sannan
tanemi gu tazauna, hankalin
mutane ya nufi kanta jin tsakin
da tayi, Deedo ma ganinta yasa
tagane da itane, anma
kasancewar tasan ta girmeta,
sai bata nuna alaman ta ji
bama, nan ta ce "ina wuni?"
Bata amsa ta ba, hakan yasa
itama ta kauda kanta, kawarta
ce take kokarin cemata ana
mata magana, nan cikin fadin
rai da iko tace "itace
munafukan danake miki
bayani" habawa tuni kawar ma
ta daure fuska "awh! Ai sai kice
min ga snatcher, lallaima ina
zaki kai wannan abun?"
"Tayani ji dai inbanda namiji
da ruwan ido da rashin sanin
daidai, Allah wadaran tsiya inji
arziki" Deedo duk tana jinsu
bata tanka ba, hatta yan saloon
din ma kowa dai yayi shiru ne
don yadda suke maganan zai
tabbatar dacewa da dayansu
akeyi
Aysha takalli kawar ta sannan
tace "kinsan wani abu ma
kuwa?"
"A a saikin fada"
"Ita fa take binshi, sai
shishigewa take, matsiyaciya
tazo tashiga arziki, ta kainane,
a zatonta yatsu tsayinsu daya,
dontaga ita yar uwa ce"
Kawar ta tabe baki sannan tace
"ji munafukar kamar ba da ita
ake ba" kafin Aysha ta amsa
tanufi kan Deedo taja gashinta
, matan ta fara bada hakuri
yayin da Deedo tamike tare da
cewa "kuyi hakuri, anma duk
abunda kuke fada bahaka
bane" bata idar ba taji anwanke
ta da mari, hannu tasa tarike
fuskan alokacin yan saloon din
suka mimmike don kawowa
mata agaji, tuni Aysha da
kawaarta suka hau dukan
Deedo har sai da suka yaga
mata riga.
Wayanta taciro da kyar takira
Nawap, batayi magana ba yana
kokarin cewa hello yaji
hayaniya yayi yawa, dama baiyi
nisa ba nan da nan yajuyo
yataho, yana isowa ya bude
kofan motan ya manta baima
kulle ba yashiga saloon din
ganin Aysha da Deedo ko baa
fada masa ba yasan abunda
suka aikata mata tunda ga
riganta ayage tana kokarin rufe
jikinta, idonshi tuni ya canja
kala yayi jajur ya kalli mai
saloon din tare da cewa "meya
faru?" Ta mayar masa da komi
kamar yadda ya faru, alokacin
yaji kamar ya shako Aysha ya
kashe don bakin ciki, ya ruko
Deedo ya sanyata a mota bai
ce komi wa Aysha ba wacce
jikinta sai bari yake,
Rufo motan yayi yabawa mai
saloon kudinta sannan ya tuka
suka fice, kuka take tayi anma
yarasa ta yadda zai fara bata
hakuri, danne zuciyansa yayi
tareda cewa "kiyi hakuri duk
abunda ke faruwa saboda ni
ne, Aysha tadauka nemanki
nakeyi, kiyi hakuri ahankali
zata gane gaskiya" bata ce
komi ba har suka isa, tuni
tabude motan tashige gida,
daki tanufa saboda ta canja
kaya, Nawap kuma yana
tunanin abunda zaifada idan
Ummi ta tambayeshi meya faru,
duk da yasan Deedo zata fada.
Bai shiga gidan ba sai dare
inda yaga Deedo sai dariya
take suna tadi da Ummi, kuma
da ya zauna baiga sauyi ba
don anhada dashi ana tadin,
nan ya tabbatar da cewa Deedo
bata sanar da ummi abunda
yafaru ba. Cikin zuciyanshi
mamaki yake ita wace irin
yarinya ce, bai ce komai ba,
haka ya daure ana dan tadi
dashi, daga bisani ya mike ya
wuce part dinshi inda ya
cigaba da tunanin abun da zai
yi ma Aysha ko dan ta fita
hanyarsa..
Ranan da zai koma Abuja ya
gama shirinsa tsab, ya saka
kayanshi a mota, ya shiga cikin
gidan yayi ma Ummi sallama,
amma bai ga Deedo ba, fitowa
yayi zai wuce, a dai dai nan ya
hade da ita zata shiga kofan
palon, hannunta ya jawo suka
bar wurin zuwa bakin
motanshi, yana kallon kwayan
idonta yace "ni zan wuce lil
sis, ba lallai ina nan admission
dinku ya fito ba, amma zan
hada ki da Dr. Kashim phrnd
dina ne, nasan zai maki komai
in sha Allah, dan haka abinda
nake so dake shine ko kinje
skool ba ruwanki da samarin
banza bata gari, wanda basu
da aikin yi sai hure ma yara
kunne, ki natsu, kiyi abinda ya
kaiki, kina jina? Nd ina mai
kara baki hakuri akan abinda
Aysha ta miki, I promise yu
hakan ba zai sake faruwa ba
kinji?"
Murmushi ta saki, tace "in sha
Allah zan cika umarninka Ya
Nawap, Allah ya tsare hanya"
ta juya zata wuce, sai ya ji
kamar kada ya tafi ya barta, da
sauri yace "baza ki jira kiga
tafiyana bama" bata ce komai
ba, sai murmushin data saki,
hannayenta ta harde, ta tsaya
tana kallonshi, hakan da tayi ya
bala'in yi mashi kyau, ba tare
da bata lokaci ba ya zaro
wayanshi, ya kyalla mata hoto,
dariya tayi, ta rufe fuskanta,
haka ya cigaba da daukanta
har sai da yaga yana niyyan
makara, sannan yace tazo, ta
matso kusa dashi, dan haka ya
daukesu tare, sunyi bala'in
kyau, sai a lokacin yaga ashe
har kama suke yi.
Ba don ya gaji da ganin Deedo
ba, yai mata sallama ya shige
mota, inda ya cigaba da
jaddadada mata cewar ta kula
da kanta, tana murmushi ta
daga mashi hannu har sai da
ya fita gate din gidan, sannan
ta shige ciki.
Yana fita, gidansu Aysha ya
zarce, a bakin gate ya hade da
ita, da alama office zata fita,
parking yayi ya fito daga motan
ya karaso gabanta. Yanayin da
ta ganshi ta san ba mutunci,
kuma dama ta dade tana jiran
wannan ranan, dan haka ta
kama kanta, ta fara raba idanu,
kaman shege a rabon gado.
Nuna ta yayi da hannunshi,
yace "this shud be last
warning, ki fita hanyar yarinyar
mutane, idan ba kina so fita
daga cikin gidanku ya gagareki
ba, na fada maki bana son ki,
to menene na yi mun
shishshigi a rayuwa, ki tsaya
matsayinki, if not, zaki ga
abinda zai biyo baya" ya juya a
fusace, yana fadin "maran
zuciya kawai" ya shige
motanshi ya bata wuta.
Aysha saboda bakin ciki bata
ce komai ba sai mazurai da
take, nan take hawaye suka
cika mata ido, kuka ta cigaba
da yi kaman an bude famfo,
cikin kunan zuciya tace "baza
a rabu da kai din ba, sai an
soka din, kuma in dai wannan
shegiyar yarinyar ce yanzu na
fara takura mata har sai wahala
tasa baza ta taba sonka ba,
wanda bai son abinda ya dace
dashi ba kawai, wannan har
wani abun so ce" ta ja tsaki ta
share hawayen, tace "bari dai
kawata ta dawo daga tafiyan
da tayi, wallahi sai mun koya
ma yarinyar can hankali" ta
jawo mirror cikin jakanta ta
gyara fuskanta, sannan ta yi
ma motar key ta bar gun..
Chapter 21 · 0% Book details