← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 36

Sashe 29

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

BA’A SHAN
ZUMA…
93,94&95
BA'A SHAN ZUMA… 93
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Gida ta dawo zuciyarta wasai,
tana jin tamkar ta sauke wani
gagarumin nauyin dake kanta.
Bayan sun gaisa da Ummi ta
wuce sama, don ta shirya ma
wannan rana, domin alkawari
ta yi yau zata fada ma Yaa
Nawap ta ansa tayin
soyayyarsa, don haka take son
tayi surprising dinshi ta hanyar
kawata mashi kanta da ado na
ban mamaki da daukar hankali.
Number sa ta laluba ta kira
amma a kashe, ba tare da wata
damuwa ba tai mashi text "I
need to see my big bro" ta tura,
amma bai yi delivery ba,
hankali kwance ta gama
shirinta tsab, ta sauko kasa
amma ba kowa a palon, ga
wani shaukin son Yaa Nawap
da yake fisgarta, bata da buri a
lokacin wanda ya wuce mata
ganin fuskar shi. Ko ina ta
dudduba amma babu kowa a
cikin gidan, ba tare da wata
fargaba ba ta zarce part dinshi,
a hankali ta tura kofar palon,
amma ga mamakinta ta jita a
datse gam.
Cikin natsuwa take
kwankwasa kofar amma shiru,
dukawa ta yi ta dan leka ta
inda ake sanya key, nan taga
jam lock, cikin rashin jin dadi
ta juyo ta dawo cikin gidan, a
palo tayi arba da Ummi, nan ta
fara kame-kame, amma Ummi
ta basar tace "ina kika shiga
ina ta kwala kiranki?" "Na dan
zagaya nan baya ne in sha iska
Ummi" tace "to, wuce ga abinci
can" dining area ta nufa ta
zuba abincin ta ci gaba da juya
spoon din tana tunanin inda
Yaa Nawap ya nufa, domin shi
dai yawo ba al'adarshi bace
matsawar yana gari to fa kullun
yana gida kaman mace.
Ummi tana hankalce da
yanayinta amma ta basar, don
bata son ta takura mata sai
taga kamar don ba ita ta
haifeta bane. Spoon biyu kawai
tayi a abincin ta taso ta dawo
gefen Ummi ta zauna ta kurawa
wayanta ido tana jiran taga
delivery na sakon da tayi wa
Yaa Nawap.
Can dai zuciyarta ta kasa
daurewa, tace "Ummi ni kam
ina Yaa Nawap ya shiga?
Rabon da na ganshi tun
shekaran jiya" murmushin jin
dadi Ummi tayi a fakaice, ta
san ko bakomai d'an nata ya
fara samun kar6uwa a zuciyar
Deedo. Ta kalleta tace "jiya tun
kafin ki tashi bacci ya koma
Abuja an mashi kiran gaggawa"
ta dan saci kallon ta taga
yadda hankalinta ya tashi
lokaci guda, sannan ta cigaba
da magana…
BA'A SHAN ZUMA… 94
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
"Bayan ya isa kuma wurin karfe
shidda na yamma ya kira ni
yake sheda mun cewar yau da
misalin karfe biyar na asuba
zasu tashi zuwa London, an
tura su yin wani course na
shekara ukku" tana kawowa
nan taja bakinta tayi shiru, tana
mai cigaba da kallon akwatin
t.v.
Mikewar da Deedo zata yi taji
wani mugun jiri ya kwashe ta,
kukan da take makalewa a take
ya subce mata tagal tagal tayi,
tana me kokarin faduwa, nan
Ummi ta kwashi salati tana
kwalawa Saude mai aiki kira,
cigaba da jijjigata tayi tana
fadin "lafiya Deedo? Menene
abin kukan?" Cikin rashin sani
Deedo take magana "Yaa
Nawap me sa kai mun haka,
bayan kasan kaine buri na,
kaine farin cikin rayuwa ta"
kuka ta kuma fashewa da shi
ta koma kaman zararriya, ta
kalli Ummi da tausayin Deedo
ya cika ta, tare da jin dadin
kalamanta, tace "Ummi da
gaske Yaya ya tafi ya barni?
Ummi ya zan yi da DAKON SO
(Na KAUSAR LUV) na Yaa
Nawap da nake fama dashi?"
Ta k'ara fashewa da wani
kukan mai ban tausayi..
Dak'yar Ummi ta lallaba
Deedo a wannan rana, banda
kuka ba abinda take yi, haka
dai Ummi ke kwantar mata da
hankali, yayin da wutar
soyayyar Nawap take faman
kara ruruwa cikin zuciyarta
tamkar ana watsa mata fetur.
* ***–******
Da sallama suka shigo palon
ba kowa sai Deedo da ta
kurawa wani makeken hoton
Yaa Nawap dake mak'ale a
palon ido, wanda ya kasance
sana'arta kullun da ta dawo
daga makaranta bata da sauran
aikin da ya wuce ta zauna
gaban wannan hoto tayi ta
kallonshi, wani lokacin har da
yan sambatun da baza a rasa
ba.
Aysha ta karasa ta dafa
kafadar Deedo, sai a sannan ta
dago a razane dan ko alama
bata ji shigowar mutun ba.
Kallonta tayi a tsorace, inda ita
kuma ta sakar mata murmushi
tace "Ina Ummi fa?" Murmushin
k'arfin hali ta mayar mata, tace
"ku zauna mana, taje unguwa
ta dawo" su Baby Labo aka ja
yan kafafuna aka karasa cikin
palon aka zauna a kujera ana
aika ma Deedo sakon
murmushi.
Ita kam abin ya bata
mamaki, mutanen da suke
neman ta su daketa sune suka
dawo kamar ba su ba, anya
babu wani kulli a kasa? Ta dai
daure ta kwala kiran Saude ta
kawo masu dan abin motsa
baki, yayin da Aysha ta fito da
I.V na guda ukku ta mik'awa
Deedo, tace "da naki, da na
Ummi, wannan kuma na daurin
aure ne ki bama Nawap"
[18/04 23:41] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 95
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Ansa tayi idonta waje ta duba
da kyau, tabbas bikin Aysha za
ayi, cikin zuciyarta tace "har ta
hakura da Nawap din kenan"
tunani ta fara itama ko hakura
za tayi dashi, tunda bai damu
da ita ba, gashi yau kusan wata
daya da tafiyarsa amma ko a
waya bata jishi ba, Ummi ma in
zai kira ta sai yayi hiding
number sannan, tasan kuma
duk don saboda ita yake
hakan. Aysha ce ta katse mata
tunani ta hanyar cewa "ya dai?
Naji kinyi shiru ko congrats
babu" murmushin dole tayi,
tace "I'm so happy 4 yu, sai
dai kuma Yaa Nawap baya nan,
yaje yin wani course London,
amma in sha Allah zaki ganmu
ni da Ummi" "Allah ya sa"ta
fada, sannan suka mike a tare,
ta d'an taka masu zuwa inda
sukai parking sannan ta dawo
ciki, tana me cike da mamakin
sauyawan da Aysha tayi lokaci
guda.
* *–****
Cikin yarda da hukunci irin
na ubangiji, aka yi bikin Aysha
da angonta Saifullahi, wanda
dak'yar Ummi ta lallaba Deedo
ta leka wurin dinner. Haka ma
aka sha bikin Hally, aka kaita
Bauchin Yuguda, amma Allah
bai ba Deedo ikon zuwa ba,
kasancewar rashin Yaa Nawap
wanda ya kasance wani jigo na
rayuwarta, tafiyarsa ta zama
wani gi6i a rayuwar Deedo,
domin tana jin tamkar ta rasa
shi ne har abada, ga wani irin
son shi da ya bi ya addabi
zuciyarta, gani take ashe son
da tayi wa Affan ba soyayya
bane shak'uwa ce kawai, amma
asalin so na zahiri Nawap take
yiwa shi, sai dai bata gane
hakan ba, sai yanzu.
Idan tana tunanin shi ta kan
zubar da hawaye domin shine
kawai abinda take yi ta samu
sassauci a cikin birnin
zuciyarta. Ummi ce ma take
dora ta akan yawan addu'oi
domin kuwa addu'a takobin
mumini ce kuma ta kan
taimaka ma bawa a kowane irin
yanayi.
Shawarar Ummin dai ta bi,
idan abun ya dameta ta kan yi
salloli tare da addu'oi, sannu a
hankali ta fara samun natsuwa,
ba wai don ta daina jin DAFIN
SO (coming soon) na harbin
zuciyarta ba, sai don
fawwalawa Allah dukkan
lamurranta da tayi, ta maida
hankalinta ga karatun ta,
wanda take ganin shine kawai
abinda zata yi ta farantawa Yaa
Nawap dinta.
Chapter 29 · 0% Book details