← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 36

Sashe 22

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 67-69
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Haka rayuwa ta cigaba da
tafiyan ma Deedo hankalinta
kwance, bata da sauran
matsala, gashi kuma ta kan
kira Hally su sha labarin
duniya amma ko ta tambayi ya
su Goggo, Hally zata
shashantar da maganar bata
ma son ko kadan Deedo na
tunawa da Goggo, yau ma
kwance take a daki suna waya
da Hally take ce mata ta samu
admission a ATBU, har ma ta
fara registration, Deedo ta mata
murna sosai, inda take
tambayar "ya maganan naku
admission din?" "Muna kan jira
muma, in sha Allah" "Allah ya
taimaka" ta fada, haka suka
cigaba da tadinsu cikin jin
dadi, daga karshe tai mata
sallama ta mike, domin gabatar
da sallahn azahar.
Bayan ta gama sallah tana
zaune kan sallaya taji wayanta
yayi kara, ta dauko ta duba,
email ne ya shigo daga KASU,
sun bata admission a faculty
of Medicine and Surgery.
Murna sosai take yi, da gudu
ta mike da niyyar zuwa dakin
Ummi, wayan Yaa Nawap ce ta
katse mata hanzari, cikin sauri
ta daga wayan tare da gaishe
shi cikin zakuwa, shiru yayi
yana imagining farin cikin da
take ciki, nan da nan ya ji
inama yana da iko da sai dai
su ganshi a gida kawai.
Murmushi yayi yayin da ta
katse mashi tunani ta hanyar
cewa "Yaa Nawap dama yanzu
zamu kira ka" "ni da na fi
damuwa daku ai gashi na riga
ku kira, kuma da babban
albishir na zo"
Cikin zakuwa tace "nima
albishir ne zan maka, amma ka
fara fada mun naka 1st"
murmusawa yayi, yadda take
maganar duk ta tafi mashi da
wata kasala da yake tare da ita,
idonshi a lumshe, yana juyawa
a kujerar office dinshi, yace
"yanzu Dr. Kashim yai mun text
sun baki admission" murmushi
ta saki mai taushi, kaman yana
gabanta, tace "shine albishir
din da zan maka nima, yanzu
email ya shigo mun"
"congratulations, sai ki shirya
on monday, kuje tare da driver,
zan hada ki da Dr. Kashim ki
fara registration ko" "nagode
Yaa Nawap Allah ya saka da
alkairi" "issokay" ya fada, inda
a lokaci guda yai mata sallama
ya koma bakin aikinshi.
Dakin Ummi ta wuce da
murnarta ta shaida mata yadda
sukai da Nawap, Ummi ta
rungume ta suna ta jin
dadinsu, tace "tashi mu wuce
kasuwa, ai zama bai ganni ba
auta zata tafi jami'a" murmushi
tare da hawayen farin ciki ne
suka gangaro a fuskar Deedo,
ta share, sannan ta mike ta
wuce daki ta fara shiri.
Siyayya sosai Ummi tayi ma
Deedo, dangin kayan sawa,
takalma, jakunkuna da sauran
tarkace na 'yan matan jami'a. A
gajiye liss suka dawo gidan
wurin karfe biyar na yamma,
wanka tayi, tayi sallah, sannan
ta gangaro palon don ta samu
damar hutawa, Ummi ta tadda
tana bude kayan da suka siyo,
inda ta zauna itama suka
cigaba da budawa tare, daga
karshe Ummi tayi ma tailansu
waya, domin yazo ya anshi
kayan dinki.
* **
A daddafe Nawap yake rayuwa
a garin Abuja don wani
matsanancin kewar Deedo da
ke damunshi, wadda ya rasa
tantance ko menene dalilin.
Pictures dinta kawai yake kallo
ya samu natsuwa cikin ranshi.
Ga aiki ya sakashi gaba sosai,
bashi da wani lokaci balle yayi
tunanin samun damar zuwa ya
ganta.
Da misalin karfe biyar na
asubar ranar litinin, wadda tayi
dai dai da daya ga watan
February, 2016 (1st Feb, 2016)
Deedo ta tashi, wanka tayi,
sannan ta doro alwala ta fito.
Sallah tayi, ta zauna a wurin ta
cigaba da azkar har wurin karfe
bakwai na safe, daga bisani
tayi addu'ar neman sa'a a
karatunta, da kuma rayuwarta,
ta kara da neman tsari daga
dukkan wani sharri na rayuwa.
Daga karshe tai ma Ummi
addu'ar da ta saba, sannan ta
nema ma iyayenta gafara a
wurin mai kowa mai komai.
Gaban dressing mirror ta isa ta
shafa mai tare da designers
din turarukan da suke zube a
wurin, simple make up tayi,
sannan ta matsa gaban
wardrobe din ta buda tana
tunanin wane kaya ya dace ta
saka a wannan farar rana.
Wata super java ta dauko, mai
kalar light orange nd purple,
dinkin skirt nd blouse ta saka,
wasu round dankunnen ta
sanya masu kalar gold, ta
daure hannunta da agogon
Vintage, itama dai kalar gold
din ce, bracelets ta sanya a
dayan hannunta na hagu,
sannan ta dora zobuna na
isassun yan mata, wanda duk a
cikin siyayyar da Ummi tayi
mata suka siyo da su.
Lafiyayyan daurin yan zamani
tayi, sannan ta jawo gyalenta
purple, takalmanta da handbag
dinta kirar Jimmy Choo wanda
suka kasance reddish brown,
ta sanya, ta dauko handbag
din, ta kara feshe jikinta da
turaruka na alfarma, sannan ta
fito. Karfe tara lokacin har da
minti biyar, dakin Ummi ta
shige, inda ta same ta tana
breakfast. Dukawa tayi har
kasa ta gaisheta, Ummi kam
binta tayi da kallon mamaki,
anya wannan autarta ce? Da
murmushinta ta ansa, tace
"wannan duk kyau ne Deedo?"
Kanta a kasa tana dan
murmushi, ta zauna kusa da
Ummi ta fara hada tea.
A gurguje tayi breakfast din ta
gama, Ummi dai sai yaba kyau
da gayun Deedo take, bayan ta
gama fitar da kwanukan, ta
dawo tayi ma Ummi sallama,
inda tayi mata nasiha mai ratsa
jiki kan ta kula da mutuncinta,
ta kuma tsare martabar
gidansu. A haka suka sauko
palon tare da Ummi, ta dauka
kudi ta bata, sannan tayi kiran
driver, tace ya kaita skool, idan
ta gama sai tayi waya, yaje ya
daukota. Cikin zakuwa ta
rungume Ummi, tayi mata bye,
ta wuce ta shige motan.
Tana shiga wayan Nawap ya
shigo, da murnarta ta daga ta
gaishe da shi, sai da yaja
numfashi, sannan ya ansa,
tambayarta ya fara "kin shirya
ne?" Tace "gamu zamu tafi
ma" yace "ina fatan dai bakiyi
wani kwalliya ba, dan karatu
zakije ba fashion parade ba"
murmusawa tayi, sannan ta
kalla mirrorn gaban motan,
tace "ban yi ba fa Yaa Nawap"
yace "idan kina son na yadda
ki mun snapping kanki, ki tura
mun ta whatsapp yanzu" "to"
kawai ta fada, yai mata bayanin
yadda zata ga Dr. Kashim, dan
shine zai mata komai ya kuma
hada ta da wannan zai taimaka
mata wurin registration. Daga
karshe cikin wata irin murya
mai sanyi yace "I wish ina tare
dake a irin wannan ranar lil
sis" kasa magana tayi, saboda
yanayin da yayi maganan bata
san ya zata fassara shi ba,
murmushi kawai tayi, tace
"thanks for everything Yaa
Nawap, sai na kira idan naje
skool din" ta kashe wayan
lokaci guda, sannan ta dauka
selfie ta kunna datan ta tura
mashi, tayi bala'in kyau kamar
aljana, ta kashe datan ta jefa
wayan cikin jaka.
Suna shiga office din Dr
Kashim ta nufa direct, ko da
bata fada mashi ba ya san ita
ce sister Dr. Nawap, saboda
asalin kamar da yaga suna yi.
Gaishe dashi tayi, sannan ta
samu wuri ta zauna, bayan ya
ansa, yace "Firdausi, ryt?" "Yes
Sir" ta fada, yace "ina fatan
kinzo da credentials dinki baki
daya?" "Eh na zo da komai" "ok,
lemme call someone who will
assist yu" "Ok Sir" ta fada,
yayin da ta dukar da kanta, ta
cigaba da wasa da 'yan yatsun
hannunta.
Wayanshi ya dauka ya kira
wani, yace ya sameshi a office
yanzu. Cikin mintunan da basu
wuce sha biyar ba, aka turo
kofar office din aka shigo,
kanshin wani lafiyayyan turare
ya daki hancin Deedo inda a
lokaci guda taji zuciyarta ta
buga da karfi, kafarshi ta fara
kallo ta ganta lullube cikin
lafiyayyun sneakers black nd
white kirar Tommy Takkies, a
hankali take dago kanta, sanye
yake da bakin pencil jeans, da
white t-shirt ta Ralph Lauren,
hannunshi daure da agogon
fata baka kirar Orlando, kasa
dauke idonta tayi lokacin da ta
yi arba da kyakkyawar
fuskarshi, gashin kanshi ya
kwanta luf, sai kyalli yake
kaman na jarirai, kallonshi take
kaman yau ne rana ta farko da
ta fara ganin bil adama.
Kallonta yake shima, inda cikin
zuciyarshi yake nanata "tsarki
ya tabbata ga Allah, ubangijin
da ya tsara wannan kyakkyawar
halitta!" Murmushi ne ya
subuce mashi, inda itama a
lokaci guda ta sakan mashi
nata kayataccen murmushin…
Chapter 22 · 0% Book details