← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 36

Sashe 26

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 79&80
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Wani fanni na zuciyarta ne
yake fada mata "ya damu da ke
ne da kuma al'amurranki, kuma
ko bakomai Yayanki ne wanda
ya cancanci kiyi mashi biyayya
a kowane irin hali" girgiza
kanta tayi, alaman ta gamsu, a
karo guda kuma ta fara kiran
numbershi amma shiru. Saida
ta kira har sau hudu, amma bai
dauka ba, hakan ya tabbatar
mata cewar lallai Nawap yayi
fushi da ita, daga k'arshe da
taga zaman ba zai kaita ba,
dan haka ta yanke hukuncin
tura mashi text na ban hak'uri,
inda take bayyana mashi cewar
ba wai abinda yake tunani
bane.
* ****
Wasa wasa har ta suka fara
lectures, amma Nawap bai
k'ara bi ta kan Deedo ba, dan
ko waya suke da Ummi da ta
bata wayar yake kashewa. Bata
damu da irin abinda yake yi ba,
dan a tunanin ta ko ya bata
freedom dinta ne, dan haka ta
ba Affan dama suka fara
shimfid'a nagartacciyar
soyayya mai asalin dad'i da
kuma tsafta, hakan yasa har
aka fara sheda su a cikin
makaranta, dimin ko da yaushe
suna manne da juna, idan
bashi da lecture haka yake
rakata har sai ta gama
lectures, yayin da itama hakan
yake a wurinta, basa iya
rabuwa ko kadan sai abinda ya
zama dole.
Yau ma kamar kullun zaune
suke gaban faculty suna
tad'insu na masoyan da suka
zurfafa a cikin son junansu,
wata bak'ar mota k'irar Corolla
S ce tayi parking daga gefen
da suke. Kamar ance ma
Deedo ta kalla wurin, cikin
firgici tayi arba da fuskar
k'awar nan ta Aysha wadda
suka nad'a mata duka a
saloon. Cikin yanayi na
mamaki matar take kallon
Deedo, bata gaskata abinda
take gani ba saida tayo tattaki
har zuwa inda suje, a dai dai
lokacin ita kuma Deedo tace
ma Affan ya tashi su bar
wurin.
Mik'ewar da zasuyi taji caraf
matar ta damk'e hannunta gam,
cikin fargaba ta zare ido tana
kallonta, can murya dashe tace
"ina wuni aunty" wani
malalacin murmushi matar ta
saki, sannan ta matso daf da
kunneta tace "hey you lil bitch!
Nan kika dawo kenan? Kin bar
mu muna shan wuyan
nemanki. Ina mai yi maki
albishir da ki shirya taranmu
nida k'awata, domin muna nan
zuwan miki, domin ke baki kai
matsayin fa za'a ci mana
mutunci saboda ke ba" tayi
wurgi da hannun sannan ta
dafa kafadarta tana murmushi
tace "see you 'yan mata" ta
juya ta cigaba da tafiyan ta.
Sai a lokacin Affan ya kula shi
kadai yake tafiya, bai wani
b'ata lokaci ba ya dawo, yace
"meke faruwa ne? Kin bar ni
ina tafiya ni daya"
Murmushin yak'e ta k'ak'alo,
tace "I'm sorry, ina gaisawa da
mutane ne, muje mu tafi" a dai
dai nan drivernta ya iso, dan
haka sukai sallama ta wuce
gida, zuciyanta fal da tsoro da
tunanin abinda zai biyo baya.
Lokaci na tafiya, yayin da
abubuwa da dama suke
shud'ewa, rayuwar Deedo ta
zama sabuwa, ta inda in ba
wanda yayi mata cikakken sani
ba, ba lallai ya gane ta ba, ta
zama cikakkiyar budurwa mai
madaidaitan shekaru kusan
goma sha bakwai, (17) kenan,
ta waye ta goge, tayi clean
abin sai dai wanda ya gani. Da
sauri take ta shiri dan tana da
exams k'arfe biyun rana,
kasancewar sun fara exams
d'in first semester, gashi kuma
tana son ganin burin ziciyarta
kafin ta shiga exams din.
Duk wannan abu da ake, har
yau Nawap bai shigo Kd ba, ta
inda ya daina kiran ta kwata
kwata, ya kuma daina chatting
da ita ta ko ina. Wannan ya
bata damar sakankancewa ta
cigaba da b'arje gumin
soyayyarta, ita da Affan.
Hakan bai k'ara komai ba, sai
asalin so da kuma k'aunar
Deedo wanda suka cigaba da
wanzuwa a cikin zuciyarshi,
suke kuma azabtar dashi.
Kasancewar yau Juma'a, da
wuri ya tashi ya fara shiri,
jakunkunanshi guda biyu
babba da k'arama ya jawo ya
cika su dam, da kayanshi, ya
tattara takalmanshi, da duk
wani abu mai muhimmanci,
sannan ya wuce toilet yayi
wanka, ya fito. Fuskarshi babu
yabo, babu fallasa, haka ya
fara shiri, ya gama tsab, ya fito
cikin shaddar Gezna fara k'al,
ya d'ora hularshi zanna mai
kwalliya bak'i da ash, ya sanya
bak'in takalmin ALDO, sannan
ya d'aure hannunshi da
lafiyayyar b'akar agogon fata,
ta Promado Royal.
Dan da nan ya fito tass dashi
kamar sabon ango, ya feshe
jikinshi da turaruka, sannan ya
fara kwasar kayan shi yana
sanyawa a boot din motarshi.
Gudu yake yi sosai, domin
baya son ya tsaya ko ina sai a
cikin garin Kaduna.

BA’A SHAN
ZUMA… 81&82
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Cikin ikon Allah Nawap ya iso
Kaduna k'arfe d'aya da yan
mintuna, bai b'ata lokaci ba ya
wuce massallacin Juma'a yabi
jam'i, sannan ya wuce gida.
Ummi tana zaune ta ganshi
kamar wanda aka jefo daga
sama, da murnanarta, ta tarbe
shi tana mashi lale marhabun
da mutanen Abuja. Cikin jin
dad'i ya zauna suka gaisa,
sannan suka cigaba da
tad"insu na d'a da mahaifiyar
da suka dad'e basu ga juna ba.
Ido ya ware yana ta jiran
saukowar Deedo, amma shiru
kake ji, Ummi ce ta so ta
fahimci halin da yake ciki,
kasancewar yadda yake yawan
kallon stairs din benen, dan
haka tace "wai baka ce ina
auta ta ba"
Yace "ina niyyan tambayarta
inda take ai Ummi" "tana skool,
kasan har sun fara exams"
nunawa yayi kaman bai sani
ba, yace "eyya, abin ba wuya
kenan, to Allah ya taimaka"
Ummi tace "amin." Har ya mik'e
zai wuce side dinshi, ya juyo
yace "k'arfe nawa zata gama
exams din na yau?" "K'arfe
biyar" Ummi ta bashi ansa, bai
k'ara cewa komai ba, ya wuce
domin ya samu damar hutawa.
* **
K'arfe hud'u da kamar minti
ashirin, Aysha tare da k'awarta
mai suna Baby Labo, suka yi
parking motarsu gaban faculty
of medicine & surgery. Baby ce
ta fara fitowa kasancewar ita ta
san kan makarantar, saboda
anan take masters dinta, itace
kuma ta binciko cewar Deedo
tana da exams yau, da misalin
k'arfe biyu zuwa biyar na
yamma.
Bayan Nawap ya dan huta, ya
tashi yayi sallan la'asar,
sannan ya shirya, ya zari key
din motarshi, ya fito. Wurin
Ummi ya k'arasa yace zai je ya
d'auko Deedo ba sai driver ya
je ba. Allah ya kiyaye Ummi tai
mashi, sannan ya sa kai ya
wuce, zuciyarshi duk a dagule,
ya rasa abinda yake mashi
dadi..
Kasancewar basu da nisa
sosai yasa ya isa wurin da
misalin k'arfe biyar saura
kwata. Gefe guda yayi parking
ta inda zai iya hango duk wani
mai shiga da mai fita a harabar
wurin.
Cikin jin dad'i Deedo ta fito
daga exam hall tana ta faman
fara'a, kasancewar ta rubuta
komai da aka tambayeta,
murmushi ta saki a lokacin da
ta hango abar k'aunarta
rungume da hannayen shi, a
gaban hall din yana jiran
k'arasowanta.
Wayarta dake cikin jakar
hannunta ta fara ruri, ta fito da
ita ta duba, Hally ce ta kira ta,
da sauri ta d'auka suka fara
gaisawa, tayi mata ya exams,
ta ansa da "lafia lau 'yan mata,
ya skool" "ina gida ma wlh,
kinsan an sa ranan bikina"
"amma baki da kirki, shine baki
fadi mun ba" "jiya ne fa aka sa,
kuma naga kina da exam yau,
shi yasa nace idan kin fito zan
kira na fada miki" murmushin
jin dadi Deedo tayi, tace
"Bauchi dai ta aureki kenan, ai
nasan dama baza ki bar
Mubarak din nan ya wuce ki
ba" duk suka sa dariya, tayi
mata fatan alkairi, sannan tace
"say hi to my boo" ta mik'awa
Affan wayar, ya ansa suka
gaisa, kasancewar ya san
labarinta tsab a bakin Deedo.
Ansar wayar tayi bayan sun
gama gaisawar, tace "zamuyi
waya anjima" "ke ban gane ba,
ina Ya Nawap din?" Hally ta
tambaya, "ke ki share, bakomai
fa tsakanin mu" "ni dai nafi son
ki da shi Deedo, wannan daga
ji ma dan yaro ne, irin chewing
gum guys din nan wallahi"
murmushi tayi, tace "zamuyi
waya anjima" ta kashe wayar ta
jefa a jaka, suka jera da Romeo
dinta, suna tafe suna firansu
abin gwanin ban sha'awa, sai
dai wanda ya gani.
Gaban faculty suka isa, saman
wasu kujeru suka zauna suna
ta zabga soyayyarsu, su Aysha
da suke gefe suna jiran
fitowarta ne suka hango kamar
ita, dan haka duk suka fito a
motar, a dai dai lokacin wani
abu yazo zai fada idon Deedo,
Affan yace ta rufe idonta ya
cire mata, hannunshi da ya sa
zai cire abun, yayi dai dai da
d'agowar Dr. Nawap ya kawo
kallonshi kan kujerun da suke.
Daaaaaaam! Yaji zuciyarshi ta
buga a lokaci guda, wani
bak'in kishi ne ya ya kai mashi
ziyara, yayin da a karon farko
yaji k'wanyarshi na shirin
d'inkewa! Da sauri ya fito, a
dai dai lokacin kuma su Aysha
suka k'arasa wurin inda Baby
tasa hannu ta finciko gashin
kan Deedo wanda ta daureshi a
baya, gyalen kanta ta fara
k'ok'arin warewa, amma Allah
ya bata sa'a ta rik'e shi gamda
hannunta. Affan yayi saurin
mik'awa yana fadin "what the
hell are you doing? Ke
wacece?" Isowar Nawap yayi
dai dai da shiga hankalin kowa
da yake wurin in banda Affan
wanda bai taba ganinshi ba,
bai kuma san daga ina yake
ba.
Deedo dake lab'e bayan Affan
tana raba idanuwa tuni tayi
saurin fitowa, ganin Idanun
Nawap sun sauya kala daga
fari zuwa jaa, ta san cewar yau
k'aryarta ta gama k'arewa.
Hannunta ya finciko tun
k'arfinshi ba tare da ya cewa
kowa komai ba, shima Affan
bai yi k'asa a gwiwa ba yasa
hannu cikin izza yana jawota
daga hannun Dr. Nawap!…
Chapter 26 · 0% Book details