← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 36

Sashe 35

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read

BA’A SHAN
ZUMA…
109-111
BA'A SHAN ZUMA… 109
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Hawaye masu azabar zafi suka
gangaro a fuskar Deedo ganin
halin da kanwar mahaifinta ke
ciki. Hannu tasa ta share, ta
juya tana kallon Nawap wanda
yake goge bakinsa da
handkerchief, karasawa tayi,
gabanshi
"Sannu Yaa Nawap" ta fada
yayin da take waige waige ko
me take nema,
"Kaje waje, bari nayi magana
da ita"
Goggo wadda ta rarrafo ta turo
kanta kofar dakin, tace
"Wai muryar su waye nake
ji nan? Iyii? Ko baza kuyi
magana bane tambadaddu
ya'yan fata, Allah dai ya tsi… "
Nawap ya katseta ta hanyar
cewa,
"Goggo Nawap ne, wannan
kuma Deedo ce, dago ki ganta"
"Deedo? Nawabu? Ku ne? Ko
dai tsinannun ya'yan unguwa
ne suke tsokanata"
Ta fada yayin da ta dago kanta,
ko Allah zai sa ta hango
kyallin wani abu wanda zai
tabbatar mata da cewar su din
ne.
A tare suka toshe bakinsu da
hannu, suna fadin
"innalillahi wa inna ilaihir
raji'un!
Goggo!"
Ganin kwantsa mai kama
da mugunya, har da wasu yan
tsutsotsi suna fita daga idanun
Goggo, idon ya ca6e, ya
cakwale, Allah kadai ya san iya
shekarun da ta dauka tana tare
da wannan azabar.
Lalube ta cigaba da yi, inda
ta jawo 'yar k'afarta guda daya
da tayi mata saura, ta fito da
ita wajen dakin dak'yar,
"'Ya'yan nan ku fada mun
gaskia, Deedo ce wannan a
gaba na da gaske?"
Tasa hannu tana lalube ko
zata samu damar ta6a Deedon.
"Nice Goggo, wai me yake
faruwa da ke ne? Bakya gani
ne ko ya akayi?"
Kuka mai sauti Goggo ta
saki, sai dai kash, kukan babu
ko alamar hawaye, amma duk
wanda ya ganta zai tabbatar
kukan nadama Goggo take
rerawa.
"alhakinku ne yake bibiyata
Deedo, dake da malam Ilu,
wanda bakin cikina yayi
sanadiyyar barin shi duniya, na
shiga ukku ni Batula,"
Abinda Goggo take nanatawa
kenan, yayin da ta dauki
hamnuwanta ta dora bisa kai,
tana kurma ihu kamar
mahaukaciya.
Ihun da Goggo ta kurma,
shi ya jawo hankalin su Hafsat,
da Mal. Labarin makwabcin
Goggo wanda shi kadai ne
mutumen da ya rage wanda ke
taimaka mata a unguwar,
kasancewar kowa ya san bakin
hali da bala'i irin na Goggo,
shi yasa babu mai kallon inda
take, anan inda take a zaune
zata yi kashin ta da fitsari,
haka kuma idan malam
Labaran ya miko mata dan
abinci, anan din dai zata cinye
shi, ba tare da wanke hannu ko
kashin da yake jikinta ba.
Da azama suka yo cikin gidan,
ganin yanayin yadda wurin
yake yasa Hafsat dakatawa,
hannunta rik'e da na Mahmoud,
yayin da Mal. Labaran ya
karasa yana fadin
"Samari daga ina? Lafiya
kuwa?"
"Lafiya lau mal., ina wuni"
Cewar Deedo, inda shi kuma ya
cigaba da kare mata kallo
kamar ya santa.
"Deedo ce" ta fada tana kallon
goggo,
Nan ya fara salati yana
sallallami
"Deedo? Ina kika shiga?
Wanene wannan din shi
kuma?"
Anan suka gaisa da Nawap, yai
mashi bayanin kanshi, mal. Ya
kara da tambayar "kai kuma ina
ka santa?"
Nawap wanda baiyi kasa a
gwiwa ba ya labartawa mal.
Yadda akai ya san Deedo, har
ma da yadda akai ya tafi da ita.
Goggo wadda ta daskare tun
lokacin data tabbatar da Deedo
din dai ce a wurin, ta kara
kurma wani sabon ihun, a
yayin da Mal. Labaran ya
kwashi sabon salati yace
"Eh lallai dole kike shiga
wannan halin Batula, ka ganta
nan" ya fada yana kallon
Nawap tare da nuna Goggo da
yatsa, yace
"Wannan matar bayan tafiyar
Deedo, duk wanda ya
tambayeta ina yarinyar nan
take, ce mashi take ta tafi
yawan karuwanci, ashe ke da
hannunki kika dauki diya kika
bayar, chabdi! Lallai Allah yana
son ki Batula, tunda har ya
baki damar sake ganin Deedo
don neman gafararta"
Cigaba da jinjina kai yayi, ko
a film bai taba jin irin wannan
tsantsan rashin imanin na
Goggo Batula ba.
[26/04 01:21] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 110
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Deedo wadda take shar6ar
kuka domin jin bayanin mal.
Labaran nan da nan taji wata
sabuwar tsanar Goggo ta karyo
mata, ba don kanwar ubanta
bace, da babu wani abu da zai
kara hada su, duk uwar azabar
da ta gana mata bata isheta
ba, har sai da ta zubar mata da
duk wani mutuncinta daga idon
mutanen garin.
Nawap ne ya lallabata har tayi
shiru, sannan ya kai dubansa
ga mal. Labaran wanda har
yanzu bai daina mamakin
makirci da mugun hali irin na
Goggo ba,
"Mal. To ita menene
musabbabin dawowarta haka?
Ina yaranta suke ne basu kula
da ita?"
"Chabdi! Dogon labari
kenan,"
Cewar mal. Labaran, sannan ya
cigaba
"Abinda yayi sanadin
dawowarta haka baya rasa
nasaba da dan ta shehu,
wanda tun yana dan shekara
sha biyar ya zama tataccen
dan daba, inda ya shiga wata
kungiya ta wasu mutane masu
yanka mutun su gudu. Haka ta
faru da shi bayan ya soka ma
wani yaro wuka a ciki, ya gudu
ya bar garin, yan sanda suka
nemeshi suka rasa, har suka
kame ita Batular, inda wani
bawan Allah da bata san ko
wanene ba yayi belin dinta, to
bayan an sako ta daga caji ofis
din ne ta taho gida mota tayi
ciki da ita, wanda hakan yayi
sanadiyyar rasa kafarta guda ta
dama"
Mal. Labaran ya dan
tsagaita, sannan ya dora,
"To ita kuma waccen Hadizar,
babbar 'yar tata kenan, da tana
kula da ita, daga k'arshe sai
abin ya dawo kamar ta dan
samu ta6in hankali, kullun in
banda kuka da kiran shehu
bata da wani aiki, nan zata yi
kashi, tayi fitsari, bata iya
motsawa ko kadan, ana haka
duk Hadizar na taimaka mata,
kwastam, sai aka wayi gari aka
ga Hadiza da katon ciki wanda
babu wanda ya san inda ta yo
shi, kuma ita dai ba aure akai
mata ba, nan fa yaran unguwa
suka dinga jifarta, suna
zaginta, itama daga nan aka
nemeta aka rasa. To ni dai a
ganina kukan rashin ya'yanta,
da kuma iftila"in da ta jefa
mutane, shine yayi sanadiyyar
rasa ganinta, ana haka kowa ya
watse babu ko wanda yake
kallonta, sai fa ni din nan, nima
dan dai kawai in sauke hakkin
makwabtaka, amma in ba haka
ba, babu abinda zai sa na kalli
mai mummunan hali irin na
wannan matar"
Ya karasa maganar, yana
mai nuna ta da yatsarsa.
"Hasbunallahu wa ni'imal
wakil"
Shine abinda Nawap yake
maimaitawa, yayin da yayi
saurin dauke idonsa akan
Goggo, wadda yake jin kamar
ya shaketa ya hada da bango
ta mutu kowa ma ya huta.
"Sai ki nemi yafiyar yarinyar
nan, tunda Allah ya taimaka
miki gata a gabanki a karo na
biyu"
Cewar mal. Labaran kenan
yayin da yake kallon Goggo.
"Na yafe mata ni kam, mal.
Ko yadda Allah ya mayar da ita
ai ya isa ishara gareta, da duk
wani mai hali irin nata, fatan
dai Allah ya yafe mana baki
daya"
Deedo ce take wannan jawabin
a lokacin da take share kwallan
idanunta.
"Amen" duk jama'ar wurin
suka ansa da.
Goggo dai banda wasu
surutai, da wasu yan bige bige
kamar wadda sauro ke cizo
babu abinda takeyi, sai kuma
lokaci zuwa lokaci kaji ta
kurma wani gagarumin ihu,
babu Allah, bare kuma salatin
annabi a bakinta.
Kofar gidan suka fito gaba
dayan su, in banda ita da bata
iya takawa sai dai
rarrafe.
Gaban mota Nawap ya
bude, ya fito da kudi wanda
bansan adadinsu ba, mik'awa
mal. Labaran yayi,
"A taimaka a gyara mata
ginin nan da ya rufta, sannan a
dinga sai mata abinci, inda hali
a samu wanda zai rinka
tsabtacce mata wurin, ni zan
rinka biya in har an samu
wanda zaiyi hakan, mun gode
mal., Allah ya kara girma, ya
kuma baku ladar abinda kuka
yi"
"Amin" ya fada, sannan
sukayi musayar number shi da
Nawap, ya wuce zuwa cikin
gidan shi, inda shi kuma ya kai
kallonsa ga su Deedo da sukai
jugum,
"Sai ku shiga mu wuce"
Babu gardama, duk suka
shige suka dau hanyar
komawa.
Sai da suka shiga Bauchi
sannan suka tsaya, domin
neman abinda zasu ci, anan
Deedo ta kira hally, tai mata
kwatacen gidanta suka je, nan
ta tarar da ita har da dan
yaronta mai shekara daya da
rabi, suna cikin fira take shaida
mata halin da Goggo take ciki,
addu'a dai sukai mata, inda
daga bisani ta fada mata
bikinsu kwana goma masu
zuwa. Hally kuma tai mata
alkawarin zuwa in har Allah
mai kowa mai komai ya bata
iko, sukayi sallama, sannan
suka dau hanyar Kaduna.
[26/04 02:05] Nty Lubiee:
BA'A SHAN ZUMA… 111
NA LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
®NWA
Har suka iso gida firar da suke
ta irin mutane masu halayya
irinta Goggo ce, Hafsat wadda
abin ya zama sabo a wurinta
tace
"Allah kenan, buwayi gagara
misali, yanzu ji yadda matar
nan ta dawo, ko duniyar da
take ma hadama ta juya mata
baya, suma ya'yan da ta
musguna ma wasu saboda su
sun gudu sun barta, kai Allah
dai ya sa mu cika da kyau da
imani,"
"Amen" suka ansa da shi,
lokacin da suka iso kofar
gidan, ana ta faman kwalla
kiran sallar maghriba.
* *******
Kwana ukku da dawowarsu,
su Ummi suka dawo, inda tayo
siyayya ta ban mamaki, sun
hado mata lefe dai dai
gwargwado, babu karya, babu
kuma karanta a ciki, sai dai
san barka, haka kayayyakin
daki ma sun siyo dai dai
iyawarsu, inda suka karasa
siyen sauran anan gida
Nigeria.
Bayan Ummi ta natsu, ta
huta duk hankalin kowa ya
dawo jikinshi, anan take
tambayar Deedo yadda akai
bata je Ningin ba, ta kara da
cewar
"Ba dai mutumin can ne ya
hure maki kunne ba?"
Ta fada tana kallon Nawap,
Murmushi Deedo tayi, tace "ko
daya Ummi, munje ai"
Nan ta labarta duk abinda ya
faru, bata rage komai ba,
Salati Ummi tayi, sannan ta
kara da "Allah kasa my gama
da duniya lafia"
Suka ansa da amin gaba dayan
su, inda suka d'auko wata firar,
wadda yawanci duk labarin
yadda za'a tsara bikin ne suke.
Biki dai sai matsowa yake,
inda yau rage kwana hud'u a
fara. Kasancewar Deedo bata
da tarkacen kawaye, hakan ya
bata damar kammala duk wani
rabon invitation da zata yi,
wanda dama duk course mates
dinta ne ta gayyato, sai fa yan
mutanen da baza a rasa ba,
wanda suke gaisawa a
makaranta.
Hakan ya bata damar
natsuwa wuri guda, tana
daukar gyara a wurin matar da
Ummi ta dauko takanas, daga
Niger republic. Haka Hafsat ma
ba a barta a baya ba, itama da
nata sinadarin gyaran na
daban, wanda ya kasance
tsakanin ta da Deedo ne, sirrin
kissa da kisisina, da iya rik'e
miji kawai take dora mata,
yayin da Deedo take kwashe su
a kwakwalwarta kamar tana
rubutawa. Domin ko zamanin
nan dai sai da kissar, amma
sai kaga mace a harbutse, ko
magana bata iya ba, sai kuma
idan mijin ta ya kyallo wata
abun ya zama bala'i, a daure a
koyi sirrikan mazan aure
yanuwana.
Rana bata karya, wai sai dai
uwar diya taji kunya! Inji
Hausawa. Haka aka fara bikin
Deedo da Yaa Nawap dinta,
amarya sai kyalli take tasha
dilka, tayi kyau har ta koshi da
shi.
Daga su sai su suke bikin
nasu, dangin Maman ta ne, sai
kuma dangin baban su Nawap,
sai 'yan gayun kawayenta
wanda duka duka basu wuce
mutun sha biyar ba, biki ne
suke hankali kwance ba tare da
hayaniya ba, babu wata bidi"a,
illa kyakkyawar dinner da za
suyi a gobe, sai kuma daurin
aure.
Amarya ce ta fito cikin light
brown din gown mai asalin
kyau, wadda ta dace da kirar
jikinta, yayin da KHADY'S
MAQUILLAGE ta gwangwaje ta
tsararran make up mai daukar
hankali. Tayi kyau dai dai
misali, haka angon ya fito a
cikin danyar farar shaddar
Sheraton, wadda taji lafiyayyan
aiki da light brown din zare,
hularshi da takalmansa, gami
da agogonsa duk light brown
din, sunyi kyau kamar a sace.
Bayan sun shigo hall din Kabir
Gymnasium, inda ya kasance
can ne aka tanada domin
gabatar da dinner, nan fa aka
fara sakin flash, masu video
coverage suma suka cigaba da
dauka, yayin da zaka hango
farin cikin da yake kwance a
fuskar Ummi domin ganin
wannan kyakkyawar rana.
Haka aka cigaba da
rakashewa, ana gwangwajewa
yadda ya kamata, har aka gama
lafia, kowa ya kama gabansa.
Washe gari da misalin k'arfe
1 na rana aka Daura auren Dr.
NAWAP KHAMIS, & FIRDAUSI
KABIR SANI, akan sadaki mafi
daraja, wanda ya ta'allak'a
akan koyarwa ta ma'aiki
(S.A.W).
Bayan daura auren da
misalin karfe shidda na yamma
aka dauki amarya sai gidanta
dake Sultan Road. Komai ya ji,
babu abinda Ummi bata yi ba,
sai kuma fatan zuri'a mai
albarka.
Kwanansu biyu a Kd, sannan
suka tattara suka wuce Abuja,
kasancewar hutun da Nawap
ya dauka ya kare. Rayuwarsu
abin sha'awa, soyayya suke ta
ban mamaki, kowa kokari yake
yaga ya faranta ran dan
uwanshi, dan haka suke zama
na jin dadi da salama.
Satinsu biyu a Abuja su
deedo suka koma hutu, bata da
yadda zata yi, dole ta dawo Kd,
da sabuwar Mercedes-AMG
dinta wadda Nawap ya bata
tukwicin amarci.
Chapter 35 · 0% Book details