← Book details Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 36

Sashe 1

Baa Shan Zuma Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

BA’A SHAN
ZUMA… 01
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
Kwance take tsakiyar wani dan
karamin daki mai mugun bakin
duhu, babu komai a cikin dakin
sai yar tabarmar kabar da take
kwance akai, ga wani irin sanyi
ana yi, mai masifar buji, ta
takure wuri guda, ta lullube
kafafuwan ta da dankwalin ta,
hannuwan ta ko ta hada su ta
cusa tsakanin cinyoyin ta,
domin kuwa ko arzikin zanin
da zata rufa bata dashi. Bata
da banbanci da prisonern da
aka yankewa hukuncin daurin
rai da rai! Wasu irin hawaye
masu zafi ne suke sintiri akan
kyakkaywar fuskar ta, tunani
take ena rayuwarta ta dosa?
Tun tana karama take shan
azaba a hannun goggo wadda
ta kasance kanwar mahaifi a
gare ta. Cikin muryar kuka take
cewa "anya kuwa goggo ta
hada jini da mahaifina kamar
yadda aka sanar dani?" Bata
karasa rufe bakin ta ba, taji an
banko kofar dakin tun karfi, ba
tare da bata lokaci ba matar
data shigo ta daga robar ruwan
dake hannun ta, ta juye ta tass
akan yarinyar, cikin tashin
hankali tayi zumbur ta mike,
tace "goggo dan Allah kiyi
hakuri, wlh ban san asuba tayi
ba" matar da aka kira da goggo
ta karaso gaban ta, ta jawo
gashin kanta tayi wurgi da ita
zuwa tsakar gida, tace "uban
mi kike nufi da baki san asuba
tayi ba?" tsinanniyar yarinya
kawai, mai hali irin na uwar ta,
wuce ga bargunan fitsarin
shehu can ki wanke su tass ki
shanya, sannan ki wuce ki dibo
mun ruwa tun kafin layi ya
cika" tana kai wa nan ta
hanbare ta da kafa, taja tsaki
sannan ta wuce.
Mikewa tayi jiki ba kwari, ga
wata irin rawar sanyi da take
yi, bargunan ta tattara, ta wuce
ta zuba su a ruwa, ta wanke ta
shanya, sannan tayi alwala,
taje ta gabatar da sallar asuba.
Tana sallamewa goggo ta dawo
dakin tace "sannu yar milki,
wato dan uban ki rainin da
kikai mun har ya kai na in maki
magana kiyi banza dani ko, yau
zaki gayawa yan garin ku" ba
tare da ta bar ta tace komai
ba, ta fara jibgar ta, ga kayan
jikin ta dama a jike, ga wani
irin muku mukun sanyi da ake
sararawa, amma babu tausayi,
ba imani goggo taci gaba da
kwalfarta har saida taji ta gaji,
sannan ta kyale ta, ta fito daga
dakin ta dauko wani Katon
baho, ta wurga mata, tace
"saura kuma in kin tafi ki
kwana a can, kizo kiga yadda
zan lallasa ki a gidan nan"
cikin kuka ta mike ta dauki
bahon ta wuce ta bar gidan…
Borehole ta nufa a lokacin
babu kowa saboda tsabar
sanyin da ake yi, ta tara bahon,
sannan ta fara buga famfon,
cikin yanayi na damuwa da
mugun tashin hankali, ga wata
irin kyarma da take yi, hakoran
ta sai gamewa suke suna wani
irin kara.
Ta cika bahon dam, dakyar ta
dauka, ta dora a kanta, sannan
ta dauko hanyar gida tana ta
uban sauri.

BA’A SHAN
ZUMA…. 02
NA
LUBABATU MAITAFSIR &
BENAXIR OMAR
A hanya ta fara ganin mutane
kadan kadan kasancewar, gari
ya fara haske. Gidan ta karasa,
taje ta aje ruwan, sannan ta
tattara wanke wanke, taje tayi,
ta gama ta share tsakar gidan,
duk su goggo ana daki ita da
ya'yan ta, ta leka dakin goggon
ta durkusa tace "na gama
goggo" ba tare da ta kalle ta
ba, ta dungura mata roba mai
kosai a ciki, ta mika mata kofin
kunu, ta ansa tayi godia,
sannan ta wuce dakin ta, ta
zauna ta cinye, ta jawo wasu
kodaddun uniform, ta burma ta
dauki jakan ta, ta wuce
makaranta. One thing da zai
birge ka a tare da Deedo shine
kokarin ta wurin karatu, bata
wasa dashi duk kuwa da
wahalar da take sha a gidan
goggo, domin kuwa babban
burin ta a rayuwa bayan ta
hardace Qur'ani, to shine ta
zama medical Dr. haka rayuwar
ta take tafia, bata da wani
'yanci balle kuma ayi maganar
gata.
WACECE DEEDO?
Asalin sunan ta Nana
Firdausi Kabeer Sani, yarinya
ce mai shekara 12 a dunia,
tana js2 a wata private skool,
wadda scholarship ne ta samu
daga Gov. Bauchi anan cikin
garin Ningi. Mahaifinta
haifaffen garin Ningi ne, ta
jihar Bauchi. Su biyu iyayen su
suka haifa daga shi sai qanwar
shi Batula wadda ake kira da
goggo. Goggo irin izgilallun
matan nan ne, masifaffu masu
ji da bala'i, irin mutanen nan
da idan suka dauki karan tsana
suka dora maka, sai kaji kamar
ka bar dunia saboda masifar
su. Tana da yara guda biyu,
Hadiza da Shehu, mijin ta
malam ilu, bata dauke shi
bakin komai ba, domin komai
ita take yiwa kanta, wannan
yasa suma yaran suka raina
uban nasu. Mahaifiyar Deedo
mai suna Rukayya,yar asalin
garin kafanchan ta jihar kaduna
ce. Yanayin aiki yasa
mahaifinta dawowa cikin garin
kaduna da zama, inda ya tare a
unguwar hayin banki. Su biyar
ne iyayen su suka haifa, kuma
duka mata. Akwai babbar yayar
su Fatima, sai Labeeba sai
umman deedo, sai Halima mai
no mata, sai kuma Aminatu yar
autar su wadda suke kira da
baby.
Riqon Deedo ya dawo hannun
goggo ta sanadiyyar hadarin
mota da iyayen ta suka yi, a
hanyar su ta zuwa Kd, inda ita
kuma Deedo a lokacin sun
barta wurin inna mahaifiyar
baban ta, saboda zuwa
makaranta, wanda a lokacin
duka duka bata fi shekara 5 ba
a dunia!!
Wannan tashin hankali shi ya
haifar wa yar tsohuwar da
ciwon zuciya, ga kuma
tausayin yar marainiyar
yarinyar da suka bari, hakan
yasa ta kwanta ciwo sosai,
inda daga bisani itama tace ga
garin Ku nan dan dama malam
mijin ta, ya dade da rasuwa.
Tun asalin auren umma da
Abban su Deedo, goggo take
fama da baqin ciki da takaicin
dalilin da yasa dan uwan nata
ya rakito umma, kwata kwata
bata son ta bata kaunar ta,
kasancewar kafin yayi auren
akwai kawar ta Badiyya data so
ya aura, sai dai kuma shi bai
yaba da halayen ta ba, hakan
ya haifar da rikici a tsakanin
su, inda daga karshe ta yanke
shawarar fita harkar shi tare da
matar shi, sanadiyyar tsanar da
take yima mahaifiyar Deedo
kuma ita ce ta shafe ta har ya
kai ga ko ganin yarinyar bata
son yi kamar ba jinin ta.
Bayan inna ta rasu, yan
tsiraran yan uwan da suka rage
masu, suka yanke shawarar
goggo ta dauki Deedo ta riqe,
amma fur matar nan ta rufe ido
tace babu dalilin da zai sa ta
hada kanta da mugun iri, tace
"wani a cikin ku ya rike ta
mana, in kuma baku iyawa sai
ku kaita gidan marayu" ta mike
tayi tafiyar ta. Haka akai ta
fama da goggo, inda daga
bisani dai aka samu aka
lallaba ta, ta dauke ta, a cikin
zuciyar ta tace "ko bakomai na
samu yar bauta" haka ta tusa
keyar Deedo gaba, ta mayar da
ita gidan ta. Tun daga wannan
rana kuma Deedo tayi sallama
da duk wani farin ciki na dunia,
daga nan ta fara fuskantar
tsananin rayuwa, dan tun tana
karama take kwana a wannan
dan daki mai kama da keji, Dan
kuwa bata da ikon da zata
matsa kusa da Hadiza, wadda
suke kusan sa'anni, balle har
ta samu damar hada shimfida
da ita.
Chapter 1 · 0% Book details