← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 36

Sashe 9

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

"DIJA zo mu gudu" da fulatanci,baiji abinda suka fada ba sai gani yayi sun ruga a guje sun bar shi a tsaye a wajen da kudi a hannu. Kasa rike dariyarsa yayi yana dariya harya shiga motarsa..

Washegari da safe yayi shirin fita office yau da wuri tun 7:30 ya gama shirinsa dukda sai 9 yake zuwa office.

Cikin irin uncompleted building din nan,DIJA na zaune a gefe kan irin buhun simintin nn sai DADA da Babanta daga gefe suma kan irin buhun ama yafi nata girma.Koko sukesha da kosai kasancewar da sassafe suke karyawa kafin kowannensu ya kama gabansa sai ganin KING sukayi akansu

Murza idonta Dada tayi tagwalalo dan son tabbatarda da gaske ka'don dasuka gani jiya ne taqara murza Ido wai a tunaninta gizo yake mata saboda sun kwana da tsoro da firgicin haduwa dashi aekuwa ya sakar mata murmushi danta tabbatar shidinne kawai saita qurma ihu tareda da fadin

"shikenan,hande min bone ya tabbata mun mutu mun mutu wlhy dija, ya'akayi yasan gidanmu dan Allah kado kayi haquri tunda bamu amsha kudinki.Ka kyalemin kan yarinyata,wollah aradun Allah ita kadai muka dasi"

Jin sumbatun Dada da yanda ta firgice yasa DIJA kallon direction din da Dada ke kallo don ta juya masa baya ne,suna Ido biyu dashi kua take kokon datakesha ya kwareta nan ta hau tari kamar zata shide ganin tarin dija bana qare bane yasa King komawa daga baya saigashi da bottle water ya bude ya kafa Mata abaki saida ta shanye tasss ya kamata ya zaunar idon nan nata yakada yayi jajir dashi tsabar azabar da tasha na tari dukda a tsorace take dashi tunda Dada tace mata dan yankan Kaine ama data kwanta bacci saida tayi mafarkinsa,har lokacin fa Dada bata dena kuka ba shikuwa wani tsamurarren mutum dana gani da rawani fari akansa amma zaku dauka ruwan toka ce tsabar datti shigarsu ta buzaye ne ajikinsa qafar wando daya ta yage tundaga gwiwa har idon sawu dayar kuwa kamar wanda akasa qusa aka daddatsa ta.

Daga kai king yayi ya kalli inda wadannan bayin Allah ke zaune kuma ga dukkan alamo anan suke rayuwarsu,wajene mai matuqar hadari a wannan zamani namu domin ko wannan er tsohuwar marasa tsoron Allah saisu Mata fyade balle gasu da yarinya dirarra don DIJA irin emmatan nn ne masu cikar halita mai daukar hankali ga kuma kayansu da koh mayafi bbu.

Karewa gurin kallon tsaff yayi kamin ya juyo da kallonsa kan Dada da keta yare da alama bawa wannan tsohon labarin abinda yafaru ajiya take Abu daya ya fahimta tsohon dayaji tana kira da babaji ya fisu nutsuwa dan haka ya qarasa garesa tareda mishi sallama ya mi'ka masa hannu yana 'kara fadada murmushinsa su Dada kua sun cure waje daya suna karkarwa.

Kama hannun King Babaji yayi da hannunsa biyu² suka gaisa don gani daya yayiwa King yasan shirmen matarsa da yarsa ne na kira wnn kamilin mutumin da dan yankan kai, nan KING ya fadamasa sunansa tareda gabatar masa da kansa da bukatarsa garesu shidai tsohon gyada kai yakeyi saida King ya gama sannan ya juya ya kalli dadaji da yare yamata bayanin abinda king ya fada da alama tasa hausar tafi tasu dada dadinji da kuma fahimta nan dai Dada ta nutsu Dija kuwa sai zare ido take daga gefe ta nutsu kamar shege akwali dan tun ajiyan tagama tsorota da king saboda Dada taita fadar yanda en yankan kai suke

King sallama yayiwa Babaji tareda fiddo kudi wanda bai kai na jiya ba dan yaga alama su dumus a wurin mutum dayane basa so sunfiso suyita yawo kwararo kwararo har sutara miwawa yace

"Ga wanna kuyi amfani dashi kamin anjima zan dawo muyi magana mai muhimmanci"

Ya fada tareda jaddada rokonsa akan su dena fita bara, Babaji yaso yaqi karba amma sayyaji zuciyarsa ta aminta da king shiyasa ya karba tareda addua da godiya. Sallama yayiwa Dada da bata gama sakin jiki ba tace

"Sai da shafe ka'do"

dariya ma abin ya basa wacce safiya kuma banda wacce suke ciki a yanzu juyawa yayi yayiwa dija kallon Ido cikin Ido sannan ya sakar mata murmushi mai burgewa kana yafita a kangon da wannan murmushin a fuskarsa yana kara jin nishadi da wani irin nutsuwa a ransa tareda wani irin bakon yanayi a jikinsa,sai sabga murmushi yake shi kadai yana driving wani nishadi yakeji sai shafa sumar kansa yake da hannu daya,dayan kuma yana driving.

Wayarsa ya juna da radio motarsa yasa wakar Right next to you na Chris brown da JB yana bin wakar cikin shauki...

U got the smile that only heaven can make,I pray to God evrday that u keep the smile............💃🏻💃🏻💃🏻

_THE MOST ROMANTIC PART_🥰 _muje zuwa TEAM KING AND DIJAH_

COMMENTS AND SHARE FISABILLAH 🥰🥰🥰
[1/6, 9:01 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

BY APHSERTEEN KHAIREE

ELEGANT ONLINE WRITERS

11

Harya shiga ma'aikatar tasu ta Ministry of foreign affairs fara'ar fuskarsa bata gushe ba,dukda en office dinsu daman sun san KING da san jama'a ga fara'a kowa nasa ne ama duk wanda ya gansa yau zai san lalle yana cikin nishadi.Rabin hankalinsa na kan aiki rabi na wajen tunaninsu DIJA da iyayenta da plans dinsa na son chanza rayuwarsu tare da ingantata,har lokacin tashi yayi ya tattara kayayyakinsa ya dau hanya.

Ya karaso kangonsu DIJAH da fatan Allah yasa basu fita ba yau kamar yanda ya rokesu,yaji dadi sosai ganinsu a zaune waje daya basu tafi kara'de gari ba har BABAJI ma yana nan yana tsumayin jiran dawowar KING.Dija na kwance kan cinyar Dada tana tufke mata yalwataccen gashinta mai santsi dukda datti ya chanza masa kala don bazaka iya tantance a tsefe yake koh da kitso ba gashi nn ne de.Da sallama ya shigo wajen hannunsa cikin wandon jeans dake jikinsa,da fara'a Babaji ya amsa tareda mikewa ya iso inda King yake zuwa yanxu hankalin Dija ya soma kwantawa da King don itama tunda ya tafi take ta Allah² BODDO (sunan da tasa mishi a ranta knn,ma'ana kyakkyawa) ya dawo ta sake ganinsa don ba karamin kyau da burgeta yake ba tunda suka shigo garin ma ita bataga wanda ya burgeta sosai kamarshi ba.Bayan sun gama gaisawa harda Dada da har lokacin bata gama sakewa dashi ba BABAJI ya shimfida masu buhu a kasa King ya zauna ba tareda damuwa da k'uran wajen ba,Babaji ma ya zauna daga gefensa ama a k'asa.

"Baba koh zan iya sanin labarinku,ma'ana daga ina kuke sannan meyasa kuke zaune anan kuma ka bari iyalinka suna bara?"

Ajiyar zuciya Babaji yayi har ransa yaji King ya kwanta masa dukda bai sanshi ba,duk irin zurfin ciki na Fulani saiya tsinci kansa da amsawa King din

"Mude asalinmu Fulanin Yola ne ama kasan mu Fulani akoi masu yawo gari² suna kiwon dabbobinsu in sun sami wani gari su d'an yada zango na kwana biyu snn su cigaba da tafiya toh muma hakane har Allah kaddara ta kad'o mu wani gari da ake yaki ana kashe² muma dakyar mukasha wai koh D'andugur naji mutanen da muka tsira tare suna fada"

Murmushi King yayi yace "kode Maiduguri koh?"

"Oho toh kila shine,toh ina fadamiki a haka shanayenmu gabadaya suka salwanta yoo wama yake ta shanu ana ta rai.A haka muna tafe muna hutawa gari²,Debbu da bingel am suna d'an bara muna samun abinda zamusi haka kuma in mun samu gini mara murfi kamar wannan da muke ciki sai mu dinga kwana,wani lokasin masu shi suna koremu haka² de har Allah ya kawo mu garin nn"

Cikin tsananin tausaya musu King ya girgiza kansa wato idan kaga rayuwar da wasu sukeyi saika k'ara gane cewa duniyar ba komai bace,gashi muna da shugabanni da Allah ya daurawa hakkin talakawansa kansu ya basu mulki da wadata don su tallafi rayuwar na kasa sai idonsu ya rufe kowanninsu burinsa ya gina kansa da iyalinsa kawai,son kai da zuciya ya yiwa shugabanni da wasu masu kudi k'atutu a rai.Basaji da ganin kowa sai kansu kawai shiyasa ta'addanci da sace² yayi yawa ga yawan mabarata ta koh ena,wani boyayye kuma ajiyayyen burinsa ne ya tashi yasan yana da wadatar da zai iya kuma wnn ne daidai lokaci da zanyi.

Tun kafin ya gama jami'a yake ganin abin al'ajabi ga rayuwarsa,koh naira biyar ya ajiye sai ta koma goma,tun abin na bashi mamaki harya koma bashi tsoro da al'ajabi.Tun da Babansa na raye bai tab'a barinsa yayi amfani da kudin da yake zaton aljanu ke ninka masa su ba har kawo yau da bayan rasuwar iyayensa lokaci daya abin ya k'ara yawaita don har cikin wardrobe dinsa inya bude sai yayi karo da kudade masu tarin yawa sai kawai yake tarasu a wani daki wataran ya k'ona don bai tab'a sha'awar amfani dasu ba.

Daya ga abin yay yawa ne yaje wajen wani malami yake fadamasa sai malamin ya bashi shawara da kawai ya dinga sadaqa da kudin shi kar yayi amfani dashi,yayi amfani da abinda yake hakkinsa kawai wanda yasan me yayi ya samesu ama yanxu ya yanke shawarar amfani dasu don cikar burinsa da manufarsa.

Kallon indasu Dija suke yayi snn ya mayarda idonsa kan Babaji yace

"Baba ina neman wata alfarma wajenka in babu damuwa zan daukeku Ku dawo gidana da zama don ni kadai ne daman,Allah ya yiwa iyayena rasuwa watannin baya da suka wuce"

Shiru Babaji yayi yana nazari maganansa,gashi de a zahiri ba shida siffar mutanen banza ama duniya ta lalace bazaka taba gane nagari da mugu ba don suma mugayen yanxu rikid'a suke cikin nagartattun suyi basaja suna ha'intar jama'a tareda zamba cikin aminci,cen ya numfasa yace

"Yaro na rokeki dou Allah kaji tsoron Allah karka shushemu,na yarda zamu bika amma ka rike amana"

Murmushi King yayi ya gyara zamansa cikin son k'ara tabbatar masa da kyakkyawar manufarsa akansu yace

"Ka kwantar da hankalinka Baba,Insha Allah bazaka taba samun matsala dani ba.Inaso ka daukeni tamkar d'a don nima tunda na ganka nakejin ka kamar mahaifina tunda na rasa iyayena nake cikin damuwa da kewa da rashin wani makusanci a kusa dani,yardarka kawai nake nema akaina"

Hankalin Babaji ya kwanta da yarda da kalaman King dari bisa dari

"Tho shiknn,Allah ya maka albarka ya taimaka maka wajen aiwatar da kyakkyawar manufarka"

"Ameen ya Rabbi Baba,nagode"

"Yawwa,kace sunanka Aliyu koh?"

"Ehh baba"
Chapter 9 · 0% Book details