← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 36

Sashe 4

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon daya King ya masa wanda ya sashi tashi ya bar parlor inya cigaba da zama zai iya kaimata mari don a kwullace yake da ita daman.

Kura mata ido King yayi kamar mai nazartar wani abu daga kukan nata ya qara mata tambaya

"I ask you for the last time,su waye suka saki?"

Dago idonta dake gaje² da hawaye cikin tsoro da rashin makama tayi,jikinta sai rawa yake da dunkule kafafunta akan kujera tace

"Ba kowa,bbu wanda ya sani don Allah ka barni na koma gida"

Cikin nuna rashin damuwa King ya mayda idonsa kan wayarsa zaiga Zaki ya shigo da alama kiransa yayi

"Take her back"

Tashi yayi ya haye sama ba tareda ya koma waiwayowa ba.Cikin tsawa Zaki yace mata ta tashi,jikinta na rawa ta tashi tabi bayansa har wajen motocin dake gida..

Suna zuwa kofar gidanta gurds dinda ke zaune tareda ita a bayan motar ya bude ya cillata kamar er tsana sukaja motarsu suka barta awajen

Er qara tasa sbd zapin da taji dakyar ta tashi tana kuka hamnunta dukya kurje ta shige gida,bedroom dinta ta wuce direct tana kuka kamar ranta zai fita,A bakin kofar dakin taci karo da handbag dinta da key motarta data dauko dazu da zumar tafiya aiki

Har zata shige dakin tayi wayarta na vibrate a cikin jaga,Private number ta gani tana dagawa aka cemata

"Ki bude WhatsApp dinki mun ajiye miki aikinki na wanda yake daidai da ran mahaifiyarki in bakiyi abinda ya kamata ba"

Kitt aka kashe wayar,hannunta na rawa da shiga WhatsApp inda taga tarin messages duk yawanci tambaya ake mata akan tambayar da tayiwa King jiya a airport har ta iso kan wanda take kyautata zaton shine nasu

Wani ihu tasa ganin sakon nasu, cikin razana batasan lokacin data cillar da wayar ba jikinta na rawa,ta durgushe a wajen tana wani irin kuka da mai cikeda tausayi..

More comments more typing guys 😎

Share fisabillah 🙏🏻
[1/6, 8:59 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

BY APHSERTEEN KHAIREE

ELEGANT ONLINE WRITERS

5

KING

Yana shiga bedroom dinsa ya bude wardrobe ya dauko wani 'katon album mai kamar diary,before then he loves to captured every moments. Yanason taking pictures ya ajiyesu cikin wannan album din tareda short note akan kowanni picture,dukda ya taso yaga taking pictures a matsayin sana'ar mahaifinsa don har babban studio ne dashi ama shi ya dauki daukar photo one of his best hubby yana son abin sosai shiyasa ko ina zaije cameran sa na gefe koh akan hanya yaci karo da abinda ya mishi kyau sai ya dauka.

_*ALIYU MOHAMMED GIWA*_ Shine farkon abinda ke rubuce cikin album din wanda ya kasance asalin sunan shi daga baya KING ya boye sunan kowa yafi saninsa da KING.

Picture din farko dake cikin album din ya kalla,tareda shafawa cikin tsananin damuwa da kewar iyayensa lokacin yana jariri akayi photon shida Amminsa da Baban sa ya riko kafadarta suna kallo kyakkyawar fuskar jaririn nasu dauke da murmushi akayi capturing wanda pic din ya kasance black and White.

Cigaba da bude kowanne pages ya dingayi yana murmushi shi kadai har yazo kan wani wanda ya tsaya ya kura masa ido sosai yana kallo

Irin _*BARAROJIN*_ nan ne Uwa da erta akan titi,yarinyar bazata wuce 16yrs ba cikin shigarsu ta asalin fulani da buhunsu a rataye a hannunsu kamar jaka ya daukesu sai zabga murmushi suke wanda kana ganinsu zaka iya karantar tsantsar jindadi da farinciki dake fuskarsu

Shafa fuskar er yayi idonsa ya kada yay jaa atake,ya yamutsa fuskarsa kamar mai son yin kuka yace

"I really missed you my FULANI, please come back to me"

Tuna ranar da ya fara haduwa da ita yayi,cikin traffic yana jira a basu hannu su wuce da yamma lokacin ya tashi daga office zaije gida

Ta mirror glass din motarsa ya hangosu itada mamarta da take kira DADA yaga suna bin mota mota,yanda sukeyi da fuskarsu in sun bar gaban kowanne mota ne ya bashi dariya dukda baisan me suke fadaba ama daga gani yasan rashin kunya sukewa mutanen cikin motar har suka karaso tashi motar.

"Muna bara muna karuwa"

Cikin mamaki da bazata yaji muryar uwar da abinda take fada,dariyace ta subuce mishi ya kalli uwar da er da kyau

Gashi de uwar ta manyata,er kuma bazata wuce 15 to16 ba.Toh waye yake karuwar acikinsu,su kuma nasu salon baran kenan?

No wonder shiyasa suke barin sauran motocin a tsiwace,horn da aketa faman zabga mishi daga bayansa ne ya sanyashi tunawa da inda yake alamar an bada hannu tuntuni kenan har en bayansa sun fara fusata

Harya wuce kuma sai wata zuciyar ta sashi zagayowa ya dawo wajen wannan bararojin yaci sa'a kuwa suna tsaye daga bakin titi basu tafi ba.Waje ya samu yay parking ya fito har inda suke

"Sannu" yace musu

Uwarce ta amsa mishi da fulatanci wanda shi baimaji abinda tace ba,sai ya kara tambayarsu

"Mesa kuke bara ahaka?"

Itade er sai binsa kawai take da ido irin kallon burgewa din nan take ta mishi sai uwarce ta kara bashi amsa cikin gurbatacciyar hausarta da ake ganewa dakyar tace

"Ka'don (hausawa) binni kunfi son karuwa shiyasa muke hadawa duka biyu ama duk shegun wai sede an basu DIJA ta tai musu karuwa ni bashasho ni kuma wollah bani bada DIJA tayi karuwa,GAR'KO (Miji) mai cheu zan nema mata tayi aure.Kaina in karuwa kakeso saide ka shii ni tunda ni mijini ya tsufa"

Tunda ta fara KING yake gimtse dariyarsa bayaso yayi karya katseta har seda ta gama tukunna yace

"Zaki bani DIJA na aureta?" Da murmushi a fuskarsa yake kallon DIJA data kureshi da ido dukda ita bamajin mai suke fada shida DADAn nata takeyi ba ama kawai mutumin ya burgeta ne sosai har bata gajiya da kallonsa

Wani dadine ya cika Dada cikeda murnar jin wnn dan gayen binnin yace zai auri DIJANTA da fulatanci take cewa dijan ta samu miji wannan yace zai aureta take nunamata shi sai kuwa itama Dija ta hau murna yace zai aureta shide kawai kallonsu yake cikeda mamakin murnar da suke daga haduwa da mutum lokaci daya bakasan wanene ba bakasan irinsa ba lalle sai yanxu ya kara gaskata zancen mutane da suke fadar wautar Fulani shi da ya dauka duk sharrine kawai ake musu.

Ce musu yayi su tsaya yana zuwa,binsa sukayi da kallo har yaje motarsa ya dauko cameransa ya dawo kusada su ya sasu tsayawa da kyau suna zabga murmushi yayi snapping dinsu.

Zo kuga murna daya nuna musu kansu acikin camera...

Wata er karamar dariya CE ta subuce masa tunawa da dramarsu ta farkon haduwarsu da DIJAnsa,Fulaninsa,abar kaunarsa wacce ya bawa dukkan soyayyarsa da gangar jikinsa gabadaya.Ya wahala,ansha drama kala²,wauta,da shirme iri² kafin DIJA ta zama cikakkiyar mace kamilalliya.An rabasa da DIJA a lokacinda ya fara jindadi da girbar wahalarsa akanta,a lokacinda yafi muradinta da kasancewarsu tare

Wasu irin kwalla masu zafi ne suka zubo mishi wanda radadinsu ke fitowa deep inside his heart,kiran sallar azahar da aka farane ya fargar dashi da irin time din daya bata a zaune daga kasan bed dinsa kan lallausar rug din dake shimfide a wajen.Tashi yayi ya shige toilet ya dauro alwala ya fita a dakin cikin sauri....

_GOV'T HOUSE_

Ba tareda damuwa da P.A dinsa dake wajen ba ZEE ta karaso daidai wuyan AA KAITA ta baya tasa hannyenta ta dago habarsa tareda daura fuskarta kan nashi ta soma aika mishi da wani lafiyayyen kiss wanda ya kashewa AA kaita jiki,Zee zata haukata shi da salonta kala kala da baya karewa shiyasa yake bala'in kaunarta.

Dauke kansa P.A yayi don take wani abu ya tokareshi a wuya sbd wani tsantsar kishi daya taso mishi,yana takaicin halin first lady da bata kunyar yiwa Excellency abu a gabanshi ama zaiyi maganinta ne.Ya fada a zuciyarsa tareda jan wani tsaki mara sauti

Saida ta tabbatar AA kaita ya harbu da kyau don har tana iya hango yanda ****** ya mike,wani murmushin mugunta tayi koh ba komai itama ta rama abinda ya mata jiya

"Morning my Excellency"

Ta fada bayan ta nemi kujerar dake kusada shi
ta zauna don hadawa kanta tea,shi kuma AA ji yayi abincin ma ya fice masa arai ya mike kawai ba tareda ya amsata ba.Sai lokacin P.A ya gaisheta

Cikin wani salo,ta aika mishi wani irin kallo mai tarin ma'ana da shi kadai yasan shi amsa masa tay ,murmushi P.A yayi don take ya harbo jirginta yabi bayan Governor AA KAITA da sauri don har yayi gaba.

"Ka kira Zaki?"

AA ya tambayi P.A dinsa bayan sun fito inda akayi parking motoci ana jiran fitowarsa ga securities dinsa a tsaye a wajen

"Nayita kira beyi picking ba kuma nasa a bincika inda King din ya sauka ama haryanxu ba'a gano ba but I send him a message akan kanason ganin King din"

"Meya ce?"

"No reply yet Sir"

Cikeda kululun takaici AA KAITA ya shige motar,PA ya shiga gaba sauran securities dinma suka shiga sauran motocin..

_FU'AD HASHIM_

Wata kakkaurar bakar matace ke saukowa daga stairs cikin shigar alfarma da atamfarta exclusive wanda aka mata dinkin manyan mata en boko da waya a hannunta,kana ganin fuskarta zaka karanto bacin rai shimfide.Tun kafin ta gama sakkowa take kwalla kiran Fu'ad dake zaune a parlor yana shan tea da remote a hannunsa yayi shirin fita aiki.

Daga kai yayi jin muryar mahaifiyarsa

"Mummy lfy da sassafe haka?"

"Ina kua lfy,bakaga abinda shashashar tsohowar matarka tayi bane jiya shiyasa tun farko na dinga nusarka akan auren er kafiri da ba wanda be san maiya aikata ba a kaff garin nan toh wallahi tun wuri kaje ka dauko min jikana kafin shegen nacin kwakkwafinta ya jawowa yaro matsala gwanda cen ita da uwarta data daure mata gindi su karata don na tabbata this time around ta tabowa kanta abinda saiya shafi kaf danginsu bama ita kadai ba"

Ajiye kofin hannunsa yayi cikeda takaicin Fahima yacewa mummyn nasa

"Mum nima niyata knn koda bakiyi magana ba tun jiya da naga lbryn abinda Fahima tayi a social media nayi niyyar yau ina tashi a office naje na taho da Salim,bansan me Fahima take nema ba,I think wannan so called profession din nata is driving her crazy"

Yaja wani tsaki ya mike
Chapter 4 · 0% Book details