← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 36

Sashe 10

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bashakka asalin Zaki ne kai don ina kyautata zato akanka"

Cikin jindadin yabon Babaji,King yace

"Nagode baba,Insha Allah zaka sameni fiyeda zato da tsammaninka"

Murmushi Babaji yayi yace

"Bara na musu magana koh"

Gyada mishi kai kawai King yayi,Babaji ya doshi indasu Dija suke sun k'uresu da idanu.Zama yayi kusada Dada ya kwantar murya kasa cikin fulatanci ya fara koro mata bayani,zaro ido Dada tayi cikin yare tace

"Wallahi bazaiyu ba,da hankalina bazan yarda na kai kaina gidan mutuwa ba.Lala lala Dija tashi² mu kama gabanmu Babanki yayi cinikin kanmu"

Ta fara daga Dija tana hawaye,ita de Dija jin abinda Babanta ya fada yasa zuciyarta rabuwa biyu ta wani bangaren murna take koh ba komai zata dinga kallon BAD'D'O kullum wani bangaren kuma tsorone kamar yanda Dada ta fada karfa dagaske yanke musu kai yayi ama ai tasan yanda Babaji ke matukar sonta bazai taba kaita inda zai zama ajalinta ba don Babaji shiyasa koh kiwo zai tafi yake yawo dasu gari² ita da Dadanta.

Dakyar da sud'in goshi Dada ta yarda akan zata bi King ama sai danqarawa King din harara take shi kuwa ya mayar mata da murmushi, haba ganin haka Dada ta koma turjewa tace allambaram ba inda zasu gashi yana musu murmushin mugunta.

"Kai kad'o kiji tsoron Allah,ki kyalemu muyi rayuwarmu ahaka bamu nemi taimakon kowa ba balle musa kanmu a halaka.Miyatti Allah miyatti Annabijo a yanda ya barmu da ranmu da lfy,don Allah kaima ka kyalemu na hadaka da Allah"

Dada keta mishi magiya Allah,Annabi.Babaji kuwa ganin bazata yarda ta dadi ba yasa shi daukar bacon buhunsa ya rataye ya dau sandarsa yace

"Kaga Aliyu muje,ka kyalesu masu kawo musu hari suna so suyi Karuwa da Dija kaga sun samu kenan daman nine nake karesu daddare"

Haba jin haka yasa Dada kara cafko hannun Dija sai gasu a gaban motar King suna tsaye jiki na rawa..

Babaji na daga gaban mota Dija da Dada a baya sun cure waje guda sai zaro ido suke,ta mirror gaban motar King yake kallonsu ya girgiza kai kawai yana murmushi cen yaji zazzak'ar muryar Dija na yiwa Dada magana da fulatanci.Bai tabaji tayi magana a gabansa ba sai yanxu,lumshe ido yayi ya dan kwantar da kansa kan kujerar yana driving a hankali kamar wanda kwai ya fashewa a ciki don wani irin kasala ne ya ziyarce shi a take

'Haka muryarta yake da d'an karan dad'i mai ga dad'in sauroro koh kuwa shine yake jin hakan?'

A ransa yake maganar take kuma yaji koli²n takaici ya tukare masa aransa tunawa da jiya daya fara ganinsu suna bara,knn haka kuwa yakejin muryarta.Ya godewa Allah daya tsaresu a inda suke rayuwa ya d'au d'amarar basu kariya da kulawa sosai iya karfinsa don he can't hide the fact,he's madly in love with the girl zai iya yin komai akanta

COMMENTS AND SHARE FISABILLAH 🥰🥰🥰
[1/6, 9:02 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

BY APHSERTEEN KHAIREE

ELEGANT ONLINE WRITERS

12

Har suka iso makeken gidansa dake tsakiyar unguwar gangare bbu wanda yace kala sai Dada da Dija dake magana kasa² tsakaninsu suna rarraba ido,bayan yayi horn maigadi ya bude masa gate nn su Dada suka kara tsurewa ganin wnn aljannar duniyar mai ban tsoro a idanuwansu sai kukan Dada suka jiyo wanda yasa King da Babaji juyawa bayan King yayi parking a compound din gidan

"Sikenan,sikenan hande min bone ya tabbata yau kwananmu ya k'are. Allah ya jikanmu ya jikanki bingel am"

Ta kara fashewa da kuka tana rike Dija da itama tasa kuka ganin Dada nayi badon taji abinda take yiwa kukan ba,girgiza kai kawai King yakeyi yana murmushin halin kafiya irinna Fulani, wato su inde suka kafe akan abu tho dakyar a juya musa ra'ayi.A da yanajin lbrynsu bai taba yarda ba sai yanxu daya gani ra'ayal ayn

Fitowa yayi a motar ya zagayo ya budewa Babaji shima ya fito don shi tsabar takaicin matar tasa koh magana ya kasa, bude musu back site din yayi. Dariyace ta su6uce mishi ganin yanda suka dungule waje daya suna kuka,Dada kuwa sai girgiza mishi kai take tana kara makalkale Dija a jikinta

"Rabu dasu kayi wucewarka,Ai'se ta fiye taurin kai kamar kafuran farko"

Babaji ya fada cikeda takaici,murmushi King yayi yace

"Aa Baba ayi hakuri,kazo ka lallabasu su shiga ciki"

Tsaki Babaji yaja ya matso kusada kofar baya,fada ya fara musu da fulatanci kamar zai ari baki yacewa Dija in bata fito ba sai ya kwakwkwada mata sandar hannunsa ba shiri ta dirgo daga motar kamar mai sauka akan machine saura kadan ta fadi kasa King da hankalinsa ke kansu yayi saurin rikota dukda haka saida guiwanta ya gurshe da kasan ai kuwa ta tsala wani gigitaccen ihu da saida gidan ya dauka wanda yasa Dada fitowa da sauri itama kamar zata fadi tayo kan Dija dake durgushe tana tsala ihu a kasa dukda kurjewar kadan ne saide ita duk k'ank'antar jini ta gani a jikinta tada mata hankali yake bataso.

Guri Babaji ya samu daga gefe yay zamansa ya dauke kai daga kallonsu, Dada kuwa zaman dirshen tayi a agaban Dija dake zabga kuka ta zuba uban tagumi kamar wasu marayu.

Magiyan duniya King ya musu akan su tashi a wajen don har an fara kiraye² sallah magriba ama sunk'i, kwallawa Baba maigadi kira yayi ya taho cikin hanzari

"Baba a aka kaisu waccen flat din na baya ka hadasu da masu aikin nn su nuna musu komai don ALLAH"

Ya juya inda Babaji yake zaune shima a kasa yana kallon wani waje yace

"Baba, ga Baba Audu zai nunamuku inda zaku zauna bari na shiga ciki lokacin sallah yayi"

Mikewa Babaji yayi yace
"toh yaro mungode kaide Allah yayi albarka" King ya amsa da Ameen ya wuce ciki da sauri.

"Muje baba" baba audu mai gadi yace tareda yin gaba, kallo daya Babaji yayiwa Dada da Dija da suke ragu6e waje daya a kasa sai wuri wuri da ido suke yayi wucewarsa batareda ya tankasu ba. Mikewa Dada tayi da hanzari tana cewa Dija ta tashi suka bi bayansa da dan saurinsu.

Saida aka yayi sallah Isha'i tukunna King ya shigo gidan tunda ya fita sallah magriba daman ya fadawa kukunsa akan yau ya kara sanwar girki yana da baki a baya snn inya gama ya kaimusu nasu da wuri. Flat din da su Dija suke direct ya wuce dauke da leda a hannunsu, a parlour ya samu Dada da Dija raku6e a kasa koh sallah basuyi ba. Shi kuwa Babaji daman tunda aka nuna masa dakuna da toilet da yanda zaiyi amfani dashi yay shigewarsa ciki bai kara bi ta kansu ba.

"Ha'a ya kuke zaune anan basu nunamuku dakunan bane, ina Baba?" king ya tambayesu, Dada tace

"Mude kayiwa Allah ka kyalemu gashi daga zuwan mu gidanka har jini ya fara fitawa 'yata tun kafin a yanka mu"

Cikin soma gundura da zancen na Dada dayaki ci yaki cinyewa King yace

"don Allah Dada ki bar zancen nn haka, ki yarda dani wallahi ni ba mugu bane. Ku kwantar da hankalinku ku dauki nn tamkar gidanku don Allah, yanxu de ga kaya na siyo muku da dan abubuan amfani. Ku tashi muje na nunamuku daki sai kuyi wanka kuyi sallah ga abinci ma naga an kawo muku"

Badan hankalin Dada ya kwanta da maganarsa ba dande bbu yanda ta iya ne, koma me ya samesu Baban Dija yaja musu, hakan nn ta daure ta mike tareda cewa Dija itama ta tashi.

Ita kuwa Dija tunda King ya fara magana take kallon bakinsa kawai, cewa take aranta inama tanajin abinda yake fada. Dakuna ne biyu a parlour sai kitchen da toilet, daya dakin ya bude ya samu babu kuwa Babaji na dayan knn ya shiga har ciki suka bishi, ya nunamusu toilet da komai ga furniture masu kyau wanda yasa su Dada sake baki suna kallo dakin kamar shashashai

Har ya juya zai fita ya tsinkayi muryarta tace

"BAD'D'O"

Juyowa yayi dukda baida tabbacin da shi take sai caraf idanuwansu ya sark'e dana juna,lumshe nasa idon yayi yanajin wani irin yanayi a jikinsa ita kuwa da sauri ta mayar da nata idon kasa ta fara wasa da zara²n fingers dinta tana cakud'asu da juna.Kura mata ido Dada tayi cikeda mamakin sunan da taji Dija ta kira King tana jira taji mai zatace masa

"Inason nayi wanka,a ina zanyi,a ina akeyi,dame zanyi kuma tayaya zanyi?"

Ta jero masa tambayoyi kusan hudu akan abu daya snn dayace mai hankali abin takaicin ma da fulatanci mutumin da koh zo na kasheka bayaji da yaren ama ita koh oho don duk tunaninta daga jiya zuwa yau ya fara koyan yaren nasu shiyasa tayi mishi tambayarta kai tsaye.

Tunda ta fara magana King ya k'ureta da ido yana kallon d'an karamin bakinta yanda take motsa shi dakyar tana maganar kamar an sata dole sai yaji ta k'ara burgesa sosai har baisan lokacin da tayi shiru ba saida yaji hargaggiyar muryar Dada tana mata magana cikin fada da fulatanci

Turo baki gaba Dija tayi irinna shagwa6a66un yaran nn

"Malam ki tafi kawai mungode,jeki abinki mun gane komai"

Murmushi King yayi ya fita tareda rufo musu kofar.Bangarensa ya wuce direct ya haura samansa sai lokacin ya shiga yayi wanka yasa jallabiya mara nauyi ya fito parlornsa dake hade da bedroom dinsa daya hannunsa glass cup ne filled with fresh milk yana dan sipping sai dayan kuma wayarsa ce yana dannawa,wata number da kana gani kasan bata nn kasar bace yayi dailing ringing daya biyu maishi yayi picking

Shiru yayi yana murmushi da alama maishi kai magana daga dayan bangaren,king ya yace

"So ya karatun, yaushe zaku samu hutu? I missed you here"

Murmushi ya kuma yayi yana sauraren mai magana

"Okay tho Allah ya nunamana,best of lucks"

Yayi cutting off,sai kuma ya kara dialing wata number bayan an dauka yace

"Yane guy,koda yake yanxu tsoho ne kai" dariya yayi bayan maishi yayi magana yace

"Nide ba wnn ba please inason gobe ka turomin Zee zata min wani taimako"

Tsaki yaja bayan maishi yayi magana yace "an gaya maka ni d'an iska ne kamar kai kuma in zanyi iskancin ma sai na rasa wanda zanyi dashi sai matarka ai saide kace nabi a hankali kar matarka tamin fyade a gidana"
Chapter 10 · 0% Book details