← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 36

Sashe 32

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka tayi zaman jiran tsammani na kwana biyu a dakin King sai Fresh milk dake fridge din dakin kawai take sha.Su Dada kuwa ganin Dija shiru yasa su tada hankalinsu nn Baba mai gadi ya basu tabbacin King na raye suma ya musu rakiya bangarensu da haryanxu yake nn yanda yake da babu abinda yya chanza

Kunya da kawaici na Fulani ya hanasu su Dada leka Dija da bincikar halin da take ciki.
Wanda banda sallah babu abinda take dagata,tana makale da photo album din king daya zame masa tamkar diary tana adduar Allah ya dawo mata da baddonta lfy ya kareshi a duk inda yake....

_FEDERAL HIGH COURT KADUNA STATE_

Tsit court d'in ya d'auka ana jiran mai gayya mai aiki Chief Justice Isyaku Barau ya bada damar fara gabatar da shari'a.

Fahima da Zee kaita na zaune daga benches din dake gaba²

Bayan ya bada dama registrar ya mike

"Court zata saurari shari'a tsakanin tsohon gwamna ALIYU MOHAMMED GIWA tare da gwamna mai ci yanxu AMINU ABDULSALAM KAITA wanda aka samu hannunsa dumu² cikin daya daga cikin kunqiyoyin matsafi masu gwarkuwa da mutane ta hanyar tsafi dasu,dukda haryanxu ba'a samu nasarar kama shi saide sauran en uwansa na kunqiyar da suke hannun hukuma"

Bayan ya gama bayani ya mikawa Alkali takardun ya karba, saida ya gama dubawa tukunna ya dago kansa tare da gyara farin medicated glass din idonsa yayi dan clearing throats dinsa snn yace

"Ina lawyern mai kara yake"

Tashi yayi cikin ladabi ya gyara bakin rigar aikinsu yace

"Sunana BARRISTER FU'AD HASHIM,nine lawyer mai kara"

Murmushi Fahima dake zaune daga baya tayi ta kafe shi da ido cikin tsantsar son mijin nata

"Koh bangaren wanda ake kara suna da Lawyer da zai karesu"

Alkali ya tambaya

"Sunana BARRISTER JOSEPH YA'U,nine lawyer mai kare wa'inda ake qara"

Bayan sun gama gabatar da kansu,alkali yayi dan rubuce²nsa snn ha dago yace

"Lawyer mai qara,Bismillah"

Tashi Fu'ad yayi

"Inason court ta bani dama yiwa David Peter daya daga cikin member na cults din tambaya"

"Court ta baka"

Nn aka fito da David tare da wani dan sanda zuwa wajen da aka tanada don amsa tambaya

"Court zataso sanin asalinka da aikinka?"

"Sunana David Peter ni Igbo ne dan asalin garin Abeokuta,Nine mallaki Bbn company nan na DP AND SON'S"

"Menene alakar da GOVERNOR AA KAITA?"

"Abokina ne tun muna jami'a"

"Tun yaushe kake cikin kunqiyar tsafi da mutane?"

"Tun ina shekarar farko a jami'a"

"Tayaya ka samu kanka a cikin kunqiyar"

"Ta hanyar Uncle dina,kanin mahaifiyata knn"

"Mutane nawa kayi sanadiyyar halakarsu?"

"Babu adadi"

"Wanene na farko?"

"Mahaifiyata"

Take court ta dau hanayi

Nan alkali ya buga gudomarsa yana

"Order order"

Tsit court din ta kuma dauka,sauran en kunqiyar da sai tsoro² suke.
Baban fahima kuwa tunda ya daga kai suka hada ido da Fahima sau daya bai kuma ya sunkuyar kasa bai kuma dagawa ba

Gyaran murya Barrister Fu'ad Hashim yayi sannan ya cigaba

"Waye shugabanku?"

"ODUBARIBA,ni kaina zuwa kunqiyar nayi na sameshi yana jagorantarta snn ina da tabbaci ya mutu tun lokacin da aka kamamu"

"Menene alakar ka da ALIYU MOHAMMED GIWA wato King kuma meyasa kuke farautar rayuwarsa?"

"Shima member kunqiya ne tun muna jami'a.........
[1/6, 9:16 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

BY
Aphserteen khairee

ELEGANT ONLINE WRITERS

40

"Kasan hukuncin false allegations kowa?"

"Yes I know and am not making any false allegations, that's the bitter truth"

"Menene hujjarka?"

"Lawyern mu na tare da dukkan hujjoji da zai bayyana alak'ar King da kunqiya"

D'an juyawa Barrister Fu'ad yayi cikin dabara suka had'a ido da Fahima,Lumshe masa idonta tayi a hankali ta budesu tare da d'an girgiza masa kanta snn ta aiko masa kayataccen murmushi

Murmushi Fu'ad yayi ya d'an shafa sajensa,ya gyara tsayuwarsa yana fuskantar alkali snn yace

"Iyakacin tambayoyin da zanyiwa David Peter,nagode Ya mai girma mai shari'a"

"Koh Barrister Joseph Yau nada tambayoyin da zai yiwa David Peter?"

"Ina dashi mai girma mai shari'a"

Mikewa yayi ya isa gaban David yace

"Tun yaushe Mohammed Giwa wato King yake cikin kunqiyarku?"

"Objection ya mai shari'a,bai kamata Barrister ya yanke hukunci kai tsaye na cewa King na cikin kunqiya ba tare da kwakkwarar hujja ba"

Fu'ad yayi saurin katse shi

"A kiyaye Barrister Joseph"

"Nagode ya mai shari'a"

Murmushi Barrister Joseph yayi ya take zuwa gaban desk dinsu ya dauko wasu takardu da photos

"Ya mai shari'a wannan itace hujjata ta farko da yake nuna king nada alak'a da kunqiya.
Bayanai ne tun daga lokacin da Mohammed Giwa ya tsaya takararsa ta farko da yanda ya kashe magudan kudade duba da aikin da yakeyi a wnn lokacin bai isa ace ya samu wnn kudin ba snn binciken mu ya nuna bbu wata committee data tallafawa takarar tasa"

Registrar ne ya karbi takardun snn ya mikawa alkali ya duba ya ajiyesu gefe,Barrister Joseph ya cigaba

"Mr David Peter koh zaka fadawa court dalilinka na cewa King nada alaka da kunqiyarku?"

"Tabbas yana da alaka, sbd koh lokacin da zai tsaya takara saida kunqiya ta taimaka masa sosai duba da hidima da yake yiwa kunqiya don shi kadai ne ya taba bada sacrifice din iyayensa dukka a lokaci guda"

Bayan David yayi shiru Barrister Joseph ya cigaba

"Ya mai girma mai shari'a akoi hotonan King a cikin hujjar Dana kawo Wanda aka daukesa a kofar makabarta snn kayansa duk ya 6aci da jini.
Mun sami tabbaci daga bakin dukkan en kunqiyar cewa a washegarin dawowar tasa aka bashi aikin kawo jini kuma sun tabbatar mana a makabarta aka sashi wnn aikin"

Saida alkalin ya gama duba dukkan shaidodin tukunna yayi ajiyar zuciya ya dago kansa yace

"Court na buqatar ganin Mohammed Giwa cikin gaggawa"

Barrister Fu'ad Hashim ne ya mike cikin ladabi ya sunkuyar da kansa yace

"Ya mai shari'a muna neman afuwan court na rashin zuwan Mohammed giwa sbd shock din daya shiga na rashin babban yaronsa wato DSS ALIYU DAPO"

"Court zata daga kara har zuwa 22 ga wnn watan kuma muna fatan Mohammed Giwa ya kasance a wnn zama"

Ana tashi kowa ya fara kananan maganganu yana tofa albakacin bakinsa,wasu suce sharri ake yiwa King wasu kuma suce akoi kanshin gaskiya a maganarsu David na kusantuwar King da kunqiya

Fahima da Zee suna dage gefe jikin motar ta suna jiran Fu'ad,daman Zee tunda suka fito a asibitin suke tare a gidan Fahima

Basu fi 5mins ba sai gashi nn ya fito ya dosu inda suke

"Zanzo anjima na karbi laptop din naki,ki tabbata kin hada kan dukkan evidence din Insha Allah a zama na gaba zamu kawo karshensu"

"Insha Allahu zanyi kokari,na rasa inda nasa laptop din ne ama maybe a office na barshi yanzu zanje cen na duba sai na maka waya kazo ka karba"

_AA KAITA_

Murk'ushishi ya dingayi a qasa na azabar ciwon da cikinsa ke masa,ji yake kamar ana tsinka hanjinsa.
Tuni mutane suka cika a kansa ana tambayansa lfy,wani police dake gefe ne ya lura da cinkosun jama'ar wajen ya karaso yana tambayar meya faru

Shi ya daga AA da har jini ya fara fitowa ta bakinsa da hancinsa,yana ganin fuskarsa kuwa ya ganeshi don an kawo musu hotonsa nn headquarter su akan ana nemansa wanted
Yanxu haka patrol din daya fito dasu kenan

Wayarsu ta aiki ya ciro a aljihunsa ya kira motarsu inda sauran en uwansa suke

Suna zuwa aka saka AA a motar sai asibiti,kafin su karasa kuwa har sun kira headquarter sun sanar da ganin AA KAITA da sukayi nn take aka kira babban headquarter na Kaduna inda case d'in yake aka sanar

Bangaren Ema kuwa da farincikinsa ya sauka garin Kaduna,yasan may now maganin beran daya sawa AA ya gama dashi

sai da ya tsaya ya siya babbar Ghana most go tukunna ya dau taxi ya fadamasa inda zai kaisa,tafice mai nisa daga park zuwa anguwar da boyayyen gidan da AA yake

Bayan ya sallami mai taxi din baisha wahala ba wajen bude jam lock din gate d'in dama gwani ne wajen balle gidan jama'a don tsohon qungurmin barawo ne

Tsari da haduwar gidan har saida ya hadiye yawo haka ya dinga bin gidan da ido har ya nufi hanyar entrance nn ma karfe yasa ya balle kofar

Yana karasawa bedroom inda safe din yake ya saka pin din da AA ya fadamasa

Magudan dalolin kudade ya gani har saida yasa ihu don dadi,cikin sauri a jidesu a Ghana most go dinsa koh tsayawa rufe kofar naiyi ba ya fice a dakin ya fito compound

"You're under arrest, ur hands behind ur back"

Cikin razana ya saki jakan ganin en sanda a zagaye dashi koh ta ina

_KING_

Yanda jikinsa ya dau zafi ga wani rawan dari da fargici da King keyi ya mugun tsorata Dija

Hugging dinsa tayi sosai tana hawaye don bata taba ganinsa cikin wannan yanayin ba

Karatu ta fara masa a kunnensa cikin zazzakar muryarta dake hade da kuka, basu fi en mituna ba ya fara ajiyar zuciya a jajjere ya kwantar da kansa sosai a jikinta ita kuma ta cigaba da masa karatun tana shafa kansa har bacci mai nauyi ya daukesa

Batayi wani yunkuri ba dukda nauyinsa daya sauke mata hakan nn ta kyalesa sai ma kara makalesa a jikinta da tayi ta jingina da jikin kofar
[1/6, 9:17 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

BY
Aphserteen khairee

ELEGANT ONLINE WRITERS

41

King ba shi ya farka ba sai pass 10 ama sai ya k'i bude idonsa yana jin kamar mafarki yakeyi,yana bude idon zai ganshi shi kadai a dakin dukda yana jinsa a jikin mutum

Wata zuciyar kuma na fatan ace mafarkin ne daya tuna da maganar doctor

_"He's no more"_

Bude idonsa yayi cikin firgici yana

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,Zaki"

Yanda ya firgita yasa Dija itama farkawa tana kallonsa da mamaki,kafeta shima yayi yana kallonta.
Tabbas ba mafarki yakeyi ba,wnn dijansa ce a gabansa

Ya rasa wani irin yanayi zuciyarsa ke ciki.Farincikin ganin DIJA koh alhinin rasa ZAKI

Higging d'inta yayi sosai tana ji yanda zuciyarsa ke tsananta bugu

"Ka tashi muyi sallah"

Ta rad'a masa a kunne,girgiza mata kai kawai yayi ta taimaka mishi ya mike
Chapter 32 · 0% Book details