← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 36

Sashe 16

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

SORRY JIA NAYI MISTAKEN PAGE NASA 18 INSTEAD OF 17,YAU MUKE PAGE 18 🙏🏻

_SHEIK IMAM MOHAMMED SULEIMAN_

"Tunda naji labarin dawowarka nake expecting zuwan ka gashi bbu hanyar samunka koh ta waya"

Cikin girmamawa da sunkwui da kai King dake zaune kan lallausar rug din dake malale da parlor yace

"Wallahi nayi busy ne sosai Sheikh nima zuwan yana nan a raina"

"Tho masha Allah,an dawo lfy ya ka baro su SHEIKH ABDULHAMEED din?"

"Duk suna lfy,suna gaisheka da iyalin dukka"

"Muna amsawa"

Shiru sukayi na en seconds tukunna Sheikh yayi gyaran murya yana kallon King

"Aliyu"

"Na'am Sheikh"

"Inaso ka dage da addu'a sosai,lalle akoi masu farautar rayuwarka banda mak'iya da suke bayyane akoi na 6oye da suke tare da kai masu matuk'ar hatsari.Muma nan muna tayaka da iya gwargwadon sanin da Allah ya bamu insha Allah bazasu ta6a cin nasara akanka ba"

Wani huci mai zafi King ya fesar yace

"Sheikh, ina cikin tashin hankali.Na rasa dukkan nutsuwata,na rasa ta ina zan fara ga rashin Dija da nake ji a jikina tana raye. Bansan ya zanyi ba,bansan ta ina zan fara ba kaina da kwakwalwata duk ya toshe don Allah Sheikh a taimaka min"

Cikin tausayawa yace mishi

"Ka tashi tsaye ka nemi a wajen Allah karka dogara da wani koh ni ka roka da kanka, ka sani Allah baya bacci snn baya zalunci kuma baya goyon bayan azzalumai.Da yarda Allah,Allah zai bayyana maka mak'iyanka zaka gansu ra'ayal ayn.Zasu durgusa a gabanka suna mai neman afuwa da yafiya,Allah zai kare maka matarka a duk inda take inde tana raye.Ka kwantar da hankalinka kayi ibadarka cikin nutsuwa nima insha Allah zan tayaka"

Sai yanxu King ya danji relief kadan a zuciyarsa,with full confidence and hope ya bar wajen Sheikh bayan sun gama tattaunawa akan siyasarsa snn ya bashi shawarwari masu kyau da inganci.Ya k'ara masa wasu addu'o'i

Bayan King ya shiga mota ya kwantar da kansa kan seat ya lumshe idonsa kamar mai bacci yaji anyi knocking window,ya bude Zaki ya miko mishi waya

"Ga secure line d'inka,Chairman din political party na son magana dakai"

Yana kar6a sukaji wani girgitaccen sound..

_FAHIMA ALIYU_

Washe gari dakyar ta tashi da safe ta hau shirya kanta da Salim,cikin sauri take komai sbd makarar da tayi don through out the night batayi bacci ba tana aikin bincike inda taci nasarar binciko asibitin da Dija ta haihu HEALTH CARE PRIVATE HOSPITAL.

Bugun gate ta dingaji lokacin tana 6alle karfen bra dinta Salim kuma yana shan tea a parlor, sbd yanda take sauri yasa ta kasa ma saka karfen ga bugun gate din da ake k'arayi.

"Ya Salam, dole ma na nemi gate man"

Ta fada tareda jan tsaki,hijab din da tayi sallah dashi ta dauko kawai tasa ta fito

"Waye"

Shiru akayi,ta kara maimaitawa

"Who's that?"

ta fada d'a d'an karfi tanaji yanda gabanta ke dukan uku² zuciyarta ke tsinkewa

"Fu'ad"

Aka bata amsa daga wajen,F'uad kuma ta k'ara maimaitawa gashi tabbas muryarsa ce. Bude gate din tayi,idonsu ya sark'e dana juna take nata ido ya tara kwalla ganin yanda ya chanza yayi duhu ya lalace har wani kashin wuya yayi ga idonsa duk ya zurma ciki.

Wani mugun tausayi da kaunarsa taji a ranta Wanda tilas ya haddasa kwalar idonta zubuwa ba tareda ta shirya masa ba,cikin sanyin jiki suke kallon junansu kallo irinna so da kauna ga dumbin kewa da buqatar juna.Ji yake kamar yayi hugging dinta tightly a jikinsa koh ya rage zugi da radadin da yakeji a ransa,dakyar ya bude bakinsa yace

"Zan iya shigowa?"

A d'an daburce ta bashi hanya ya wuceta ta rufe gate din,kamar sokuwa yana gaba tana biye dashi a baya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki har suka iso parlor. Salim kua yana ganin daddynsa yayi tsalle harda zubar da tea din hannusa ya rungume Fu'ad cikin tsantsar murna da kewar baban nasa

"Daddy I missed you"

"Miss you too,hope you're fine now"

"Naji tsoro sosai daddy inata kuka ina nemanka kai da mummy ama dukkan baku zo ba har suka yanka Mami irin yanda akeyi a film na ganta kwance a kasa bata magana cikin jini kuma naga photo wanda ya yankata wajen Mummy"

D'aga kai Fu'ad yayi ya kalli Fahima data zuba musu ido

"Are you still working on it?"

"Salim jeka jirani a mota ina zuwa yanxu"

Makalewa jikin babansa yayi yace

"Uhm uhmm ni yau daddy ne zai kaini school"

Shafa kansa fu'ad yayi yana mishi murmushi

"Jeka jirani tho,yau tareda daddy zakaje school"

Cikin murna yana tsalle ya fita a parlor

"Heema why are you so stubborn,me kike nema da har kike saka kanki a hadari akansa,kikasa zuciyata take muradin kasancewa tare da yin nesa dake.Meyasa bazaki hakura ba haka?"

"Bazan iya hakura ba fu'ad har sai burina ya cika"

"Har sai sun salwantar da sauran rayukan innocent people dake tare da ke koh? Fine,zan tafi da Salim I don't think this is safe for him anymore"

"No Fu'ad,no u can't do this to me.You can't take him away for me,bazaka rabani da kanka kuma ka rabani da d'ana ba"

Ta fashe da kukan da har cikin ransa yake jin radadinsa

"Ke kika raba kanki dani Heema,u choose your work over and over again.Aikin da yayi sanadiyyar mahaifiyarki ya kusa da ki rasa yaronki da uban d'anki ama still....

Kasa karasawa yayi don takaici yayi tsaki kawai yayi hanyar fita a parlor, da gudu Fahima ta rungumeshi ta baya tana kuka

" please fu'ad,please don't leave me again karka rabani da d'ana I need you both please"

Juyawar Fu'ad yayi daidai da breaking news da akasa a TV dake kunne a parlor, wanda yasa fahima juyawa ya d'auke hankalinta.Tsaki Fu'ad yayi yayi ficewarsa cikeda takaicinta suna mltsaka da argument ama all she care is news.....

Kuyi manage zuwa anjima 🙏🏻
Don't forget to share and comments 🥰🥰
[1/6, 9:06 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

ELEGANT ONLINE WRITERS

19

_ZEE KAITA_

Dakinta ta wuce direct ta kulle kanta a cikin don bata buk'atar kowa sbd halin rud'un da take ciki,wajen closet d'inta ta nufa cikin sauri take birkice kayan tana neman abu kana ganinta kasan bata cikin nutsuwa.Wani abu kamar powder cikin farin leda dake cen kayanta ta d'auko har wani ajiyar zuciya tayi data ganshi, dawowa tayi bakin gadonta ta zuba wnn abun akan side drower.Cikin wani irin kwarewa ta kafa hancinta tana zuk'a har tsakar kanta take jinsa,haka ta dingayi inta zuk'a sai ta wani d'aga kai tana lumshe ido tana jin wani nutsuwa na shigarta,take idanunta suka sauya kala.

Tafi 30mins tana zuk'an wnn powder har bacci ya kwasheta a wajen.

Hannu taji yana yawo a jikinta tun daga kasanta har zuwa kan kirjinta kamar a cikin mafarki take jin yanda ake mata wasan dayasa jikinta mutuwa ta k'ara wani mikewa tana bank'aro jiki harya cire mata rigar dama bbu komai a jikinta ya shiga sarrafata iya son ransa hakan nn ta biye mishi koh bude ido batayi ba suka nitsa cikin luguiguita junansu,tun yana biye mata da iya karfinsa har ya soma gajiya daman yasan halin Zee bata dau chaji bama ya aka kare balle yaga yau tasha cocaine din nata.Har kusan asuba yana abu daya ama sam bata nuna gajiyarta ba sai silalewa yayi ya gudu ya barta ita kadai tana faman biyawa kanta buqata.Bayan sallar asuba AA ya shigo dakin nata don dubata ya,kunna wutan dakin yayi nn ya hangota tsakiyar gado bbu komai a jikinta har bacci ya dauketa.

Jin ana k'ara ta6a jikinta ya kai bakinsa kirjinta yasata wani irin qara cikin nuna jindadi ta d'ada turlmishi kirjin tana k'ara danna kansa

"Yawwa Shams (P.A)ka cigaba please,I still need u"

Dago kansa AA yayi yana kallonta da mamaki,jin ya tsaya ita kuma ta bude idonta zata mishi magana sai ganin mijinta tayi cikin dan diriricewa tace

"Emm emmm AA yaushe ka shigo?"

Tana kokarin jan blanket din ta rufe jikinta,murmushi yayi ya kara yaye blanket ya kaiwa ***sy hot peck cike da bariki ya kara jawota jikinsa yana shafata tareda daura bakinsa setin kunnenta yana d'an lasa

"Shiiii...calm down beb,aiki zan bawa sugar pot dina yamin"

Kokarin seta kanta tayi itama tace

"Aiki zaka bashi koh aiki zai maka,kasan pot dinka is always filled with honey sweeter than sugar"

Dan cizon kunnenta tayi yana wani shek'iyin murmushi tace

"Awwchhh"

Tana kara shigewa jikinsa

"Bani zanyi aikin ba,nide zan bashi aiki yamin"

Cikin rashin fahimta tace mishi

"Wani irin aiki?"

"SEDUCE KING"

Ya rada mata a kunne,zaro ido tayi tana kallonsa da dumbin mamaki

_FAHIMA_

Cikin sauri ta shiga dakinta tama manta da wani fu'ad koh Salim ta saka kaya koh breakfast bata tsaya yi ba ta dau key da sauran abubua ta fito,direct inda taga abin ya faru ta nufa inda ta samu d'and'azon jama'a ga en sanda kota ina sai en jarida da aketa turesu suna kokarin daukar rohoto.Sai kokari itama take ta hango wajen da asalin mutanen da abin ya shafa addu'arta Allah yasa ba motar su King bace

"A k'aro mana ambulance daya don bayan motar tasu akoi mutanen da sukaji boom din ya shafa ama su da sauran numfashinsu,quick please"

Ta tsinkayi muryar wani police dake waya daga gefe ga wajen haryanxu hayak'i yakeyi tama kasa daukar komai sbd yanda aka cika sai hak'ura tayi ta shiga motarta ta wuce office bayan ta d'auki iya abinda zata iya.

Tunda ta shiga office ta kasa aiki hankalinta ya kasa kwanciya fatanta Allah yasa King yana lfy ama da harda shi ai dole za'a fada don koh a news cewa sukayi boom ya tashi da daya daga cikin motocinsu King.

"Who's attacking him? I must found out"

Ita kadai take magana a office din sai kai kawo take,wani tunani ne yazo kanta tace "yes" ta fito a office din ta nufi na boss dinta.Knocking ta farayi yace bata izinin shigowa,bayan sun gaisa yace

"Kinga abinda ya faru yau?"

"Yes Sir yanxu ma daga wajen nake"

"But you're late,don har press dinmu daya ya rigaki d'auko rohoton tun dazu"

"Na makara ne yau,sai a TV naga news din"

"Allah ya tsare" tace "Ameen"
Chapter 16 · 0% Book details