← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 36

Sashe 21

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ma bata nemi rakiyar kowanne guard da driver taja motarta ta fice a govt house din

9:05pm ta karaso hotel din,da hijab dinta harda niqab kamar ta Allah.Da tazo reception kua saida ta daga niqab din ta musu bayani inda zata room102 wani ma'aikaci guarding dinta har kofar dakin

Bata tsaya knocking ba ta murda kofar wanda ta jita a bude ya shige tareda kullewa,YANA tsaye ya juya bayansa hannayensa cikin aljihun jeans din dake jikansa don kananan kaya bak'ak'e hatta pcap dake kansa da takalmi dukka.Cire hijab din tayi ta ajiye a gefe daga kasa tareda Jakarta tana wani tako ta karaso inda yake tsaye

Hugging dinsa tayi ta baya tareda kwantar da kai a bayansa tana jin irin shauki a ranta farinciki mara misaltuwa

"Close ur eyes"

Ya fada a hankali kamar mai rad'a,yana shafa hannunta dake makale a jikinsa.Without second thought ta rufe idonta tana murmushi

"My eyes are closed my love,can't wait to feel ur warm hot lips"

Juyawa yayi yana karewa fuskarta kallo,shima yana aika mata wani killer smile dukda idonta a rufe yake sai kamshin turarensa da take shak'a.Ta matso taji lips dinsa a nata, slowly ya fara aika mata wani irin passionate kiss dayasa dukkan wani gab'ab'ai na jikinta mutuwa tanaji tsayuwar na neman gagararta

Rikeshi tayi gam² cikin kwarewa itama ta fara mayar masa martani kamar zata cinye bakinsa

She can't believed wai itace yau a jikin King,all her dreams for years are surely coming true.Tsayuwa ne ya soma gagararsu har saida suka dangana da gado,inda ya mata rufa da jikinsa yana aikawa kowanni sashi na jikinta saqonni masu rikitarda kwakwalwa

Dukkansu sun fada wata duniyar ta daban basaji,basa gani don har lokacin idon Zee a rufe yake tana karbar abinda ta dade tana muradin samu daga wajen masoyinta King dama tun suna tsaye ya samu nasarar rabata da rigar jikinta ta fadi kasa, kyakkyawar surarta ya bayyana kasancewar bbu komai a jikinta sai rigar dama

Sun lula iya lulawa,sun nitsa cen²n duniyar nishadinsu cikin shagala da juna...

Tafi suka fara ji kamar daga sama wanda yasa Zee bude idanunta da suka mata nauyi cikin sauri, charaf idonta ya fada kan wanda yake kanta bbu riga jikansa

"SHAMS......"

Ta furta a matukar tsorace da tsananin tashin hankali,sai kuma ta mayda kanta inda take jiyo sautin tafin

Ganin King ya tsaye yana zabga wani irin murmushi na mugunta ya sata kara rudewa,tashi yayi da sauri yana gyara wandonsa tareda neman rigarsa yana sinne kai kasa sai lokacin ta kalli kanta da take tsirara take ta fara jawo banklets din kan gadon tana kokarin rufe jikinta

Zama King yayi a kan kujerar dake fuskantar gadon yana duba wata er camera dake hannunsa ya dago kansa ya kalli P.A

"You can leave"

"Ranka ya dade iyalina fah?"

"They're home already"

Cikin sauri ya fice a dakin ya bar Zee dake ta rusar kuka,ashe duk trap King ya hada mata sai yanxu takejin haushin kanta na rashin tunanin abinda tayi na zurmawa a tarkon King din cikin dan k'ank'anin lokaci

"Thousand days for the theif, one day for owner"

King ya fada bayan ya aika mata wani shegen murmushi ya bude kofar ya fice ya barta dukunkune cikin blanket tana kuka akan gadon.

_WASHEGARI_
Yau ta kama zagayowar sati na program din Fahima da gubernatorial candidate inda yau zatayi hira da KING

She's so much eager and well prepared for it.Ba ita kadai ba har jama'a ma sun kosa sanin cewa Fahima Aliyu gwanace wajen zakulo tamboyoyi masu saka mutum cikin rud'u

Kowannensu ya kintsa cikin shiga na alfarma da kamewa ta fara gabatar da shirin inda tayiwa King barka da zuwa ya amsa fuskar sa a sake da kayataccen murmushi yana kallon camera

"My first question to our former and new gubernatorial candidate ALIYU MOHAMMED GIWA known as KING is"

Shiru tayi na en seconds tana kallon fuskar king da murmushi snn tace

"Masu kallo zasu so sanin some little things about you sir"

Cikin sakin fuska yace

"Go ahead"

"Words in ur heart?
Ur desires?
Ur fears and
Most importantly the secret that kept u in for so long?"

_MUJE ZUWA FANS YANA TAFE DA DUMINSA_⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️

Kuyi manage da bbu gwanda ba dadi 🥴

COMMENTS
SHARE FISABILLAH 🙏🏻
[1/6, 9:08 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

BY APHSERTEEN KHAIREE

*ELEGANT ONLINE WRITERS*

24

Gyara zama yayi tare da gyaran murya yana kallo Fahima Aliyu snn ya maida akalan kallonsa kan camera yana murmushi yace

"Ni Aliyu Giwa the words in my heart?" Sai kuma yayi shiru na en seconds tukunna ya cigaba

"Na taso a tsakiyar talakawa,na rayu da soyayyar al'umma,na gina zuciyata da murad'in taimako da kawo kowanni irin cigaba a k'asata baki daya,ina fatan da add'uar Allah ya cikamin burikana na alkhairi akan dukkan al'umma.Masoyana masu goyon bayana,en uwana da abokan arziki kai harma da mak'iyana masu son ganin bayana ina musu fatan alkhairi a koda yaushe.These are the words in my heart"

"Masha Allah"

Fahima tace tana kallon King daya cigaba da magana

"My desires?"

Shima ya fada da sigar tambaya nn ma ya cigaba

"Is to be a great and good leader to my good people and great nation.Sai me ma kika tambaya?"

"Your fears Sir?"

D'an lumshe ido yayi ya bude,yanayin fuskarsa ta chanza a take ama yayi kokarin controlling kansa da hanyar kwakulo fake smile yace

"Abinda nake tsoro a raina yanxu biyu ne,Na farko shine rasa matata,that's my first fear.Inason amfani da wnn d'ama wajen rokon barar al'umma da dukkan masoya na dasu tayani addua Allah ubangiji ya bayyana min ita cikin gaggawa da koshin lfy"

Shiru ya d'anyi wanda yasa Fahima yin shiru itama tana kokarin son karantar yanayin da yake ciki,hakama masu saurare daga kan radio da masu kallo a TV hakama masu bin shirin live a kowanne kafar sada zumunta duk sun tsaida hankulansu sun dakatar da comments dinsu suna sauraron King daya cigaba da magana

"Second fear d'ina shine ache nasamu mulki amma na kasa cika burikan talakawa na kasa riqe amanar da Allah ya danqamin nakasa yin adalci, naji son mulki da giyar mulki ita take juyani naji cewa zuciyata ita take juyani takesani yin abinda raina keso,naji cewa kaina nakeso nagini ba qasata da al'umma naba"

yadakata kadan sannan yaja numfashi murya na rawa yace

"Yah Allah karka bani waanan mulkin in har zansamu namanta dakai,Yah Allah karkabani wannan mulkin inhar zan sab'a maka ya zama sanadiyya halakata ta hanyar sa bayinka cikin kuncin rayuwa"

Ji tayi jikinta yayi sanyi,taji bazata iya masa tarin tambayoyin da tayi niyya ba don ya rufe mata baki da maganganunsa.Ajiyar zuciya ta sauke snn tace

"Ameen ya Rabbi,my last question is What's the secret that kept you in for so long Sir?"

"It's had been a while,na tsawon shekara 6 da nayi bbu wani sirri daya boyeni.A kullum ina kwana na tashi da kewar k'asata,Masoyana baki daya.Addu'ata kullum Allah ya dawo dani gida lfy cikin aminci,al'ummata su karbeni with their clean heart su bani damar jagorantarsu a karo na biyu da dukkan karfina.There's no secret that kept me in for so long"

Anan Fahima ta rufe shirin tare da yiwa King godiya,har yaje parking space jama'ar wajen na biye dashi a baya suna ce masa sai kayi tare da jinjina masa da addu'ar Allah ya bayyana masa matarsa da samun nasara kan takararsa.Hatta ma'aikatan wajen jikinsu yayi sanyi dajin kalaman King din haka Fahima ta dawo office dinta jiki a sanyaye ta tattara ta koma gida kawai don bataji zata iya wani aikin kuma tana buk'atar hutu don samun kwalkwalwarta tayi aiki da kyau.

Washe gari ya kama Thursday ta tashi as usually tayi shirin office dukda jikinta still a mace yake wanda ta rasa dalilin faruwar hakan,abubua dewa suke mata yawo a kwanyarta da takeson aiwatarwa cikin k'ank'anin lokaci wanda dukka yake buk'atar dogon nazari da bincike akai gashi tanaso a weekend dinnan taje ganin Babanta kamar yanda ya bukata dukda shima tafiyar a sanyaye take tashi tanaji kamar karta je ama dole ta kokarta taje din koh da kwana daya ne tayi ta dawo.

Harta shiga motarta sai taji buk'atar zuwa taga Salim tunda har yanxu 8am baiyi ba maybe ta samesu a gida bai tafi school ba,nn ta juya akalar motarta zuwa anguwarsu Fu'ad

Luckily kua ta samesu a bakin gate sun fito daga gida knn mai gadi ya rufe Fu'ad zai sauke Salim a school kafin ya wuce wajen nasa aikin.Ganin motar Fahima ya sashi parking a gefe itama tayi tareda fitowa ta doshi motar Fu'ad d'in

Salim na ganin mummynsa ya bude kofar motar dake zaune a gaba ya fito da gudu yana mata oyoyo inda tayi rungumeshi cikeda kewar d'an nata,fitowa shima Fu'ad yayi yana kallonsu yayi folding hands dinsa

"Mummy I missed you,when are you coming back to daddy ni banason gidansu grandma kullum tana yiwa daddy fada wai kar yaje wajenki kuma nima tace bazan koma wajenki ba"

Ya fada cikin muryar shagwaba da iyakar gaskiyarsa,kissing din cheeks dinsa tayi tace

"Don't worry babyn mummy, mummy is soon coming to take you back home"

Yeeyyyyy ya fada cikin jindadi yana tsalle,matsowa Fu'ad yayi kusada su ba tareda ya kalleta ba ya kama hannun Salim

"Oya let's go,we're late"

Saida Salim ya shiga mota snn Fu'ad ya juya ya kalleta

"Duk lokacin da kika shirya zama full house wife and caring mother,you'll always be welcome with an open arms"

Bye² Salim ya dinga mata har Fu'ad yaja motarsa ya barta tsaye a wajen cikin mutuwar jiki take taji hawaye ya fara sauka a idonta ta kusa 20mins tsaye a wajen dakyar taja kafarta ta karasa wajen motarta. Hakama a motar saida taci kusan 10mins tukunna ta tayar tana tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki a takaice saida takai pass 9 kafin ta iso office

Tun a nesa ta fara hango taron jama'a da motocin en sanda an kewaye ma'aikatar tasu yanda bbu wanda zai shiga wajen in ba jami'in tsaro ba.Daga dan nesa tayi parking ta fito tsorace ganin ambulance ana kokarin saka mutum cikin jini kaca² wanda har baka iya gane wanene yasa gabanta wani mugun faduwa har jikinta na rawa
Chapter 21 · 0% Book details