← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 36

Sashe 26

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Garin yaya ka jefa kanka cikin wannan mummunar halakar AA?"

KING ya tambayeshi yana kallonsa da idonsa da suka bayyana irin raunin da yake ji a ransa.Tun daga lokacinda ya fara mu'amala dasu David har zuwa yanda akayi ya fada harkar ya bawa King lbry

"Tayaya na tsinci kaina a ciki kuma ni menene alakata ta kunqiyarku da har kuke neman na zame muku shugaba,meyasa sai lalle ni?"

"Saboda irin farinjini da tarin nasarorin da kake dashi,lokacin da kunqiya ta buqaci na kawo wani makusanci nawa idan baka manta ba kasha tuhumata da kyamatar kudin hannuna Wanda hakan ba karamin ciwo yakemin ba shiyasa kawai na yanke shawarar jefaka kaima a harkar inga yanda zakiyi.Dana kai sunanka kunqiya nan take sukayi bincike akanka sukaga yanda kake da farinjinin jama'a kuma hakan ba karamin taimako bane ga kunqiya nan suka amince suka bani wani kwan tsafi guda biyu.

Watarana ka dawo daga lectures a gajiya da yunwa ni kuma nayi amfani da wannan kwan na dafa maka indomie dashi idan zaka iya tuna ranar"

Ya kyalkyale da dariyar mugunta,shiru King ne ya kokarin tunawa.Tabbas kuwa yasan lokacin don sbd yunwar da yakeji bai kawo komai a ransa ba ya cinye indomie nan da kwan daya dafa mishi guda biyu.AA ya cigaba

"Tho daga wannan lokacin kunqiya ta fara amfani da ruhinka wajen biyan buqatunta ba tareda saninka ba ni kuma da cigaba da bibiyarka da saka ido akan irin kudaden da kake gani koh zakayi amfani dasu koh zakamin zancensu ama sai naga ba abinda ya chanza daga yanda kake amfani da kudi.

Haka muka bada aikin a sace mana kai don kaika kunqiya sbd mu samu ka shiga cikinmu sosai kuma da cikin hayyacinka ama nsn ma bamuci nasara ba don wanda muka Bawa aikin ya mutu kuma daga nan muka fara shirye²n gama makaranta har muka bar jami'a bamuyi nasarar saka a kunqiya da saninka ba ama bamu daina amfani da ruhinka ba.NYSC mu kuma ya kasance ba waje daya ba sai daga baya aiki da zama ya kara hadamu a nan Kaduna.Tun ranar daka kira ZEE akan aikin da zata maka akan DIJA nida kunqiya muke cikin farinciki don burinmu dama bai wuce kayi aure ba a lokaci yanda zamuyi amfani da matarka koh 'ya'yanka.

Ka shiga takarar Governor ta taimakon kunqiya don na tabbata da kudin kunqiya kayi amfani wannan lokacin harka samu kujerar governor ni kuma ka nadani deputy ka abinda ba'a cika samu ba a Nigeria both Governor da deputy su kasance addini daya dukda ba laifi bane hakan.Mun samu goyon bayan jama'a sosai a shekara daya dakayi akan kujerar mulki"

"Ina ka kaimi Dija?"

King ya tambayeshi cikin bacin rai,zuciyarsa sai tafasa take yana wani irin nishi,ji yake kamar ya shake AA saide yana kokarin danne zuciyarsa saboda yasan inda matarsa take

"Matarka da kyawawan en biyunka da hannuna na mikasu kunqiya a lokacinda aka ciro matasu koh kallonsu baka samu damaryi ba sannan bada aikin a kashemin kai don na gaji da irin yanda kunqiya ke daukaka a kodayaushe,Nina kawoka kunqiya ama koda na buqaci zama governor kunqiya bata bani wannan damar ba sai kai,kasan yanda nakeji a raina,kasan yanda na tsaneka tun muna jami'a saboda yanda koyaushe kake wuceni a komai,koyaushe nake kasancewa a kasan ka shiyasa na saka trailer tabi takan motarka lokacinda ka fito daga asibiti bayan matarka ta haihu zakaje gida.

Har video yanda trailer tabi takan motarka an turomin na gani, yanda motar tayi ba yanda za'ayi kayi rai.Daga nan na bude sabon shafin rayuwa na hau kan kujerarka nayi rikon kwarya na cikon 3yrs da zakayi sannan na zama GOVERNOR AMINU ABDULSALAM KAITA ba mataimaki ba na tsawon shekara 3.

Bayan shekaru 6 da har na shafeka a babin rayuwata,ina murza duniyata yanda nakeso,ina ganin yanxu babu wanda yamin zarra koh ya fini kwatsam sai lbryn dawowarka naji"

Tasowa yayi daga kan kujerar dayake ya dawo kusada gadon King inda yake zaune yana sauraronsa cikeda al'ajabi,matso da fuskarsa yayi kusada ta King suna kallon juna ido cikin ido

"Nayi bakin cikin dawowarka kuma ina kanyi saide zan baka zabi daya cikin abubuwan dazan lissafa maka.Koh ka amince da buqatar kunqiya na zame mana shugaba kamar yanda kakeson zama shugaban al'umma,ka tsira da ranka, matarka da surukanka.

Koh kuma kaki amincewa da zama shugaban Kunqiya ka tsira da ranka don kunqiya bazata iya kasheka ba ama ni tabbas sai naga bayanka yanda wannan karan zan kasheka da hannuna tareda matarka da surukanka wato iyayen matarka.

Zabi ya rage naka kuma ina buqatar jin zabinka ayau sbd gobe zan kammala dukkan shirina akanka........

"Na amince"

"Ka amince dame?"

"Na zama shugaban ama sai naga Dija da iyayenta da idona na tabbatar da suna raye kamar yanda ka fada tukun"

"Hahahaha..nasani daman,nasan zaka amince.Karka damu gobe zan kaika har inda suke ama inaso a hanyarmu ta zuwa airport ka kwantar da hankali ka saki jikinka yanda jama'a bazasu kawo zargin komai a ransu ba.Don't evr try to make any foolishness"

Bai kara magana ba King ya mayarda kansa dake masa ciwo kan pillow yana tunanin yanda akayi yazo hannun AA shi kuma AA ya fice tareda rufe kofar da Key.

_WASHEGARI_

Wani guard ne ya kawowa King kayan sawa da abinci akan yayi wanka shirya,toilet ya shiga don yin wanka dakyar sbd yanda kansa ke bala'in masa ciwo,ga rashin bacci,ga tunanin duk ya taru yay masa yawa. Haka nan ya shirya cikin kayanda suka kawo mishi bayan 30mins guard din ya dawo da gun a hannunsa ya titsa keyar King suka fice a gidan inda suka shiga black tinted car dake Parke a kofar karamin gidan dake cen bayan gari.

A airport suka hadu da AA shi kadai sai wasu guards dinsa su biyu suka shiga wani private jet sai ABIA STATE.

Suna sauka suka tararda motar da tazo daukarsu,shide King binsu kawai yakeyi har suka karasa anguwar da gidan yake wanda bashida nisa da airport din garin.

A wani daki na musamman aka sauke King,dakin da yafi kowanne tsaruwa a gidan kafin su gama aiwatar da yanda zasuyi zuwa gobe.....

COMMENTS
SHARE FISABILLAH
[1/6, 9:11 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

BY APHSERTEEN KHAIREE

ELEGANT ONLINE WRITERS

30

"I need my husband, I need people, I need some noises.Na gaji da kadaicin nan ina buqatar mijina, kace min ya dawo toh yana ina?Har yaushe wannan zaman zai kare,please take me back to him"

Kuka take sosai kamar ranta zai fita,tasa fuskarta tsakiyar guiwuwinta tanayi

"Ki kara hakuri DIJA insha Allahu komai yazo karshe,KING WILL RETURN to u soon kede ki cigaba dayi masa addu'a"

Dago rinannun idonta tayi tana kallonsa tace

"Ka fadamin gaskiyar abinda ke faruwa,kace min KING ya dawo ama meyasa haryanxu baizo gareni ba.Tsawon shekara 6 muna tsare a gidan tareda iyayena,kun hanamu 'yancin mu,kun katse mana rayuwarmu,kun rabani da abinda na haifa wanda haryau bansan kalarsu ba sannan kaki fadamin dalilin hakan.Zan kara rokanka abinda kullum nake roko a wajena,don Allah Ku kasheni na huta nasan kun kashe min yarana,kun kashemin mijina don Allah na rokeka nima ka kasheni kawai"

Har cikin ransa yakejin kukan nata, ficewa kawai yayi a dakin nan DIJA ta kara fashewa da sabon kukan mai ban tausayi.

_ABIA STATE_

Ihun da Fahima tasa bai sa DAVID dakatawa da abinda yakeyi ba,runtse idonta tayi tana karkarwa jikinta sai 6ari yakeyi hawaye na rige² a idonta.Yakai 20mins yana abu daya,yaso ya juyata ya shigeta ta gaba ama sanin kunqiya bata yarda da hakan ba inde mace ta shigo gidan nan toh saide suyi luwadi da ita.

Yana zare jikinsa yayi wurgi da ita ta fadi kasa gefen matar nan,yayi ficewarsa

Yana fita Fahima ta rarrafa kusada ZEE tana kuka ta mayar mata doguwar rigarda David ya yaga ta dukda bai rufe mata kirji ba ta rungumeta suna kuka tare.Suna cikin wannan yanayin AA ya shigo, kallo daya ya musu yasa dariya

"Wow,what a pleasant surprised. Who am I seeing? FAHIMA ALIYU,so kece yarinyar UCHENNA?"

Takowa yayi ya zauna kan kujerar da Fahima ta tashi yana kallonsu

"I must say,this time around am the luckiest person.Fahima Aliyu kamar kinsan plan dina a kanki kenan tun ranar da kika fara shigamin hanci da kudundune dukda rasa mahaifiyarki da kikayi.ER jaridar da bata sarewa right?

Hahahaha....yau ga labarai kala² sai wanda kika za6a,am sure yanxu kinsan wanene mahaifinki sai kuma yanxu zakisan wanene governor ki mai ci yanxu.Las_las kuma kisan wanene KING our next governor kuma shugaba ga wannan kunqiya tamu"

Zaro ido Fahima tayi tana kallonsa da mamaki

"Don't be surprised dear, na miki alkawari kafin ki mutu sai burinki kema ya cika na son sanin wanene King"

Yana dariyar mugunta ya taro har inda suke ya dago wannan matar zaune,sai nishi take tana numfashi dakyar

"Am so sorry,kin taka sawun barawo.Nida kaina bansan ya akayi ke kika zo gidan nan ba a maimakon DIJA,taki kaddarar kenan na tsawon 6yrs da kika rayu anan gidan.Am sorry once again"

Dagata sama yayi shima ya mannata a bango kamar yanda David yayiwa Zee, ya cire mata Jan zanin dake daure a jikinta.Runtse idanuwansu Zee da Fahima sukayi suna kuka har AA ya gama abinda zaiyi ya jefar da ita.

Ajiyar zuciya take ta saukewa alamun samun relief na azabar da takeji.Ya koma kan kujerar ya zauna

"Fahima Aliyu"

Bude idonta tayi tana kallonsa

"Ina neman yafiyarki na kashe miki mahaifiya,ni nayi amfani da wannan bitch din tawa ta hanyar blackmailing dinta da past d'inta.Saboda tana tsoron kar a bata mata image a matsayinta na first lady shiyasa tayi yanda na buqaceta ba tareda sanin wanene yake amfani da ita ba

Mikewa tsaye yayi yana murmushi yace

"Na barku lfy girls,am sure zuwa dare kema FAHIMA zaki fara karbar naki so be prepared"

Yana dariya ya fice a dakin,kuka sukayi sosai har saida suka gaji Dan kansu sukayi shiru

Matsowa Fahima tayi inda wannan matar ke kwance da alama baccin wahala ya kwasheta ta dauko zanin nata dake gefe ta rufe mata jikinta dashi,sai kuwa ta farka a firgice daman batayi nisa ba.Ajiyar zuciya ta sauke ganin Fahima ce

"Zaki iya tashi,inaso muyi magana?"

Fahima ta tambayeta,dakyar ta bude bakinta tace

"Bana iya zama"

Take idon Fahima ya tari kwalla cikin tausaya mata tace
Chapter 26 · 0% Book details