← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 36

Sashe 15

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

"O'o am so sorry dear, kinsan yanxu ne muke kan campaign da zarar an kammala primary election komai zai zo da sauki i promise you'll be having my full time just like before,kinji"

"Gaskiya nide bana sonka da siyasa wlh don de ka dage ne,kuma a ina kake samun kudin da kake campaign din dashi?"

Shiru yayi yana nazarin tambayarta

"Ba ina aiki ba Dija"

"I know your salary won't be enough"

"Waya fadamiki ana kashe kudi a campaign"

"Nayi bincike ne"

Jan hancinta yayi yace

"Karki damu muna samun tallafi daga manyan committee"

"Please bad'd'o am, don't put urself into mess.Komai zakayi kayi da iyakar gaskiyarka da kuma abinda yake halal a gareka gudun jefa kanka a matsala don ranar mu'allim dinmu yace mana duk abinda aka ginasa ta hanyar k'arya da haram baya tab'a tasiri"

Jikinsa ne yayi matuk'ar sanyi da maganganun nata..

Wani irin iska mai hucin zafi ya fesar daga hancinsa tunawa da shawarar Dijah,tabbas maganarta haka yake duk abinda aka ginasa da haram baya ta6a tasiri dukda bashida haryanxu ya kasa tabbatar da hallaci da rashin akan tarin dukiyar daya tsaya takara da shi a baya har ya samu dubbin goyon baya daga kan talakawa har zuwa manyan kasa.knocking kofarsa akayi yace

"Come in"

Zaki cikin jallabiyarsa fara kal ya shigo da sallamarsa bayan ya gaisheshi ya amsa masa

"Lafiya baka fito sallah ba?"

"Headache ama zansha drugs yanxu na d'an kwanta kafin anjima hope yau bbu wani schedules?"

"Allah ya sawwake,saide in P.A ya iso"

Jigina yayi da jikin gadonsa yace

"Ka zauna inason muyi magana"

"Okay" ya zauna kan cushion dake fuskantar King yana sauraron sa

"Menene tunaninka akan takarar nan?"

"All is well insha Allah"

"Kana ganin bbu wata matsala?"

"On my on view,babu ama zamu tattauna da P.A muji ya abin yake daga 6angarensa"

"Okay,that's all bari na dan huta"

Mikewa Zaki yayi yace

"A huta lafiya"

ya fice a dakin,tashi yayi ya kuma kan gadonsa ya zauna daga bakin gadon wajen side drower.Panadol ya dauko daga cikin drowern ya 6alli biyu ya kora da ruwan dake kan drower yana jin yanda kansa ke sara masa,kwakwalwarsa na buk'atar hutu da nutsuwa koh dan ya samu yayi tunani da kyau sbd abubuan dake gabansa dole ne ya d'inga samawa kansa nutsuwa.Ya kwanta tareda runtse idonsa,bacci yayi awon gaba dashi.

Bai farka ba sai quarter pass 9,Alhamdulillah ya tashi wase bbu ciwon kan sai na zuci wanda bazai ta6a denawa ba har sai ranar da burinsa ya cika.Toilet ya shiga saida yayi kusan 30mins yana k'alk'ale jikinsa tukun ya nad'a towel a k'ugunsa karami a hannunsa yana goge jikinsa da gashin kansa,shiryawa yayi cikin favourite d'insa black colour suit ya fito tsaf kamar bbu d'igon damuwa tattare dashi ya sauko downstairs inda tarin guards dinsa,Zaki da P.A ke zaman jiran saukowar tasa ya nufi dinning direct bayan ya amsa gaisuwar da suke mishi

P.A da Zaki ne suka mara masa baya,Zaki ya fara serving dinsa breakfast P.A kuma na tsaye daga gefe.Tea ya fara hada masa,sai chips da fry egg daya zuba masa a plate bayan Zaki ya gama zai bashi waje yaji yace mata ya zauna,zama yayi yana fuskantar King

"Ka tattauna da P.A akan maganar da na maka dazu?"

"Ehh munyi ama bari ka sake ji daga bakinsa"

Kujera ya nunawa P.A shima ya zauna ya kallesa alamar ya masa bayani

"Campaign dinmu na tafiya lfy sbd kullum muna k'ara samun magoya bayan election d'inka,kana da jama'a da suke son fitowarka takara sosai ama fah duk masu karamin karfine I mean talakawa gashi ba muda means din da zamu cigaba da campaigning, the little we have komai yayi k'asa wanda hakan zai iya sawa party ya zama weak duba da yanda Governor AA KAITA ke 6arin makauniya da kudi wanda yanxu shine abu mafi rinjaya wajen al'umma shiyasa duk wasu manya k'asa suna bayanshi hakan kuma ba karamin barazana bane"

Tsap King ya gama sauraron P.A yana yiwa maganganunsa fashin baki dalla² yace

"Idan muka chanza party fah?"

"How can this be possible Sir?" P.A ya tambaya

"Party president fah?"

"You mean ANP?"

"Yes"

"Already suna da gubernatorial candidates dinsu daya fara campaigning kusan shekara kenan"

Shiru King yayi ya cigaba da cin abincinsa,shima P.A bai kara magana ba harya gama ya dau tissue ya goge bakinsa.Fita yayi gurds dinsa suka mara masa baya sai P.A dake gefensa don yanason kaiwa babban malaminsa SHEIKH IMAM MOHAMMED SULEIMAN ziyara..

_ZEE KAITA_

Gudu take shararawa cikin rashin nutsuwar jiki dana zuciya tareda tunani kala² a ranta hatta mayafin ma ajiyeshi tayi gefe gashi bbu gashin attachment d'in da take sawa akanta sai kwakwuidon kashinta da baifi tafin hannun ba a waje

"Who's behind all this,waye yake min haka,waye yake blackmailing d'ina? An sani nayi aiki ba tareda sanin wanda ya sani ba ama nasan koma waye he's close to me wanda yasan sirrina ne yasan komai nawa since from day1 yanxu kuma ance nayi freeing yaron.Sun sani kidnapping yaronta da mamanta daga baya kuma sun sace mamar sun kashe,why why"

Abinda yafi d'aure mata kai shine tho duk aikin mutum daya ne koh kua wani daban ne ya sata ta sake yaron

Ita kadai take magana kamar zautacciya tana rough driving har ta iso wani uncompleted factory wanda yake kamar store cikin wata anguwa da take kamar bayan gari sbd rashin jama'a ga koh ena duhu bbu haske wuta,parking tayi daga cen nesa ta fito daga motar cikin sauri ta karaso wajen.

Ta dade tana knocking shiru,tunawa da thugs d'in da tasa bazasu bude kofar ba inde ba waya ta musu ba ita shaf tama manta

"Ohh shit"

haka nn ta kara komawa motar ta dauko wayarta cikin sauri har rigarta na hard'eta kamar zata fadi.Kiran wayansu dukka ta dingayi ama shiru yanata ringing ba'a picking, inda ranta yayi dubu toh duk a 6ace yake dakyar d'aya daga cikinsu ta samu yay picking cikin muryar layi yace

"Alooo wai wani d'an shegiyar ne,don mai cin uwarsa zai dameni ina cen Paris tareda masoyiyata"

Tsawa ta daka mishi a wayar

"Kai dan iska kazo ka budemin ZEE KAITA ce"

"Oh oh sorry sorry"

Yana layin maye yazo ya bude mata sai faman sorry sorry yake ce mata sauran kua koh kansu bbu duk sunsha sunyi tatil.

Salim kuwa har yayi baccinsa a k'asan wajen, tun yana musu kuka harya hakura duk ya rame ya lalace

Cikin takaicin en daban Zee ta shiga tana zaginsu oho basu san ma tanayi ba sai dayan dake layi bai gama cakewa bane yake cika ta da sorry

d'aukar salim dake bacci tayi ta fito dashi.Haske ta gani kamar flash din camera cikin tsoro ta fara waigawa ama bbu alamun kuwa a wajen haka ta doshi mota tasa Salim a baya lokacin har 12 ta wuce ta bar wajen dashi

Tana hawa titi kira ya shigo wayarta da private number tayi picking cikin sauri

"Ki ajiyeshi a wajen ki wuce"

parking tayi a gefen titi kamar zatayi kuka duk ta rud'e ta fito a motar ta bude inda tasa Salim a baya tana ta6ashi kua ya tashi daga baccin ta fito dashi kan titi da yake shiru tayi ta waige² ama bataga kua ba ita de ta barshi a wajen taja motarta cikin wani wawan speed wanda ikon Allah ne kawai ya kaita gida,da mmk securities din government house din ke kallonta bbu damar tambayar daga ina take hakan nn suka bude mata ta shiga lokacin har AA ya koma dakinsa ama yana ganin time din data shigo yay murmushi kawai

A wannan daren a ranar da King yayi magana da Fahima kenan bayan su AA sun wuce yasa aka mayar da Fahima gidanta da aka ajiye mata securities biyu,tana zaune a parlor ta kasa shiga ciki har 12:30 taji knocking kofar parlor

Jikinta a sanyaye ta tashi ta bude inda tayi arba da Salim dinta a kafadar security, cikin tsantsar murna da farinciki ta kar6eshi sai kuma kuka tana kissing dinsa all ova his face da wani irin shauki na kewa.

Wanka ta mishi da ruwan zafi ta gaggasa mishi jikinsa tanayi tana kuka tana gamawa ya koma baccin wahala ta shimfide sa a gado tana kallonsa.

Bata runtsa ba a wnn daren har kusan asuba tana nafilfilo da addua neman tsari da taimakon Allah akan aikin da zata sa a gaba tareda nemawa mahaifiyarta gafara wajen ubangiji da yiwa mahaifinta adduar neman shiriya.

Haka ta tashi da safe da wani irin karfin guiwa ta shirya Salim da kanta ba tareda tsoro ba tayi dropping dinsa a school ta wuce aiki itama with full confidence and believed akan maganar King daya ce mata she's free and safe

5 ta tashi a office da tarin gajiyar aikin da tasha yau ta biya school dinsu Salim dama sai yamma suke tashi sbd school din hade take da islamiyya,bata tarar da guards din da suna kwana tare jiya a gidan ba sai kawai ta ta6e bakinta ta wuce a ranta tace

"Allah ne zai cigaba da karemu ba wasu katti ba" (ta shaqa🤭)

Tana shiga parlor ta zube akan kujera tana rage gajiya

"Jeka cire uniform dinki salim"

"OK mummy"

ya amsa mata ya wuce dakinsa,sai tajita kamar ta zauna kan takardu ta tashi ta duba.Wani katon envelop ta gani an rubuta

"NEW PACKAGE FOR YOU"

bude envelope tayi dauke ta addua a bakinta da tunani,what's again? ta ciro wasu pictures, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai take ambata.Photon King ne a bakin maqabarta cikin farar shadda da gabanta ya 6aci da jini,daya papern ciki ta ciro taga an rubuta

"Who's King?"

Samun kanta tayi da maimaita Kalmar

"waye king?"

Sanin batada mai bata amsa a yanxu kuma tana buqatar wnn amsa koh ta wani hali

"ZAKI! yes shine kadai mafita,a wajensa kadai zan samu wnn amsar ama tayaya?"

"Mummy mummy yunwa nakeji"

Salim ya fada YANA ta6ata sai lokacin ta dawo hayyacinta

"Laa mummy kinga photo wani da jini,shine ya yanka Mamin mu koh? Na ganta a kwance cikin jini"

Sai yasa kuka tunawa da Maminsa,rungumeshi tayi itama tasa kukan suka hau rerawa tare....

😤🤧I need pepper soup, this catarrh don tire me aswear
[1/6, 9:06 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
Chapter 15 · 0% Book details