← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 36

Sashe 18

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

Guard din ya fadamata haba kamar an mata bushara da gidan aljanna haka taji don dadi,ta wani kara sauke wuyan rigarta da yake off shoulder mayafin dama oneside ta yafashi sai er mini bag dinta a daya hannu ta haura sama cikin wani tako mai jan hankali,koh knocking batayi ba ta bude kofar kanta tsaye

Yana nn a kwance haryanxu idonsa a rufe tayi sallama karaso har inda yake,ciki² ya amsa mata still bai dago ba kuma bai bude idonsa ba.Tsaya tayi tana binsa da wani mayen kallo from head to toe,singlet ne jikinsa sai three quarter har wani hadiye yawo take don nn take jikinta ya bata wani irin sign

Sarai YANA kallonta ta wutsiyar ido ama yaki koda motsawa a wajen ita kuma hakan ya bata daman kare masa kallo tanaji kamar ta kwanta a kirjinsa a yanda yake kwancen,hannun kujerar ta zauna wajen kafarsa tace

"Hy king"

Sai lokacin ya bude idonsa yana dan lumshesu yana mata wani irin kallo daya kara narkar da ita,a hankali kamar wanda bayason yin maganar yace

"Zee how u?"

Mayfinta ta ajiye kan table da jakarta tana gyara zamanta akan hannun kujerar har kafarsa na shafan bayanta ta kwantar da kanta jikin kujerar tana mishi wani jarabben kallo

"Am good my King,ya hakuri?"

Kafin ya bata amsa yaji hannunta kan yatsun kafarsa tana shafawa zuwa tafin kafarsa,bai hanata ba kuma bai tanka ba snn bai tashi daga kwanciyar ba ya kyaleta tanayi.Ita kuma ganin mai gwaleta ba yasata jin wani irin dadi har ranta suka kafe juna da ido ta cigaba da shafa kafar tasa har kan wajen sangalalin inda gashi yake luff a kwance

Lumshe idonsa kawai yayi,ya rabu da ita, hakan ya mata dadi sosai tana ganin yau ta taki babbar sa'a sai ta zame daga hannun kujerar ta daga kafafun nasa ta zauna akan kujerar dakyau tare da daura kafarsa akan cinyarta.

"What are you trying to do"

Ta tsinkayi muryar King daya bude ido yana kallonta,daga kai tayi ta kalleshi tayi dan murmushi ta wani langwabe kai akan kujerar tana lumshe ido

Knocking kofar parlor aka fara Wanda yasa Zee zubara ta mike ba shiri,murmushi king yayi yana kallonta sai lokacin ya tashi daga kwanciyar ita kuwa tuni ta dau mayafinta da jaka zatayi hanyar kofa

"Five star room 102 tomorrow at 9"

Ya fada,juyawa tayi kafin tayi magana yacewa mai knocking din

"Come in"

Dole ta tsuke bakinta,Zaki ya shigo da sallama a bakinsa wani banzan kallo yayi mata ya dauke kansa ita kuwa da fice kawai tanajin wani irin farinciki mara misaltuwa....

Sorry kunji ni shiru 🙏🏻🙏🏻

More comments more typing😎
[1/6, 9:07 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

21
"Where av u been,na kira wayarka bakayi picking ba?"

"Sorry King,naje checking wnn guys din da muka samu ne.They're very hard to break don haryanxu sunk'i bada had'in kai kuma kace mubi dasu a hankali and that will not be possible"

Shiru King yayi na en seconds tukunna yace

"Ku musu duk abinda ya dace"

"Okay"

"P.A na downstairs, yanason ganinka"

"Lemme fresh up,ina zuwa"

"A fito lafiya"

Fita Zaki yayi sai da King ya debi kusan 10mins a zaune tukunna ya tashi ya shige bedroom dinsa.Bayan 30mins ya fito cikin shiri wani voile yasa cream color kansa bbu hula ya gyara gashin sai sheki yake,takalminsa da wrist watch kalan kayansa,guards dinsa da P.A suka gaishesa ya amsa ba yabo ba fallasa bayan ya zauna akan cushion P.A ya karaso kusada shi da takarda a hannu na schedules dinsu na yau ya fara masa bayani

"Kamar yanda muka tsara zamu kaiwa gidan marayu ziyara yau that's will bayan sallar la'asar,gobe kuma zamuyi visiting kasuwanni koda biyu.Ranar Wednesday kana da interview da Daily trust TV"

"Allah ya kaimu"

King yace tareda mikewa sbd kiran sallar la'asar da akeyi suka fice dukkansu don gabatar da ita.Suna idarwa Zaki yacewa daya daga cikin guards din

"Get the cars ready"

Koh kafin King ya gama gaisawa da jama'ar da sukayi sallah tare har an shirya motocin shi kawai ake jira,ya shiga gidan baya P.A a gefe sai Zaki da driver a gaba sauran guards din kuma suka shiga sauran suma. P.A na mishi bayani kan tsare²nsu,King kuwa kallon garin kawai yake da d'an chanje²n da aka samu sai yaga garin ya chanza mishi gabadaya.

"Kaduna has really changed"

King yace har lokacin yana kallon hanya,Zaki ne ya bashi amsa

"Yes it has my King but it's still also belongs to you"

Murmushin gefen baki King yayi bai sake magana ba hakama P.A sai driver dake aikinsa,suna cikin tafiya driver yayiwa Zaki wani magana wanda yasa Zaki juyawa ya kalli King yace

"It seems we have company, koh zamu juya?"

Kwantar da kansa King yayi ba tareda nuna damuwa ba yace

"No,Kyalesu suyi"

Waya Zaki ya ciro daga aljihunsa yasa a kunne

"Keep moving but shine ur eyes"

Ya mayarda wayar aljihunsa har suka iso orphanage din inda suka zazzaga snn King ya bada tallafin mak'ud'an kudade wanda yasa P.A bayan sun shiga mota zasu koma gida magana

"Sir,account dinmu yayi kasa sosai fah gashi gobe zamuje kasuwa"

"Ina kace zamuje?"

King ya tambayi P.A

"Kasuwa"

Bai sake magana ba har suka iso gida.

_FU'AD_

Dawowarsa knn daga office ya baje a parlor yana sassauta tie dinsa inda Salim ya taho da gudu yana masa oyoyo,kannensa emmata biyu Abidah da Siyama na zaune a parlor da waya kowacce a hannunta suka mishi sannu da zuwa

"Yawwa emmata Mummy, ina mummy take?"

"Tana upstairs bari na kawo maka ruwa bro"

Siyama ta amsa tareda mikewa ta nufi kitchen,Abidah da hankalinta ke kan waya ne ta d'ago ta sauri tana

"Bro bro kaga news din dake trending a social media kuwa,wow gsky mom Salim ta burgeni"

Tsaki Fu'ad yayi yace

"Ai daman ke shashasha ce,me abin burgewa a aikin sa kai a had'ari,aikinda zai rabaka da masoyanka"

Ya fada with deep pain in his heart,shiru Abidah tayi bata sake magana ba don ta harbu jirgin Yayan nata

"Ai sai taje cen ta karata tunda abinda ta zab'awa kanta knn,kai kuma daman koh kusa koh alama banasoji na sakeji ka taka inda take tunda Allah ya tseratar dakai da yaron nn toh ya kare mata ita kadai.Duk tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa yake duka"

Suka tsinkayi muryar Mummy dake saukowa daga stairs, kasha shan ruwan da Siyama ta kawo mishi yayi kawai ya dauki jakarsa da rigar suit dinsa ya shige ciki hanyar dakinsa.Salim kuwa shiru yayi jikinsa yay sanyi don tunda yaji Aunty Abidah ta kama sunan Mom dinsa yasan akanta ake magana ga yaron da shegen wayo

Koda Fu'ad ya shiga dakinsa kwanciya kawai yayi kan gado cikeda damuwa da kewar matarsa,don har gobe bazai dena sonta da murad'in sake rayuwa da ita ba.

"Why Fahima why,meyasa kika zabi nisanta kanki dani,why do you always choose ova me,me kike nema a rayuwa da bazan iya miki ba,mesa bazaki tausayawa halinda zuqatanmu suke ciki ba? nasan kema kina cikin damuwa ama strong head dinki yayi yawa.Why....?"

Hawaye yake kamar karamin yaro yana jin wani irin rad'ad'i a ransa.

_FAHIMA_

"Assalama alaikum"

"Wa'alaikis Salam Fahima Aliyu sannu da zua, har kin k'araso knn"

Yace da fara'a a fuskarsa don ba karamin burgeshi daman take ba akan aikinta,hatta hiran da tayi da AA ya daya daga cikin wanda suka nuna jindadinsu akan tambayoyin da tayiwa AA din ta hanyar suburbud'o comments da jinjina a duk shafukan zumuntar da aka daura shirin live.Murmushi ta mishi tace

"Yawwa Magaji Ilyas right?"

"Sure sure,ka guri zauna mana"

Yana nuna mata kujera dake gaban desk dinsa sai fara'a yake zabgawa irin yau gashi ga cele dinnan don Fahima yanxu kam ta zama celebrity duk inda ta wuce sai ta gaisa da jama'a wasu ma har suyi requesting selfie da ita. (Wato yanxu de abu kalilan zakayi ka zama cele,kana daga kan gadonka ma in Allah ya daukaka akan wani abu sai kaga ka zama 🤭Allah ya kara soyayyarmu a zuk'atan masoyanmu ya bamu ikon nishad'antar da masoyanmu)

Zama tayi akan kujerar tana fuskantarshi ta ciro pen da wani dan karamin littafi mai kyau ajakarta

"How can help you"

Ya tambayeta,dan clear d'in throat tayi tace

"Thanks,shekararka nawa kana aiki a asibitin nn?"

"8 good years"

"Daga wani irin aiki ka fara?"

"Da farko na fara daga mai bada kati na kusan shekara 1 da rabi har Allah yayi daga baya na kuma registrar wato duk wani file na patients ni nake adana shi har kawo yanxu"

"Masha Allah,Allah ya taimaka ya k'ara daukaka"

Sosai yaji dadin addu'arta YANA murmushi yace

"Ameen ameen nagode kema ina miki fatan haka"

"Shekara 6 da suka wuce matar tsohon governor ALIYU MOHAMMED GIWA tayi ante natal dinta a nn asibita har takai matakin haihuwa kuma duk anan asibitin tayi koh zaka iya tuna lokacin"

"Tabbas haka yake,duk wani tsohon staff kai harma da sabon yana da wnn labarin don haihuwar wnn baiwar Allah ya kasance daya daga cikin kundun tarihi na wnn asibiti"

Cikin jindadin samun had'in kai da bayanai masu matuk'ar mahimmanci daga wajensa Fahima tace

"Koh meyasa haka?"

D'an furzar da numfashi yayi yace

"Sbd wani abu daya faru mai kamar almara koh tatsuniya,kamar a shirin film koh irin qirqirarrun labaran nn na litattafai.Abinda ya gigita asibitin nn da ma'aikatar cikinta gabadaya suka shiga cikin rudu da tashin hankali,yaso tarnishing image din asibitin.Tabbas wnn rana ta kasance unforgettable moments,abun was just unbelievable inde ba agaban idonka ya faru ba"

D'an katseshi Fahima tayi

"Koh zaka d'an takaita please ka fadamin ainihin abinda ya faru a wnn ranar"

"Tho nide kamar yanda kika sani nine in charge na kowanni irin file na patients a asibitin nn,Iyalin Gov,Mohammed GIWA wanda kowa yafi sani da King a nn take awonta har zuwa lokacin haihuwarta.Allah sarki mace mai fara'a,taimako da son jama'a kamar mijinta don koyaushe tazo asibitin nn sai tabi kowanne staff da mishi ihsani shiyasa duk cikin asibiti bbu wanda bai santa ba ga barkwanci sam bata da girman kai.Kasancewarta matar Governor a lokacin baisa ta raina asibitin nn da jama'ar cikinsa ba,Allah ya jikanta da Rahma"

Ya fada cikin jimami,Fahima ta duk ta tarkata nutsuwarta akanshi tace

"A nn ta rasu ne?"
Chapter 18 · 0% Book details