← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 36

Sashe 17

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Fahima this is what av been warning you,kinde gani koh shi da kansa King din bai tsira ba balle ke kice zakiyi kutse cikin hakarsu.Am warning you for the last time,stay out of it"

"Sir please karmu sare, remember a real journalist can take any risk just to find a true information about anything, please ka bani goyon baya inaso gabatar da wani program"

"Wani irin program?"

"Hira da dukkan wani gubernatorial candidates na kowanni party harda Governor AA KAITA"

Shiru yayi na en seconds yana tunani

"That will not be a problem, zaki iyayi but I warn you again and again Fahima Aliyu be very careful. Infact shawarar da zan baki ma shine go home,go back to ur husband,tell him how much u missed him and hug ur son yafi miki wnn hatsarin da kike kokarin jefa kanki"

Murmushi tayi tace

"Don't worry,I'll be fine insha Allah

_KING_

Sai kai kawo yakeyi a asibiti kana ganinsa kasan yana cikin mummunan tashin hankali,idonsa ya kada yayi jaa innocent soul are just dying duk akansa.Guards dinsa hudu boom ya tashi dasu yau a gaban idonsa ga sauran mutanen da sukaji rauni kusan mutane 6 Wanda tsautsayi ya biyo dasu,hango motocin King yasasu zua su nuna mishi kaunarsu kafin su karaso boom din ya tashi shine ya shafesu wasu sun rasa hannu wasu kafa

" Innalillahi wa inna ilayhi rajiun,Allahumma ajirni fi musibati" yaketa maimaitawa

"Who's behind all this,me suke nema dani"

Fitowar doctors ne ya katse masa tunani ya taho wajensu yana

"Ya jikin nasu"

Daya daga cikin doctors dinne ya amsa

"Five are fine,saide ayi hakuri an rasa daya daga cikinsu"

Wani jiri ne yaji yana kokarin kayar dashi sai doctors dinne suka taimaka suka rikeshi

"Calm down,you need rest"

Cikin 6acin rai da tururin zuciya king yace

"Tayaya zan huta bayan innocent lives are dying day by day duk a kaina"

Kuka yasa kamar yaro don ya kasa controlling kansa,take yaji kansa na juyawa ya fara ganin dishi².Zaki daya shigo yanxu tareda wasu police ya taho da sauri ganin halin da King yake ciki ya fadi jikinsa,cikin ihu yacewa doctors din

"Save him now,karku bari ya mutu" (tohpa doctors kunga ta kanku 🙆🏻‍♀️)

Da kansa ya ciccibi King abinka da garjeje ga kuma training don kana ganinsa kaga irin thugs dinnan en daba majiya karfi,nurses suka nunamasa dakin da zaisa shi doctors suka rufu kansa

_AA KAITA_

Yana zaune a kan cushions din dake office dinsa da katuwar kwalbar non_alcoholic wine yana sha

"Am confused David,am really confuse idan har na aiwatar da aikin da aka sani akan King tho tabbas zan rasa kujerata"

Wani irin dariya Wanda aka kira da David din yayi yace

"Hakama in bakayi aikin ba zaka rasa kujerar ba,so you have no choice"

"Ina bazaiyu ba,ban shirya barin Government house yanxu ba.Dolene nayi wani abu akai idan kua zan rasa saide kowa ya rasa wallahi"

"AA KAITA lemme tell you sumtin that u already know,ur success belongs to King, u can't be successful without him,we all need him now so don't try koda wasa kace zakaga bayansa am warning you as a friend"

Ya nuna masa kujerar aiki dake office din

"This chair belongs to him"

Comments and share fisabillah 🙏🏻🙏🏻
[1/6, 9:07 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

ELEGANT ONLINE WRITERS

20

Breaking news da aka sa a TV ne ya dauke musu hankali daga hiran da suke

"AA hope you're not the one?"

Cewar David yana kallon AA da jiran karin bayani,murmushi AA yayi yace

"Kaima kasan bazan cutar dashi ba maybe sauran abokan adawa ne kasan de siyasa"

"Hmmm,better not"

Bangaren King kuwa doctors sun rufu akanshi ana bashi taimakon gaggawa har suka samu da taimakon ALLAH numfashinsa ya daidaita,ama saida suka rikeshi kwana biyu a asibitin don yana buk'atar bedrest dukda ba haka ya so ba Zaki ya k'afe akan baza'a sallameshi ba har saiya huta, haka ya tura Zaki da guards dinsa wajen en uwan wanda boom din ya shafa da wanda ya rasa ransa dakyar suka hakura da toshiyar bakin mak'udan kud'ad'e tukunna suka yarda aka bar zancen.Bayan kwana biyu suka kuma gida cikeda alhinin abinda ya faru don kwata² bayason abinda zai shafi innocent lives akanshi har yashi siyasar ma ta fice mishi a rai gaba daya tunaninsa yanxu kawai Dijansa.

An turawa AA katin gayyata na hira da suke son yi dashi daga wajen aikinsu Fahima na Daily trust ya kuma amsa gayyatarsu.

_Wednesday 2:00pm_
Ta kame cikin shigarta na suit din mata brown color sai d'an baby hijab dinta tayi kyau sosai,AA KAITA na gefenta cikin manyan kaya shaddarsa fara kal sai maiko take harda binjima ya kafa hula akansa Wanda ya fito a asalin bakatsinansa,skin dinnan sai shekin take na jindadi,mulki da daular da yake ciki

"Good day ladies and gentle men,welcome to the live TV show with our Excellency Governor AA KAITA on DTN studio in Kaduna Nigeria.I FAHIMA ALIYU will present"

Ta juya dubanta daga camera ta mayar kan AA cikin kwarewa akan aikinta tace

"Barka da zua excellency, muna godiya da amsa gayyatarmu da fatan zamu samu dukkan hadin kanka wajen amsa mana dubbin tamboyoyin da al'umma da masu sauraron zasu so jin hak'ik'anin gaskiya"

D'an clearing throat dinsa AA yayi cikin dakewa na masu makumi a hannu yace

"Insha Allah"

"Thanks,Kamar yanda kowa yasan wanene AA KAITA right from the beginning da kuma irin kokarin da jajircewarka akan aikinka. Masu kallo zasu so sanin menene ainihin halak'arka da former governor wato ALIYU MOHAMMED GIWA probably known as KING?"

Ji yayi kamar ta soki jin sunan King complete,d'aurewa yayi ya kwakwalo murmushin dole yana kallon camera

"ALIYU GIWA ya kasance best friend d'ina ina nufin amini na kwarai tun muna jami'a"

"So,yanxu fah?"

Shiru yayi na en seconds tukunna yace

"Har gobe insha Allah"

"Masha Allah,a lokacin da ALIYU GIWA yake Governor ka kasance Deputy sa koh zamu iya sanin abinda ya faru harka samu rikon kwarya na tsawon shekara 2 kana na uku yanxu?"

"Wannan abu ne da kowa ya sani,I don't need to answer that"

"Hakane,tunda kace kai amininsa ne kenan kanada masaniya akan inda yake lokacin da aka nemesa dare daya aka rasa?"

"Banida masaniya"

"Woww kuma kace kai amininsa ne anyakuwa akwai wannan amintar tsakanin ku ache best friend naka kuma ur governor yashiga rudu da rashin lafiyar kusanta jirkicewar ƙwaƙwalwa amma kace bakada masaniyar inda yake?"

Zuba mata ido yayi dukda bacin raine a kwayar idanunsa baiyarda hakan ta bayyana a fuskarsa ba wani murmushin gefen baki yayi sannan yabita da fadin

"I have no idea,say ur last question"

Murmushin tamayar masa tace

"inaga Ni inada amsa ko hasashen yanda amsar take amintar da amini yake boyewa dayan amini gskiar abinda yake faruwa a cikinsa akwai rashin yarda,zamba cikin aminci, cin amana, dadai sauran muggun halaye saide anan nakasa gane shin wake cin dunduniyar daya a cikinku?"

Jijiyoyin goshin AA ne suka miqe sukayi rad'u rud'u idanunsa suka d'ad'a rinewa,a zuciyarta tace

"Anzo wajen"

Gyara zamanta tayi tace

"Kamar yanda kace last question, I have no choice dukda dubbin tamboyoyin dake bakina dole na tak'aita.Baka ganin zargi zai iya hawa kanka akan 6atansa sbd ka samu ka hau mulki?"

"Saide in kece zaki cusa musu wnn tunanin yanxu"

"Thank you so much for your time Excellency,anan muka kawo muku karshen wnn shiri sai ince sai mun mako na gaba inda zamu k'ara gayyato muku daya daga cikin gubernatorial candidates dinmu"

Tashi yayi gaba koh amsa godiyansu baiyi ba securities dinsa suka goyo masa baya suka bude masa bayan mota ya shige tare da P.A a gefensa

"Ina buk'atar kowanne movement dinta"

Yacewa P.A ba tareda ya kallesa ba

"Done"

Da fara'a a fuskarta Fahima ta doshi sauran ma'aikantan nasu dayan daga cikinsu ne yana fara'a yace

"Wow Fahima Aliyu you killed it,wallahi kin burgeni don nasan kua da tambayar nn a bakinsa kinga kin jawo attention din jama'a bari ma kigani"

Ya shiga Facebook a wayansa inda suka daura shirin live dubbin comments din jama'a

"Yes Nurraddeen haka mukeso dama"

Cewar Fahima sai murna take,Boss ne ya karaso inda take yace

"Weldone Fahima Aliyu am proud of you,samun jajirtacciyar da mara tsoro cikin ma'aikatan mu abu ne mai wuya.Allah ya taimaka ya kareki"

"Ameen Sir thank you so much"

Tattarawa tayi ta bar office sbd aikinta na gaba da takeson aiwatarwa,Health care hospital ta nufa direct dama ta samu contact din registrar asibitin..

_ZEE KAITA_

Tunda AA ya fadamata buk'atarsa ta shiga rud'u da tunani dukda abinda ta dade tana nema ne da mafarkin samu ama tayaya hakan zai faru,menene dalilin AA na sata wnn aikin kode cutar da King yakeson yi don har wani abu ya bata da zatasa a gabanta.Toh ko da hannun AA a 6atan King da matarsa ne? Ita kadai take yiwa kanta tambayar

"No,bazan taba yarda ka cutar dashi ba AA.Inason King son da bazan ta6a bari wani ya cutar dashi ba balle ni da hannuna, tabbas 6acewa Dija ni alheri ne a wajena snn sai kayi nadamar damar da ka bani akansa don zanyi amfani da ita wajen cimma nawa burin"

Shiryawa tayi cikin atamfarta lemon green dinkin gown tayi kyau sosai,mayafi,jaka da takalminta milk ratsin atamfar.Ita kadai ta fita don koh guards dinta da driver ce musu tayi bataso yau ta ita kadai zata fita

Cikin wani black tint car ta nufi anguwarsu King da sunan zataje mishi jajen abinda ya faru last two days.
Luckily kuwa ta sameshi a gida inda ta tarar da gurds dinsa guda biyu a parlor,Zaki bayanan ta tambayesu King daya guard din yace mata yana sama bari ya mishi magana kamar ta ce masa ya bari zataje saman da kanta sai kuma ta basar.

Yana kwance akan 3seater a parlornsa na sama idonsa a lumshe kamar mai bacci, guard din yayi knocking ya bashi izinin shigowa

"You've a visitor downstairs"

Ba tareda yabude idonsa ba yace

"Who's that?"

"First lady Zee KAITA "

"Kace ta karaso sama"

"OK"

"Meet him there"
Chapter 17 · 0% Book details