← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 36

Sashe 31

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaki ya amsa tare da gyara zaman cikin ladabi kamar ba tsohon d'an awawa ba yace

"Daman ina buqatar shawararka ne akan dawowar King shin kana ganin lokaci yayi da zai dawo gida koh kuma kana da wata shawara game da hakan?"

D'an gyaran murya Sheikh yayi snn yace

"A hangen da lissafin dawowar Aliyu yanxu ba shine mafita ba koh sbd batan iyalinsa zanzo ace kun tsananta bincike koh Allah zai taimaka inda rabon a sameta nima nn zanyi iya kokarina daga cikin d'an sanin da ubangiji ya bani wajen tayaku da addua gwargwadon iyawata.

Nan da wani d'an lokaci idan da rabon toh idan kuma bbu labarinsu sai a mishhi shirye²n dawowa. Allah ubangiji ya mana jagora"

"Bana tunanin tana raye"

Zaki ya fada kai tsaye,Kallon nazari Sheikh ya mishi

"Menene dalilinka na fadar haka?"

Sai lokacin Zaki ya tuna amsar daya bawa sheikh take ya basar yace

"Saboda tsawon lokacin da naga har yanxu bbu lbrinta"

Badon Sheikh ya gamsu ba yace

"Addua CE kadai mafita,Allah ya warware mana komai cikin sauki"

"Ameen,Maganar King din fah"

"Akoi wani Dan uwana dake Jidda da zama anan Saudi Arabia koh zan mishi maganar Aliyu ya kuma wajenshi da zama SBD shima babban malamine don Aliyu na buqatar karin ilimin addini kodan ya tsare kansa duniya da lahira"

Koda Zaki ya sanar da King shawarar da suka yanke da Sheikh bai ki ba don tunda akace masa bbu Dija yaji kasar ma ta fitaa ransa gabadaya.

Ji yayi hannun Zaki dake damke cikin nasa na motsawa kadan²,daga kai yayi da sauri yana kallon fuskar Zaki dake kokarin motsa idonsa nason budewa

Fitar numfashinsa ne ya fara sauyawa cikin sauri² yana kokawa da fitarsa.Bude kofar dakin akkayi inda doctor dake in charge ya shigo daman yaga motsin Zakin ta CCTV dake makale suna jiran farkawarsa at anytime

_AA KAITA_

Jansa a jiki Igbo nn ya dingayi har saida AA ya sake dashi hakama da lokacin tashinsa yayi ganin AA na zaune still a wajen ya sashi tambayarsa bazai tafi gida bane nn AA ya fadamasa shi bakone bashida wajen kwana

Inyamuri fah a tunaninsa yaga kudi kawai take ya Yankee shawarar kai AA gidansa ya kwana in yaso cikin dare ya yasheshi kawai don ya tabbata bazai rasa kudi koh abin kudin a jikin AA ba..........

COMMENTS
SHARE FISABILLAH 🥰
[1/6, 9:16 PM] +234 708 603 7570: RETURN OF THE KING

By APHSERTEEN KHAIREE

ELEGANT ONLINE WRITERS

_INA NEMAN AFUWARKU DA JINI SHIRU FOR COUPLE OF DAYS.WAYATA KE BANI HEADACHE AMA INSHA ALLAH KOMAI YAZO KARSHE DAGA YAU ZAKU CIGABA DA SAMUN UPDATES KULLUM_🙏🏻🙏🏻🙏🏻
_TABBAS RASHIN UPDATES AKAN LOKACI NASA NOVEL YA FITA A RAN FANS,INA MAI NEMAN AFUWARKU KU CIGABA DA HAKURI.INSHA ALLAH ZANYI IYAKAR KOKARINA WAJEN BAKU UPDATE KULLUM,KU CIGABA DA BANI KARFIN GUIWA DA HADIN KAI KAMAR YANDA KUKA SABA.I PROMISE THIS TIME AROUND I WON'T LET U DOWN_

JUMA'AT MUBARAK ❤️❤️

38

Wani k'azantaccen gida ne da gantsa kuka duk ta mishi ru6anya daga jikin bangon zuwa simintin dake kasan gidan wanda yake a faffashe.
Irin ginin nan ne da ake kira da face me I slap u wato dakuna na kallon juna a jere gashi kowanne daki d'an karamin generator Tiger na aiki daga bakin kofar sai kara kakeji koh ta ina ga hasken bulbs a kowanne kofar wanda ya taimaka ya haske gidan.Dakin iyamurin nn daya taimaka AA na daga karshen passage d'in kusada jnda toilets ke jere shiyasa dakinsa yafi na kowa wari

Tunda ya bude suka shiga AA ya toshe hancinsa sbd wari ama shi kua Ema koh a jikinsa da alamu ya saba kayansa.
Wata yamutsattsiyar katiface a dakin sai tilin kayansa dake ta tashin tsami a jibge daga gefe,su bucket da kayan kwanukan abinci duk yana ciki harda yar rishow dinsa na girki.
Kallon dakin AA yakeyi a kyamace wai yau shine zai kwana a cikin wannan kazantar

Bayan sun gama cin abincin da Ema ya siyo musu daga fastfood duk lissafinsa zai fanshe kudinsa a jikin AA.
Ruwa AA ya d'an watsa koda ya fito ji yayi jikinsa na wani yamyam sbd toilet d'in

Bayan sun kwanta AA ya kalli Ema yace

"Thank u so much my friend I really appreciate"

Dariya Ema yayi yana nuna masa babu komai snn AA a cigaba da magana

"Inason ka sake taimakona da wani abu"

"Ka fadi koma menene zan maka baka da damuwa"

"Zakaje min garinmu ne,ni yanxu bazan iya shiga ba don nasan ina cikin list wanted criminals yanxu"

Dan numfasawa Ema yayi yana mamaki decent person kamar AA ne wanted

"Karka damu ka fadamin koma menene zan maka shi"

"Inada wani gida boyayye a Kaduna bbu wanda yasan dashi.Anan nake ajiye dukiyata,shine nakso kaje ka balle gidan zan baka pin number safe dina inda tarin kudi yake da ni kaina bansan adadinsu ba but please ka rikemin ma'ana zan jiraka harka dawo then I promise u zan raba kudin nn biyu na baka rabi"

Wani murmushin gefen baki Ema yayi

"U don't have worry, trust me"

Washe gari suna tashi da safe Ema ya fara shirin tafiya,saide ya hada musu lafiyayyen breakfast AA yaci ya koshi sukayi sallama akan yana zuwa ayau zai jiyo ya dawo Abeokuta

Har park AA ya raka Ema yana daga masa hannu,wani killer smile Ema ya mishi
Motarsu na kokarin tashi AA dake gefe yaji cikinsa ya murd'a

D'an ya mutsa fuska yayi duk tunaninsa chanjin waje da abinci ne ama ina sai yyaji abin ya dado.Ema dake kallonsa yayi murmushi ya dauka dark glass ya toshe idonsa,wasa² AA saiga Abu na zama babba

Zubewarsa a qasa yayi daidai na tashin motarsu Ema suka bar park din,bye² yake yiwa AA dake zube a kasa yana dagawa Ema hannu alamar yana neman agaji

_KADUNA STATE_

Doctor na shigowa dakin da Zaki yake ya fara bashi taimakon gaggawa sbd numfashin sa dake fita da kyar.
King na rike da hannun Zaki shima kansa wani irin heavily breath yake saukewa

Cen sai sukaji Zaki yayi sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya,cikin sauri King ya kalli fuskarsa jin yanda hannun Zakin ya sake daga cikin nasa sai kuma ya maida kallonsa kan Doctor

"Ka dubashi mana"

King ya fada a tsawace

Ajiyar zuciya Doctor yayi cikin mutuwar jiki ya dafa King yana

"Am sorry,he's no more"

Ji yayi kamar an buga masa gudoma a tsakiyar kansa,duk wata gaba na jikinsa ta sake ya kasa motsa koda yatsan hannunsa.
Bakinsa nason furta wani abu ama ya kasa,kafe doctor kawai yayi da ido kamar wani shashasha

Ganin yanayin da King ya shiga yasa doctor rike kafadarsa ya fice dashi daga dakin inda guards dinsa ke tsaye yace musu

"Take him home,yana buqatar Hutu"

Mario ne ya riko King da mamakin shi kuwa kawai binso yakeyi da ido har suka saka shi a mota

Koda suka karaso gidan ma saida suka taimaka mishi wajen fito dashi daga mota suka kaishi har sama, Mario na bude bedroom din King idanunsu ya sarke dana juna

Sake shi Mario yayi tare da jayo kofar ya rufe. King dake tsaye daga bakin kofar ya kasa karasawa ciki, ya kasa gasgata abinda yaji dazu balle kuma wanda yake gani yanxu

Wani irin shock ya shiga na zuciya, jiki da kwakwalwa
Ji yayi numfashi na kokawa,kirjinsa na tsananta bugawa take jikinsa ya d'au rawa koh ta ina

_INDE NAGA HARYANXU MASOYA KING NA NAN INSHA ALLAH ZAN BAKU NA DARE YAU_

COMMENTS
SHARE FISABILLAH 🙏🏻🙏🏻
[1/6, 9:16 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

By
Aphserteen khairee

39

Ganin king na kokarin zubewa k'asa ya sata saurin karasowa gareshi ta riko kafadunsa suka zube durgushe a kasan.Runtse idanunsa da jikinsa ke rawa yayi,he can't believe what his eyes is seeing.
Yasan duk mafarki yake daga maganar Doctor har zuwa abinda yake gani a gabansa

Hugging dinsa tayi tightly tana shafa kansa,hawaye na rige²n fita a idonta na tausaya junansu for all his while da kaddara tasa suka nesanta da juna ba tare da sanin kowannensu na raye ba.

Lokacin da suka gudu daga gidan gonan, tafiya sukayi mai nisan gaske kafin su fito bakin titi.
Haka suka dinga tafiya suna hutawa har suka shigo cikin garin Kaduna

Koda su Babaji sukace mata su gudu su bar garin sai Dija taqi yarda tace musu saita tabbatar da abinda take zargi.
Sai ta tabbatar King baya raye tukunna zata bar garin Kaduna

Haka Dija dasu Babaji suka badda kama suka shigo har anguwar gangare inda tamfatsetsen gidan King yake.
Knocking din gate din sukayi fuskarsu rufe,koda Mai gadin aminin Babaji wanda shima ya tsofa ya bude ya tambayesu daga ina sai Dija ta bude masa fuskarta

Tsananin mamaki yasa Baba mai gadi zaro ido yana

" 'Yata daman kina raye?"

Dan waigawa Dija tayi taga bbu idon jama'a akansu tace

"Baba bari mu shiga"

Anan compound d'in gidan Dada ta zube sbd gajiya,Babaji kuwa rungume juna sukayi da baba mai gadi na murna sai Dija CE ta wuce entrance din da zai sadata da bangaren King abubuwa dayewa na dawo mata

Gidan na nn yanda ta barshi babu wani abu daya chanza,tunda ta shiga zuciyanta ke tsinkewa,kirjinta ke dukan uku² ga mamakinta na rashin ganin kowa kuma parlor a bude

Haka tayita kalle² na tsawon lokaci tana tsaye a parlor bbu alamar akoi mutum koh kuma anyi amfani da wajen a kwana biyun nn ama kuma ganin bbu kora yasata samun Dan karfin guiwa harta haura sama

Bedroom ta wuce direct,taga nn ma fes yake ama bbu alamar mutum.
Kallen² ta farayi koh zataga abinda zai tabbatar mata Bad'd'onta na raye ama bbu shi don daga kan kayansa har man shafawa tabbas bazata taba mantawa ba dukka wanda ta sani ne.
Babu wani abu sabo

Hawaye masu zafi ne suka gangaro idonta na sarewa,ta juya zata fita daga dakin knn sai ta hango towel dinsa akan cushion dake dakin,cikin sauri tasa hannu ta dauka tana tattabawa.

Jin danshi kadan a jiki na alamar ba dade da amfani dashi ba ya sata sakin murmushi
Chapter 31 · 0% Book details