← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 36

Sashe 35

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayi sanadin Iyayensa da yaransa jajirai biyu.A lokacinda AA KAITA yayi plan din sace mai dakin King da jajiran en biyunsa snn ya bada aikin kashe aikin a kashe King inda yasa trailer nabi takan motarsa wanda dakyar muka samu aka ceto King da taimakon Allah kuma Allah yayi kwanansa na gaba,shine muka fitar dashi kasar waje inda yayi jinyar shekara da shekaru ba tare da Sanin matarsa na raye ba don shi da kansa ya dauka ta mutu kamar yanda kowa ya dauka.
Na dauke ita matarsa daga asibitin da taimakon Doctor Sa'id na boyeta tare da iyayenta a gidan gonarsa dake bayan garin sbd sanin cewa inde wani yasan tana raye tabbas sai AA yasan yanda yayi ya cimma mummunar manufarsa akanta ama sai akayi rashin sa'a AA KAITA ya sace wata baiwar ALLAH da akayiwa aiki aka fitar mata da yaro daya mutu a cikinta wacce mijinta ya rasu take gaban Uwar mijinta.

A labarinta dana samu daga bakinta a asibiti da haryanxu take jinyar cutarda rayuwarta dasu AA KAITA da sauran en kunqiyarsu sukayi mata
Ta hanyar luwadi da ita na tsawon shekara 6 da take tsare a gidan tsafinsu duk suna tsammanin DIJAH ce matar King"

Hawaye Dija,Fahima,Zee da wasu daga cikin masu sauroron Zaki kawai sukeyi barinma Dijah da tsananin tausayin wnn baiwar Allah ya shigeta dukda bata ganta ba

Zaki ya cigaba

"SAUDAT ta kasance marainiyya,ta taso gaban kanin mahaifinta wanda bayan ya aurar da ita shima ya bar garin Kaduna.
Mijinta ya rasu tana da cikin wata 5 wanda tsananin damuwa da tunanin rashin mijinta nata ya haifar mata illa itada d'an cikinta ga rashin isheshen kulawa don tana gaban mahaifiyar mijin nata wacce itama da taimakon d'anta take rayuwa.
A ranar da ciwon ya turnik'e Saudat d'in aka kaita asibiti da taimakon mak'ota akace aiki za'a mata don yaron cikin ya mutu, ranar aka kai Dija haihuwa.
Kuma a binciken da mukayi a asibitin bbu wanda ya dawo don tambayar ita saudat d'in har yau duk tsawon shekarun da ta dauka a hannun azzaluman,Muna rokon court a cikin hukuncin da zatayiwa wnn mutane a kara sbd hakkin wnn baiwar Allah da sauran jama'a

Wani huci iska mai zafi ya fesar daga hancinsa cikin bacin rai

"AA KAITA yayi nasarar kai yaran King kunqiya"

Sai kuma yayi shiru yana aikawa AA wani irin kallo,ji yake inama zai iya da yau sai ya kusa halaka shi,King da kansa wasu abubuwan sai yau yake jinsu

Dija kuwa Kuka kawai takeyi kamar ranta zai fita su Fahima na tausarta dukda suma kukan sukeyi.....

Masoya Aphserteen khairee,masoya King 💃🏻💃🏻
Show some love and support.A garzayo ayi payment MATA AYAU salon na daban ne tabbas na shirya muku da sabon sanfurin baku nishadi Fanmily akan farashi mafi sauki 150 kacal

3140418863 First bank
Hafsat Yahaya
07086037570 evidence of payment
[1/6, 9:17 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

By
Aphserteen khairee

ELEGANT ONLINE WRITERS

ALHAMDULILLAH AM BACK AGAIN 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
_INSHA ALLAH ZUWA GOBE ZAKU SAMU KARASHEN LAST FREE PAGE NA MATA A YAU_
_A GARZAYO AYI PAYMENT MY BEAUTIFUL FIFUL_ 🥰
_contact me via 07086037570_

44

Take court ya rud'e da hayaniyar mutane,kowa sai jifan AA yake da kalaman Allah wadai saide alkali ya buga gudumarsa kusan sau 4 tukunna jama'a sukaja bakunansu suka tsuke

Registrar ne ya karb'i laptop d'in hannun Zaki sbd shirun da yayi wanda yake nuna alama ya gama maganarsa don ya kuma d'inke fuskar nn tamau kamar wanda bai taba darawa ba daman ya lafiyar kura balle tayi zawo

Gani da jin irin badakala da tuggun da AA ya jima yana yiwa aminin nasa ya karasa court kaurewa da zantuttuka nn wani dattijo ya tashi tsaye rai a bace yana

"Kai ku wannan yaro Allah ya tagayyaraka ya kacencana maka rayuwarku duniya da lahira,bakin haihuwa bakin asara,bakin mu'ayyabi,jikan qaruna,yayan fir'auna"

Gudumarsa alkali ya buga yiwa dattijon tsohon gagardin a court yake, ya kiyaye

"Kai dallah kyaleni,kaima kayi wani kikip dakai akan kujera nasan dakyar ka yanke masa hukuncin kisa tunda yanxu duniyar gabadaya ta zama ta shu'umai.
Gwanda nayi ta tsine masa har saiya zama alade mafi kaskancin dabba abin kyama da la'ana"

Nan fah dattijon nn ya d'inga zazzagawa AA zagi har saida securities suka fitar dashi daga dakin court koda ya fita waje inda ya tarar da dandazon jama'a da en jarida ya hau basu labari A_Z harda kari,yana kwakwulo hawaye yace

"Haka bak'aken mu'ayyaban nan suka saka yaran wannan Dan albarkan Kinsh suka dake a turmi suka kirbesu"

En jarida kuwa da jama'a an samu abinda akeso nan take labari ya fara yad'uwa a kafafen sadarwa game da Governor Dan takara kuma mai ci a yanxu tare da sauran en uwansa en kunqiya wanda har sunan Baban fitatciyar er jarida FAHIMA ALIYU saida ya fito tundaga sharrin da aka masa na farkon zuwansa garin Kaduna,wanda suka san labarin daman na kullace dashi.

Nan hayaniya ta kaure daga wajen FEDERAL HIGH COURT,jama'a suka fara

"A miko mana mu konasu,a miko mana mu konasu.Mu bazamu yarda ba².........

Wasa² sai ga gari ya dauka kowa da irin tofin Allah tsine da yakewa su AA.

Bangaren court kuwa Alkali ya yankewa su Baban Fahima,David,Jboy,suleguy life in prison tare da kwace dukkan wani abinda suka mallaka shi kuwa AA KAITA an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsa da laifuka mafi girma a cikinsu dukkan hakama sauran guards dinsu da aka kama dukka an yanke musu shekaru masu yawa a gidan yari tare da huro mai tsanani.

Alhamdulillah dukkan wani masoyin King da al'umma yake ambatawa,Dija dasu fahima kuwa hawayen farinciki suka d'ingayi wanda baki bazai taba iya misaltawa

Babu abinda ya sake karyarwa da jama'a zuqata sai da sukaga King ya kalli gabas yayi sujjada ga mahalliccinshi na tsawon mintuna yana hawaye jikinsa har rawa yakeyi wanda yasa jama'a da dama zubda nasu hawayen suma

Lalle dukkan tsanani yana tare da sauki haka kuma babu yanayi mai daurewa duk daren dad'ewa.Yah Rabbi karka kawo mana abinda bazai wuce ba,Allah ka tsarkake mana zuqatanmu,ka cire mana kyashi da hassada a cikinta ka sama mana kaunar junanmu.
Yah Allah kasa muyi koyi da kyawawan halayyen na shugaban mu Annabi Mohammed SAW,Yah Rabbi....

Kuka ne yaci karfinsa sosai wanda ya sashi kasa karasawa,AA kuwa dan kukan nadama kamar zai hadiye ransa,ji yake inama mutuwa zatayi gaba dashi a yanxu a nan tafe. Koh ba komai wnn hukuncin da aka yanke masa ya masa matukar dadi don baisan maiya rage masa ba anan duniya

Hattasu David saida jikinsu yayi sanyi sukayi mugun karaya,nan aka fita dasu cikin handcuffed dukkansu.
Suna fita kuwa jama'a suka hau jifansu kamar daman sun shirya hakan dakyar aka sakasu a mota

King na mikewa idanuwansu cikeda kwalla ya kalli masoyinsa na hakika,amininsa bilhakki sai wani irin murmushi mai dauke da tsantsan farin ciki ya subuce masa dukka hawayen dake idonsa

Baya farincikin wankesa a zarginsu AA kamar yanda yakeyi ganin Zakinsa a raye

_Alhamdulillahi bi ni'imatillahi kasiran_

Karasowa yayi gaban Zaki ya durgeshe inda yake zaune a kujerar yayi hugging dinsa tightly har saida Zaki yace

"Awwcchhh,Oga zaka karasani"

Cikin zolaya abinda bai taba ganin Zaki yayi ba wato wasa koh zolaya,nan dukkansu suka fashe da dariya harshi Zakin first time in history har dasu Dija na tayasu.Zee kuwa galala tayi tana kallon Zaki cikin mamaki ganin fusakarsa dauke da dariya,sai taga wani irin kyau da cikar haiba tartare dashi

Wani murmushi ne ya subuce mata bbu zato ( uhhmm uhmm Zakinmu de yafi karfin fyade,su kwartowa Zee 🤭🥱 au,Ashe ta tuba 🏃🏻‍♀️)

Masha Allah
Tho mutanena na dawo 🥱
Mu hade gobe,insha Allah 🏃🏻‍♀️
[1/6, 9:17 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

By
Aphserteen khairee

ELEGANT ONLINE WRITERS

_*LAST PAGE*_ 💃🏻💃🏻🤗

45

Kwatonto yanda zuk'atansu ke dilmiye da tsantsan farinciki ma bata baki ne barin ma shi kansa uban gayyar da inya juya nan yaga Dijansa hakama ga Zakinsa a kusada shi.Sai iyayensa da yake musu fata da rahmar ubangiji da ma duk wanda ya rigamu gidan gaskiya

Mutanen daya gama cire rai da sake rayuwa dasu sai gasu zagaye dashi cikin falala da ni'ima ta Rabbi mai jaraba bayinsa ta kowacce siga,Allah ya bamu ikon cinye kowacce irin jaraba a rayuwa yasa ya zama sanadiyyar shigarmu aljannah kenan.

Ga kuma nasarar da suka samu na durgusar da manyan azzalumai masu amfani da jinin al'umma don biyan mummunar buqatarsu.
Sun yanka bayin Allah,su sha jininsu,sunyi luwadi dasu ga tsafi.Duk wasu laifuka mafi muni kuma manyan kaba'ira sun had'a.Yah Subhanallah,Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.Duniya ina zaki damu,biyewa dunqulallen tsokar dake kirjinmu yasa dan adam jefa kansa cikin halaka.Allah ubangija ya cigaba da tonawa masu irin halayyensu asiri ya kuma tsarkake zuqatan bayinsa salihai da fadawa mummunan halaka,Ameen yarabb..

Kyakkyawar rungume barrister fu'ad Hashim yayiwa Fahima,itama rikesa tayi tightly tana maida numfashi a hankali na samun nutsuwan zuci da gangar jiki

Hamdala fu'ad yake karayi a ransa da bai tafka kuskuren rabuwa da heemansa ba ma'ana bai saketa ba da yayi babban nadama a rayuwarsa.Tabbas a kowacce irin zamantakewa barin ma aure da shine ginshiki ana buqatar fahimtar juna da kyakkyawar mu'alama na kyautatawa juna.Allah ya karawa mana fahimtar junanmu tare da abokan zamanmu

"Kwa bari ku k'arasa gida koh Mr and Mrs Hashim"

Suka tsinkayi muryar Zaki da bayan ya gama maganar ya dauke kansa daga dubansu kai kace ma bashi yayi maganar ba,dariya dukkansu sukasa har Dija itama dake makale da mijinta ita kuwa Zee sai binso da ido kawai takeyi, duk sai taji ta daban.Kewa da nadama na Kara nukurkusarta na sanin AA a ayuwarta tun farko Wanda bai taba zama alkhairi ba.Ya Rabbi Ya Karim ka rabamu da aikin dana sani a rayuwa

_A YEAR LATER_

Ihunta ne ya karade ilahirin compound d'in da shashin GOVERNOR MOHAMMED MOHAMMED GIWA yake tare da surukansa daga kusada su wanda yake daga cikin Government House din.

Harsu Dada da Zee dake zaune tare dasu suka jiyota daga flat dinsu suka fito a rude jin muryar Dija tana kurmoton ihu da turtsetsen cikinta ta shaqo wuyan King ta hammatarta sai aika masa cizo take a kafada,yayi yayi ta sakeshi ya sata a mota suyi maza suje asibiti ta tsaya bala'in duk shi ya jawo mata
Chapter 35 · 0% Book details