← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 36

Sashe 27

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wanene yayi sanadiyyar zuwanki gidan nn?"

"Nima bansani ba kawai na farka na tsinci kaina ne a wannan dakin"

"Daga ina kenan?"

"Daga asibiti,nasan de labour ya tasomin daga gida surukata ta kawoni asibiti.Na wahala sosai har karfina na kare ban haihu ba harna fita a hayyacina daga nan sai farkawa nayi na tsinci kaina a wannan dakin"

"Mijinki fah?"

Saida tayi shiru kamar bazata tanka ba sai kuma ta sauke numfashi muryarta na rawa tace

"Allah ya mishi rasuwa tun cikina nada wata 4"

"Iyayenki fa da sauran danginki?"

Shiru tayi bata Bawa Fahima amsa ba

"Kiyi hakuri da tambayoyina ama yana da mahimmanci musan junanmu tunda kaddara ta hadamu"

"Sunana Saudat Ni marainiyace,iyayena sun rasu tun ina karama na taso a wajen kanwar babana. Na wahala a hannunta sosai har Allah ya kawomin miji nayi aure.Habib ya zame min mijin marainiya, don ya kula dani ya bani gata da kulawa da dukkan mace zata buk'ata wajen miji. Mahaifinsa shima ya rasu sai mahaifiyarsa da suke zaune tare

Habib ya rasu sanadiyyar hatsarin mota a hanyarsa ta zuwa Zaria shine na koma wajen Ummansa da zama na cigaba da rainon cikina wanda kullum yake bani matsala sbd mutuwar mijina daya shigeni sosai har zuwa lokacin haihuwa na"

Daga Fahima har Zee sun tausayawa labaryn Saudat.Gashi koh hawaye yanxu bata iyayi sai ajiyar zuciya,Fahima ta sake tambayarta

"Wani asibiti aka kaiki a ranar da zaki haihu?"

"Asibitin da nake ante natal HEALTH CARE"

Shiru Fahima tayi tana tunanin,asibitin da Dija ta haihu kenan

"Tsawon shekara nawa kina gidan nan?"

"Nima bansani ba sai dazu danaji mutumin daya fita yana fadan 6yrs"

Sai lokacin maganganun AA ya fara dawowa Fahima kai
_kin taka sawun barawo_
"Wato ba ita akayi niyyar daukowa ba kenan"

_Nida kaina bansan ya akayi kikazo gidan nn ba a maimakon DIJA_
"Ya shiga asibitin da niyyar dauko DIJA bai sani ba ya dauko wannan baiwar Allah.Toh knn sace DIJA plan din AA ne sai kuma yayi rashin sa'a

Idan hakane tho ina ita DIJAN take da yaranta?"

Ita kadai take ta maganganunta,cen kuma ta sake yiwa Saudat tambaya

"CS aka miki koh da kanki kika haihu don na tabbata koh wanne ne dole zaki gane bayan kin farfado"

"CS akamin,lokacin dana farka ina kokarin mikewa sbd dakin dana ga kaina a ciki baiyi kama da dakin asibiti ba sai naji zafi daga cikina ina dubawa naga alaman dinki.Haka sukayita kula dani na tsawon lokaci harna warke daga nan suka fara....."

Kasa karasawa tayi itama Fahima bata kara magana ba sai tunani data fada.Sun kai kusan 20mins dukkansu da abinda yake sakawa banda saudat data gama cire rai take yiwa kanta adduar mutuwa ta huta.Mayarda kallonta kan Zee datayi shiru tana kallon waje daya Fahima tayi ta dafa kafadarta,juyawa tayi tana kallon fahima cikin nauyi

"ZEE KAITA zaki iya fadamin wacece ke?"

Saida tayi shiru na en seconds tukunna tayi ajiyar zuciya ta fara bawa Fahima amsar tambayarta

"Sunana Zainab Yusuf,asalina ni er Katsina ce wato garinmu daya da AA KAITA hakama anguwarmu daya.Tun AA na secondary school SS2 lokacin ina JSS1 yace yana sona irin soyayyar yarintar nn,iyayena sunyi² su rabamu ama naqi haka harya gama secondary school muna tare.Da farko AA inyazo wajena haka zaita tattab'ani tun ina ki nima harna saba abin yakemin dadi, bana mantawa akoi ranar da AA ya daukeni mukaje dakin abokinsa muka fara wasanni kamar yanda mukeyi don yace bazai shigeni ba harsai munyi aure,bansan ina da karfin sha'awa ba sai ranar don na kasa jure wasan da AA yakeyi dani har saida na sashi yayi amfani dani a Wannan ranar.Toh tun daga nan nida AA muka saba da juna ta wannan fannin koh bai nemeni ba ni zan kai mishi kaina.Ana haka har nayi ciki wanda yayi sanadiyyar mahaifina zuciyarsa ta buga shine mahaifiyata ta daukeni mukaje aka zubar.

Bayan AA ya samu makaranta a Lagos ya tafi ni kuma na kasa rike kaina gashi bbu wanda nakeso na aura kamarshi haka na zama tamkar public toilet ina rabawa maza kaina,na zubar da ciki harsu 4 da kaina wanda ya zama sanadiyyar damaging mahaifata.Bakin cikina ne ya dasawa uwata hawan jini itama ta mutu ta barni ni kadai dama mu uku ne kuma dukkanmu mata nice karama,yayuna mata sunyi aure daya tana bauchi daya tana kano.

A wani zuwa hutu da AA yayi ne yaga yanda na koma shine ya daukeni muka tafi Lagos tare ya kamamin daki. Zuwa na Lagos ya kara budemin ido saboda irin kudin da AA yake kashemin,kowanni club ina nan duk wani bariki da yawon duniya ina gaba har AA ya gama karatunsa.Soyayyar dayake min da tausayina na tunanin shiya fara jefani a wannan harkar yasa shi aureni muka dawo Kaduna da zama inda ya samu aiki.Tun lokacin da na fara daura idona akan KING naji duk duniya bbu wanda nakeso kamarshi,babu irin dabarun da banyi ba akansa tun inayi a boye harna fito fili ama KING bai bani hadin kai ba dukda yanda surata da kyau na ke tasiri akan kowanne namiji shi kadaine daban a cikinsu shiyasa akullum yake kara shiga raina"

"Da sa hannunki a batan matarsa DIJA kenan don cimma burinki akansa?"

Shiru tayi kamar bazata tanka ba cen kuma tace

"Babu sa hannuna a batan DIJA ama bazan boyemiki ba nafi kowa farinciki a lokacin danaji labary saide farincikin nawa ya koma ciki lokacin da naji shima KING din an nemesa an rasa.Tsawon shekaru ina dakon soyayyarsa da burin dawowarsa har zuwa ranar da labarin dawowar tasa ya baza gari saide a ranar farincikina ya zama ragagge"

"Saboda me?"

"Saboda sex photos da videos dina da aka turamin da aikin sace yaronki da mahaifiyarki idan kuma banyi ba za'a yada wannan videos din da photo duniya tasan wacece ni"

Sauran maganar da AA yayi dazu ne ya sake dawowa kwanyar Fahima

_Ni nayi amfani da wannan bitch din tawa ta hanyar blackmailing dinta da past dinta,sabod tana tsoron kar a bata mata image a matsayinta na first lady_

"Kenan AA ne ya kashemin MAMI na?"

COMMENTS
SHARE FISABILLAH
[1/6, 9:11 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

BY APHSERTEEN KHAIREE

ELEGANT ONLINE WRITERS

31

"Yanxu son zuciyar AA har yakai haka,me nayi masa da zayyi amfani dani wajen tarwatsa amininka,me nayi masa da zaai rabani da Mamina?"mena masa dazai so tarwatsa farin cikina akan abin duniya abin duniya fararre qararre abin duniyar da zamu mutu mubarshi dukiyar da daidai da kwayarta sai antambayeka yanda ka tarata dukiyar da ranar kiyama zakaji dama baka tarata ta wannan hanyar ba ranar da bbu wani mai cetonka ranar da halinka shine jarinka yahh subhanallahi Allah kayimana kyakkyawan qarshe karabamu da son zuciya ameeen

Kuka takeyi sosai mai ban tausayi Zee na tayata,Saudat kuwa sai mayarda numfashi takeyi dakyar.Karar bude kofa sukaji inda wani guards ya kawo musu abinci a takeaway guda uku ya ajiye.Zee ce tayi karfin halin janyo abincin sbd wani irin yunwa dake nuk'urk'usarta,kokarin tashin Saudat tayi ama ta kasa daga koda kanta ne sai numfashi take saukewa a wahale.Fahima kuwa koh kallon abincin batayi ba daman,addu'a kawai takeyi Allah ya kawo musu mafita kohta halin k'ak'a su bar gidan nan don ta dau alwashin matukar ta bar gidan nan sai ta tona musu asiri.Idan kuwa government sukayi burus da lamari don halin kasarmu kenan na rufe manyan laifuka,ita da kanta zata d'au fansa da hannunta koda hakan na nufin karshenta kenan.

_KING_

Tunda suka sauka a d'akin nan bai huta ba koh na minti daya dama da alwalarsa ya taho, sallah ya dingayi yana karatun Qur'an dake haddace a kansa ba qaqqautawa wanda sautin zazzaqar qira'arsa ke tashi daga dakin yana daukar gidan a hankali.Ji yayi an banko dakin nasa a gigice cikin rudewa don karatun da King yakeyi har ODUBARIBA na amsar sakon a jikinsa daman gashi karfinsa ya fara janyewa shiyasa yakeso a nada sabon shugaba tun fakin komai ya lalace musu.

Wasu guards ne biyu suka shigo dakin da bindiga hannunsu suna pointing din King,bai dago ba har saida yakai aya tukun ya daga kai yana kallonsu.Kasa hada ido sukayi dashi sbd wani kwarjini daya cika musu ido dayayi

"Stand up and put ur hands at back"

Daya guard din ya fada,ba musu King yayi yanda sukace

"Oya move"

Gaba ya wuce suna biye dashi a baya har suka fice a dakin,hanyar corridor din suka biyo inda dakuna ke jere suna zuwa dai² dakin dasu Zee suke King ya tsaya yana kallon kofar dakin,nishin Saudat da kukan Zee ke tashi daga dakin sbd bbu komai a dakin sai kujera kwaya daya shiyasa yake daukar sauti sosai

"I said move"

Dayan guard din ya sake magana yana taba keyar King da gun din dake hannunsa har suka karaso parlor dake cike da mutane,bin jama'ar parlor ya farayi da kallo.

Gboy da Suleguy ya fara daura idonsa kansu kana ganinsu kaga cikakkun hausawa sai AA KAITA dake zaune daga gefensu,idonsa ne ya sauka kan David da Samuel da koh a mafarki a gansu sai ganesu sai wata fuskar daya d'au kusan 2mins yana kallonta sbd tsantsar kamarsa da Fahima Aliyu.Dauke idonsa yayi ya aza kan Joseph da Marcus da bai shaidasu ba sukam.

D'an lumshe idonsa yayi ya bude inda idonsa ya sauka kan mutumin da ya daukeshi danginsa yanxu,yake jinsa kamar jininsa,mutumin da a yanxu yake jan zaren ragamar rayuwarsa,yake tafiyar da komai nasa,yasa masa Sunansa sbd shakuwa da soyayya dake tsakaninsu wato ALIYU sannan ya mishi laqabi da ZAKI akan jajircewarsa da rashin tsoronsa akan komai.Ji yayi kamar an sokeshi a ransa,runtse idonsa yayi ya sake budesu saboda ya qaryata abinda yake gani

"No Zaki,not you.Zan iya daukar kowanni irin cin amana a wajen koma wanene ama banda kai Zaki,please ka karyata min abinda nake gani da idona,kace min kaima daukoka sukayi"

Zaki dake zaune kan wata single chair dake daban kamar ta sarakuna yayi cross leg fuskar nan a toshe da bakin glass as usually ga guards din King a zagaye dashi ta bayansa.AA KAITA ne ya ari bakin Zaki ya fara magana

"U see our humble King hatta na hannun damanka ya zabi yayiwa Kunqiya aiki,so u have no other choice than to surrender"

"But ZAKI why,meyasa zaka siyarda loyalty ka?"
Chapter 27 · 0% Book details