← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 36

Sashe 36

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 3 min read

Da taimakon Zee aka samu Dija ta shiga baya donsu Dada da suka fito kunya da kara ya hanata karasawa dama King ya hana securities da guards shigo bangaren idan bashi ya nemesu ba.Zaki kuwa ya tafi aiki daya rike masa wuya sosai yanxu don yana daga cikin manyan jami'an tsoron da ake ji dasu a kasa baki daya sbd jajircewarsa da kokarinsa kan aiki.

Zee ce tayi driving d'insu zuwa asibiti kafin su karasa kua King yasha cizo da mintsini harya gode Allah

Babu wani bata lokaci akayi labour room da ita inda King ya tsaya kafa² ya kafe babu inda zashi har saiga matarshi ta haihu tukun

Zaki da Zee ne sukayi ta wani shiga da fice a asibitin dukda magana bata hadasu saide ido kawai

Kapshara!Yanda Dija ke ihu haka King keyi shima,yau de ya ajiye mulki ya taya matarsa labor wanda har nurses din dariya suka dinga masa. Wani gigitaccen ihu na karshe da suka saka wanda ya cakude da kukan samb'alelen yaronsu shima yana tsala nasa ihun kuka da muryarsa data karade ilahirin dakin yasasu sakin wani ajiyan zuciya wanda Dija da king suka sauke a tare sai kuma hamdala ga Rabbi,dakyar nurses din suka lallabashi ya bar dakin akan za'a gyrasu

Yana fitowa waje kuwa ya rungume Zaki dake tsaye a gefe

"It's a boy,Alhamdulillah alhamdulillah.A new lion is born again"

Haka sukaita murna,take Zee ta kirasu Dada ta sanar dasu Dija ta sauka lfy bayan nn ta kira Fahima dake kwance jikin fu'ad itama da d'an matashin cikinta ta Sanar da ita haihuwan

"Allah sarki,Allah ya jikanki Saudat ya kai Rahama kabarinki"

Fahima ta fada idonta na tara kwalla tunowa da kiran ajali wanda yayi sanadiyyar fadawar Saudat hannunsu AA a ranar data haihuwa

Kafin kace mai garin ya dau amon haihuwar First lady DIJA GIWA ta hanyar picture kyakkyawan yaron mai kama da babansa sak da Zee ta daura a social media tun suna asibitin tasa

"Welcome to the globe Prince"

Nan aka fara kururuwar cika a asibitin danma securities da sauran guards dinsa suna tsaye tsayin daka aka hana mutane shiga

Duk wani hidima da shiga da fice Zee da Zaki keyi,duk da irin daure mata fuskar da yakeyi sai daya sassauta yau sbd d'a kuma takwara da yayi wanda farincikin hakan yaki boyuwa a fuskarshi

Tun suna magana kasa² shi da Zee sai gashi Zaki ya sake harda d'an hira da wasa da dariya.A cikin satin haihuwar kuwa shakuwa ta ban mamki ya shiga tsakaninsu

Nan su Fahima da Dija suka fara shigewar Zee da tsokana

"Nide tambaya daya nakeso ki masa akan maganar daya taba fadamin na ya tsani kukan mace shine nakeso naji dalilinsa"

Inji Fahima suna zaune a bedroom din Dija ana gobe suna suna duba dinkunansu,Dija na shayar da baby.Dariya Zee tayi tace

"Dadinta nide ba er jarida bace gidan bin kwakkwafi da nacin jaraba"

Masha Allah,Barakallah.Masu jego King da Dija babu dama sai godiya ga Rabbis samawati mai kowa mai komai,mai yin yanda yaso a lokacin dayaso

Yaro yaci sunan mahaifinsa kuma aminintaccen mahaifinsa wato ALIYU ALIYU GIWA (AA GIWA)

Dakyar Zaki ya yarda ake kiran takwaransa da AA sai da King yace masa Insha Allah abinda yake tsoro bazai taba faruwa ba,shima AA KAITA muna masa fatan gafara da rahamar ubangiji masu irin halayyensu na Hassada,son zuciya,cin amana da ha'inci Allah ya ganar dasu gaskiya ya tsarkake mana zuqata

_AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM_
_TAMMAT BILHAMDULILLAH_

_SAI MUN HADU A MATA A YAU,ER UWA KARKI BARI AYI BABU KE.A SHIRYYE NAKE TSAF DA SABON SALO WANDA SAI ILIMANTAR YA KUMA NISHADANTAR DAKU INSHA ALLAH DUK AKAN FARASHI MAI SAUKI_ 150KACAL

CONTACT ME VIA 07086037570

_YOURS APHSERTEEN KHAIREE_
Chapter 36 · 0% Book details