← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 36

Sashe 12

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsa Dada takeyi ido cikin ido harya gama,Allah daya ambata yasata jin nutsuwa a ranta da d'an kwanciyar hankali.Tabbas su kansu sunsan Allah ne kawai yake karewa irin gararin da sukeyi daga nan zuwa can kuma bbu guri daya dayake safe gwanda ma nan za'ace gidane saide zukatan masu gidan ne haryanxu bata da tabbas akai don ance mugun mutum ba shida kama.

"Toh sikenan k'ad'o na yarda da Allah ama ban yarda dakai ba,nasan Allah ne ke karemu a duk inda muke haka a nan ma shi zai cigaba da karemu.Bansan me a zuciyarka ba daka nace mana lalle saika taimaka mana ama mun yarda zamu zauna a gidanki Idan kika shushemu keda Allahnki"

Ta fada sound so helpless irin bbu yanda ta iya d'in nan.Ajiyar zuciya King ya sauke at least de ta yarda zata kwantar da hankalinta ta zauna don amincewar Dada shine na Dija,sannu² zasu gane wani irin mutum ne shi da manufarsa akansu na son inganta rayuwa

"Nagode da amincewarki Dada insha Allah bazaku ta6a nadamar kasancewa dani ba"

"Munji tho,yanxu a kawo mana abinci bingel am tanajin yunwa don tun jiya rabonmu da abinci"

Tashi King yayi cikin hanzari yace tho ya fita a dakin inda ya samu Zee da AA na zaune zaman jiranshi,dinning ya wuce ya dauko warmers din abincin da aka jera wanda Babaji yaci nashi ya bari don plate dinma na wajen ya hada da plate da spoon ya kara wuce dakin nasu sude su Zee da kallon mamaki kawai suka bishi harya rufe kofar dakin.

Dija na ganin King da warmers din abinci ta hadiye kukanta dukda batasan meya dauko ba ama tana kyautata zaton kwanukan abinci ne na en gayu,ajiyewa yayi a gaban Dada yace

"Ga abincin nan Dada,idan kun gama ku fito parlor don Allah"

"Toh sannu mungode,ina fatan bakasa guba a abincin ba?"

Murmushi King yayi ya girgiza kansa kawai ya fice a dakin

"Sorry na barku jira"

Ya zauna kusada AA,kallonsa AA yayi yace

"What's going on man?"

"Karka damu aikin ba naka bane"

Ya fada yana maida dubansa kan Zee yace

"Ermmm Zee please taimako zakimin,inada baki en Fulani ne a nan gidana that I want to help.Family ne I mean Baban da mamar sai er su duk suna nn wajena"

Da mamaki AA da Zee suke kallonsa

"Man a ina ka samesu,na tabbata bakuda en uwa Fulani?"

"Abeg AA ka kyaleni nace maka aikin nan bai shafeka ba,just listen in kuma bazaka iya ba then set your way kawai"

Dariya AA yayi yace

"Kaide a kwashe² zaka kare wallahi"

"Ehh naji,mind ur business please"

Wayarsa ya ciro yana dariya shi kuma King ya kara maida dubansa kan Zee data kuresa da ido tun dazu

"Kinaji Zee,yarinyar nakeso ki taimakawa don inason kaita school gashi koh Hausa bataji Kinga ba karamin aiki bane"

"How old she is?" Zee ta tambayeshi

"Bazata wuce 16 ba"

Wani irin tuquqi Zee taji a ranta dukda bataga yarinyar ba

"Can I see her"

"Yeah,zasu fito yanxu suna cin abinci ne"

"Okay,so yanxu me kakeso na maka akai?"

"Yawwa,like I was saying zaki taimaka mata wajen koya mata wasu abubuwa na zamani da kuma karatun please kinde gane mai nake nufi.Irin fulanin dajin nan ne masu yawo kiwo,she needs to know a lot"

"Karka damu zanyi iya kokarina Insha Allah"

"Yawwa nagode sosai,yanxu wani school kike ganin zata fara?"

"Ehmmm,we'll think about it"

Bude kofar da sukaji ne ya mayda hankalinsu wajen inda Dada ta fita Dija na rukube a bayanta,tashi King yayi da fara'a a fuskarshi yana nuna musu kujera yace

"Bismillah Dada,ga dan uwana da matarshi sunzo gaisheku"

Wani kallo Dada ta bisu dashi ta tsaya kallon Zee din sama da kasa kamar taga kashi,AA ne ya fara gaisheta ta amsa a dakile snn Zee tace musu

"Morning"

Wani sheqeqe Dada ta kalleta tana wani sake baki tace

"Kaji kafura er gidan kafurfur jikar k'aruna"

Wani kallo Zee tabita dashi tana mamakin wannan village woman d'in da ko kallo Bata ishetaba take cemata kafura karde sune King yake magana akai?kallon AA tayi tana fadin

" Wonder shall never end, can you imagine see dis old rag"

gyaran murya king yayi Zee ta juyo tana kallonsa ranta a 6ace daman ita akoi saurin hasala yace

"Take it easy lady,Dan Allah don't take it personal help them for my sake"

Hadiye wani tuquqin bakin ciki tayi daya tokareta a wuya dakyar,Dada kuwa tashak'a takai har wuya jin suna zuba yaren kafirai.kallon king tayi tace

"k'ad'o shinikin kanmu kakeyine mude mundogara ga Allah"

AA yayi gyaran murya yamaida kallonsa ga Dada yace

"Mama ki kwantar da hankalinki indai agidan nan kuke wurin wannan bawan Allahn to bakuda fargaba dan mutumin kwarai ne in yanason cutar daku bazai kawo ku gidansa ba ya kawo kune kawai dan inganta rayuwar ku data erku
Kuyarda da Allah ku yarda dashi bazai cutar da kuba"

kallon zee yayi yana guntse dariya cikin murya kasa² yace

"Saikin dage dan kansu a tukunya yake"

Gyada kai tayi tana mai jinjina aekin da king ya bata murmushi tasakarwa Dija dan ita Dada tagama shaqar da ita duk da taga yanda jikinta yayi sanyi da maganganun AA tace

"Emmata ya sunanki?"

King ne ya bata amsa da DIJA,murmushi tayi tunawa da abinda King ya fadamata dazu akan batajin Hausa.Still tana kallon Dijan da kanta ke k'asa tana wasa da fingers dinta ta maqale a jikin Dada tace mata

"DIJA,masha Allah Khadijah kenan ko?"

Jin ta kira sunanta yasa Dija d'aga mata kai kawai badan taji mai ta fada ba saide yanda Zee keta mata murmushi ne ta burgeta har taji itama ta kwanta mata arai tana mayar mata murmushi ta mai kyau wanda yasa zuciyar zee bugawa dan zallar kyau da quruciyarta daya bayyana sharewa tayi ta mayda kallonta kan King tareda lumshe idonta da gyada masa kai alamun komai zai tafi dai²,itade Dada kallonta kawai takeyi a yatsine don sam yarinyar bata kwanta mata ba...........

🤥🤥🤥
Kar kuyi sanya,ku cigaba da biyoni don ba'a ma fara wasan ba tukun 🤙🏻

"
[1/6, 9:03 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*
BY APHSERTEEN KHAIREE

ELEGANT ONLINE WRITERS

15

ZEE basu bar gidan ba saida ta tabbatar taja Dija a jikinta sosai ta sake da ita dukda Dada na tsawata mata dole ta hak'ura ta kyalesu ama idonta na kansu kar a cutar mata da 'ya.Ran Zee fes cikeda nishadi don wnn aiki da King ya sata tamkar wani tsani ne na cimma nasara wajen biyan buk'atarta,mutuk'ar gyara wnn er dajin ne farincikin King toh ta daura d'amarar biya masa buk'atarsa ta tabbata hakan ne kad'ai zaisa ta samu kusanci da shi.

Sun tafi akan kullum zata dinga zua tana yini dasu Dija harsu sake da ita kafin a sama mata makaranta,Babaji kua yana cen wajen sabon abokinsa Baba Audu mai gadi da yake cewa Bandarawo (abokina) ya sake sosai suna hirarsu Babaji ya dafa musu shayi a er butar shayin mai gadi sun karkace akan benci suna shan kidarsu a tashar radio.

Koda King ya rakusu AA suka gansu abin ya mishi dad'i sosai don har saida kwalla ya taru a idonsa tunawa da Babansa don shima yana yawan fitowa wajen mai gadi su sha hirarsu, yana fatan Dada ma zata sake ta kwantar da hankalinta su daukeshi tamkar d'a.

Su AA zasu shiga mota King ya tsaida su

"Ga baban Dija cen wajen Baba mai gadi muje ku gaisa"

"Ohh King toh ka bari mu shiga motar ai sai mu tsaya mu gaisheshi" inji AA

"NO,wallahi baka isa ba wani irin gaisuwa ne a mota"

"Hahaha,Man anya kua ba wata a k'asa kode²"

"Kai kasani,nide muje ku gaisa lokacin sallah yayi don iskanci ka tsaya kayi sallah tukun ama zakace wani sauri kake.Haryanxu bazaka dena missing sallah a jam'i ba koh?"

Basar da zancen AA yayi yace

"Kaide muje mu gaisa dashi kana 6atamin lokaci bansan yaushe ka koyi surutu ba yau,Zee taho da motar bakin gate kawai ki sameni anan"

Okay tace bayan sunyi sallama da King ya shiga tayi warming motar su AA kuma suka doshi wajensu Babaji dake kishingid'e Baba mai gadi kuma ganin Zee ta tada mota ya nufi gate

Bayan sun gama gaisawa AA ya shiga mota suka wuce gida cike da sake² a ransa,shima zuciyarsa fess don yana ganin lokacin cikar next burinsa akan King ya kusa dama Allah² yake a zo wajen

"You're smiling?"

Zee da tagama noticing dinshi don yana driving yana zabga murmushi kana ganinshi kasan yana cikin farinciki,cikin er basarwa AA yace

"Kuka kikeso nayi?"

"No,but what's the reason behind d smile? Tunda muka fito kamar kana cikin nishadi"

Dariya AA yayi ya d'an buga sitiyari yace

"Zee sa ido,kawai mutanen King ne suka bani nishadi.They're really funny,I like them"

Ya fada yana murmushi,6ata fuska Zee tayi taja tsaki kawai har suka iso makeken gidansu dayafi na King tsaruwa da kele²n duniya don ba karamin kudi AA yake kashewa kansa ba haka zasuyi ta fada da King akan ina yake samun irin kudi daya yake kashewa haka don yasan aikinsa de bai kai ya dinga samun wnn mak'udan kudin ba sai yace mishi yana k'ananan harkokine.Haka ma wajen suturu da motoci duk ya kere King ama dukda haka farin jinin jama'a da samun nasara akan komai King ya fishi don koh a wajen aiki ya fishi matsayi saide kawai AA ya nunamasa kudi wanda baisa jama'a kaunaceshi ba kamar yanda sukewa King.Sau tari ma mutane na mu'amala dashi ne sbd kusancinshi da King din

A kwana a tashi ba wuya,duk abinda aka sawa naci da addu'a tareda fatan nasara sai an cimma gaci saide wani ikon Allah don ba lalle ba komai kake so saika sameshi ba arayuwa duk nacinki wani abin saide ka hak'ura,haka ma idan kaga kanata addu'a da rokon Allah akan abu kaga bai baka ba toh karka sare shiyasa akeso ka barwa Allah zabi akan komai da zakasa gaba arayuwarka.Allah ya mana zabin alkhairi
Chapter 12 · 0% Book details