← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 36

Sashe 8

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bring her along" ya fice a dakin,wani tsawa Zaki ya daka mata wanda ya sata razana ba shiri ta mike jikinta na rawa tabi bayansu.Kasancewar da mota daya kawai suka zo ya sata shiga baya kusada King sai driver da Zaki daga gaban mota,tsit motar ta dauka sai driver dake ta aikinsa har suka karaso unguwarsu King bbu wanda ya gane motarsu King ce sbd bai cika fita shi kadai ba da mota daya gashi motar irin dark tint din nan ne, gate man ya wangale musu gate suka shige har kusada entrance na gidan.Jin motar ta tsaya yasa Fahima dawowa daga duniyar tunanin data tafi,ficewa sukayi suka barta cikin sauri itama ta fito tabi bayansu da dan gudu²nta harta cimmasu a parlor

"Ka kaita dakin Dija ta kintsa kanta,a sama mata abinda zataci"

Yana gama fada ya haye samansa dama shi kadai ke amfani da saman duk sauran dakuna na daga kasa,da kallo kawai Fahima ta bishi harya 6acewa ganinta sai muryar Zaki dake kada mata hanjin cikinta taji yana

"Tsayuwar uban me kike a wajen?"

Cikin sauri ta karasa inda yake,hanyar wani dan corridor suka bi inda dakuna yake a jere harya bude mata wani daga ciki da shiga. Tanaji ya sawa dakin key

Ajiyar zuciya ta sauke,bata cikin nutsuwar da zata tsaya karewa dakin kallo sai kofar toilet kawai ta nema ta shige.Cire kayan jikinta tayi, wani danko² takejin jikinta na mata ta tsaya a gaban shower ta sakewa kanta ruwa

Har lokacin photo gawar Maminta take gani a idonta kwance cikin jini, wani irin kuka tasa mai kamar ihu ta durkushe a kasan wajen tana rerawa

"Mesa zaku kashemin Mamina, me mamina ta muku,mesa zaku jefa rayuwar wanda basuji ba basu gani ba akan cikar burinku.Wayyo Mamina Allah ya jikanki shiknn sun rabani dake,shiknn bazan sake ganinki ba,shiknn sun raba Uwa da erta.Rabuwa ta har abada"

Ji tayi hawayenta sun 'kafe,zuciyarta ya bushe.Kuka ba nata bane yanxu,she really av to be strong.Cikin muryar mai cikeda 6acin rai tace

"ZEE KAITA,Wallahi wallahi sai na zama ajalinki,sai kinyi nadamar saka rayuwata cikin gagari"

Wanka ta tashi tayi cikeda karfin hali da dakewar zuciya tayi alwala ta fito,closet dake kusada toilet din ta bude.Kayane a Jere wasu a hanger wasu a jere a kasa kamar wani karamin shagon kaya.Gown mara nauyi ta nema tareda hijab ta saka ta dawo kan rug dake gaban gadon ta tada sallolin da suka wuceta,tana cikin sallah Zaki ya shigo ya ajiye mata tray da plate din abinci a rufe sai bottle water da cup akai

Bayan ta idar da sallah ta gama addu'o'inta tareda nemawa Maminta gafara,sai lokacin ta samu karewa dakin kallo.Kana gani kaga dakin mace don komai yana nn kamar mai shi na dakin haryanxu,a ranta tace

"Koh ina matarsa take,ta rasu ne itama koh haryanxu tana raye, mesa matar amininsa da kowa yasan hakan will chase after him,me dalilinta na kokarin tarnishing image din King,meya takashe iyayensa lokaci daya,garin yaya aka nemi matarsa da yaransa biyu aka rasa immediately her delivery kuma a hospital kuma daga ranar ba'a kara ganin KING ba sai bayan 6yrs,meyasa,ina yaje,ina yakai matarsa da yaransa?"

Numfashi ta sauke tareda kankance ido tace

"there's sumtin behind king's life,wanda harya shafi rayuwata yayi sanadiyyar Mamina ga Salim dina shima cikin hatsari.I must find out,dole sai na nemi duka amsan tambayoyin nn by all means"

Shigowan Zaki ne ya dawo da ita daga tunanin data fada, kallon juna suka fara ido cikin ido don ya cire bakin glass din da koyaushe yake idonsa. Fahima kuwa duk wani tsoronsa ne taji ya kau a zuciyarta sbd abinda tasa a ranta yanxu na cikar burinta wanda tasan Zaki shine first step dinta dukda batasan takamaimai alakar Zaki da King ba ama kowa yasan shine very close da King duk inda kaga King tho tabbas Zaki na wajen

Kan cushions dake dakin Zaki zauna yana facing dinta,juyawa yayi ya kalli tray din abincin daya kawo mata ya dauke kai.Har lokacin idon Fahima na kansa

"Meyasa bakici abincin ba?"

"I don't feel like eating" ta bashi amsa tareda mayarda kanta kasa

"Ranar yaushe suka kiraki akan aikin?"

"Ranar da king zai dawo"

"By which time?"

"Around 6 bayan na dawo daga aiki na tarar sun kwashe Mami da Salim"

"Zaki iya tuna number?"

"Private number ne"

"Me suka ce miki?"

Ranta ne ya soma 6aci da tambayoyin nasa kamar bazata amsa ba sai kuma tayi wani tunani

"Ce min sukayi na duba message dina inada sako kuma wnn aikin daidai yake da ran Mamina da Salim,then they cut off the phone"

"Me a sakon?"

"Tambayan da nayiwa KING ne a ranar daya dawo"

"Zaki iya gane wanda ya fito dake dazu?"

"Fuskarsa a rufe yake,ina cikin bacci naji kamar ana yimin allura bayan na farka naga mutum a kaina na tsorata har zanyi ihu yayi pointing dina da gun kuma ya nunamin pics din gawar Mamina"

Wannan karan kasa daurewa tayi ta fashe da kuka sosai,tashi zaki yayi ya fice ya barta a dakin saida tayi mai isarta tukunna tayi shiru.

Kogin da taji cikinta nayi ne ya sata tashi dole ta dauko abincin,fried rice ne da chicken lap kana gani kasan abincin restaurant ne haka taci kadan badan taji dadinsa ba don bakinta bbu taste koh kadan tasha ruwa kadan ta kwanta kwanta kan rug din wani wahallen bacci yayi gaba da ita.

Ba ita ta farka ba sai jin kiran sallar magrib tayi ta tashi tayi sallar,tana zaune kan rug din Zaki ya kara shigowa dauke da wani tray a hannunsa ya ajiye ya dauki na dazun ya fita. Bata mike ba a wajen har aka kira isha sai da ta gabatar da kamar 20mins Zaki ya dawo dakin ya zauna kan cushions din yana kallonta

"Zaki iya gane wani abu a pictures koh video da suka turumiki,I mean kamar wajen da aka dauki photo?"

Shiru ta danyi tana tunani cen tace

"Bazan iya tunawa ba"

Shiru Zaki yayi na en seconds sai kuma ya mike da zummar barin dakin yaji muryarta tana

"Menenen alaqarka da KING and how long av u been together?"

Zaki cikin tsananin 6acin rai da mamaki Fahima ya juyo yana kallonta,saida ta tsorata da irin kallonda yake mata ama ta dake itama tana kallonsa

"Wato ke duk halinda kike ciki yanxu bai isheki ba koh tukunna ma ya akayi kikasan ZEE KAITA ce ta saka aikin bayan kince bakiga fuskar daya daga cikinsu ba?"

Dauke kai Fahima tayi cikin halin koh in kula tace

"Idan ka shirya amsamin tambayata kaima zaka samu duk abinda kake bukata"

Kwafa yayi yace "Fine Allah ya baki sa'a" yayi ficewarsa

_KING_

Tunda ya haye sama bbu wanda ya qarajin motsinsa,toilet ya wuce direct ya cire kayansa yayi wanka tareda dauro alwala.Wata jallabiya fara kal mara nauyi ya saka ya gabatar da sallah la'asar daya basu sami damar yi a jam'i ba,saida yayi addu'o'insa sosai tukunna ya mike ya koma kan gadonsa.Album dinsa dake kan side drower ya dauko don shine kadai abinda yake debe masa kewarsu,idan yana kallon pictures dinsu sai yaji kamar suna kusada shi.

Yau daidai kan pics din Dijah ya tsaya,murmushi yayi yana shafa photo yace

"My fair lady" kallon pics dinta yayi daya bayan dayan har yazo kan wani da take tsugunne a kitchen da hawaye a idonta sharbe² yayi snapping dinta ba tareda ta sani ba

Wata er dariyace ta su6uce masa tunowa da drama da yasha ranar.....

_RAYUWAR KING DA DIJANSA_

COMMENTS AND SHARE FISABILLAH
[1/6, 9:01 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

APHSERTEEN KHAIREE

ELEGANT ONLINE WRITERS

10

_IN LOVE_

From the very first moment he saw her begging along the road side sumtin inside of him told him that she's the one,definetly it was love at first sight.He loves evrtin about her more especially that craziness. A ranar da ya fara ganinta,daga lokacin da ta zama mallakinsa,tsawon lokacin da suka dauka tare da kuma ranar da kaddara tayi sanadiyyar rabuwarsu har zuwa yanxu dayake da fatan da burin dawo da ita cikin rayuwarsa,those memories are really unforgettable.

Zuciya,ruhi da gangar jikinsa basasu taba hutawa ba har sai yaga DIJANSA a tareda shi cikin koshin lafiya da walwala kamar yanda take a da.Idan da gawar DIJA ya gani dole zai fawwala ransa kamar yanda ya rasa iyayensa ya hakura sanin cewa dukkan mai rai mamaci ne,ama yanaji a jikinsa DIJANSA na raye cikin tsananin bukatarsa.Kuma alkawari ya dauka bakin rai bakin fama sai ya nemota duk inda take da yardar ALLAH.

Bayan yayi snapping din DIJA da Dadanta sunata murna bakin nn har kunne,shi da kansa wani irin nishadi ya tsinci kansa ciki haduwarsa dasu.He can't get rid of looking at that cute smile on her cute face,yaji matukar dadi ganin ya sasu farinciki dukda basu san shi ba shima bai taba ganinsu ba

"Wait a minute please" KING yace tareda daga musu yatsa daya,da kallo kawai suka bishi don basu san meyace ba.Bude motarsa yayi ya ciro kudi masu yawa ba tareda ya kirga ba ya taho

Wani irin zaro ido dukkansu sukayi ganin kudin masu yawa a hannunsa ya taho wajensu tareda mikawa DADA yana murmushi yace

"Ga wannan,daga yau banaso ku sake bara sannan ku bani address dinku insha Allah zanzo tunda kince kin bani DIJA"

cikin nuna tsoronta DADA ta zaro ido jikinta na rawa tareda ririke DIJA kamar wani zai dauke mata ita tace

"Kai ka'do Ashe kai dan yankan kaine, kai ba karuwa kake so ba kan mutum kake nema.Wallahi bani baka DIJA,na fasa, na fasa bama sho ka rike kudin tsafinka bama sho"

Ta riko DIJA sosai,ita batama san me DADA ke fadi ba ama yanda taga jikin DADAn na rawa tasan bbu lapia itama nata jikin ya fara mamar² tana zaro manyan fararen idonta.Shi kuwa KING dariya suka bashi ba kadan ba ama ya daure sai murmushi kawai yake yana kallon yanda duk suka firgice, mutanen dake yawon neman kudine kuma bayan sun samu suke tsoro.

Kafe DIJA yayi da ido yana murmushi don ba karamin kyau ta kara mishi a ido ba yanda ta firgita ta zazzaro ido saiya kara mata wani kyau sosai,kan ya ankara yaji DADA tace
Chapter 8 · 0% Book details