← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 36

Sashe 19

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Asshha,ai da anan akaga gawarta ai da sauki"

"So maiyafaru?"

"A ranar da aka kawota labour ta nn gaba na aka wuce da ita,shiganta na karshe knn sai amsa amon mummunan labry da asibitin ya dauka na 6acewarta itada abinda ta haifa en biyu.A yanda nurses din suka fada tana haihuwa bayan doguwar nakuda wanda har takai karfinta ya kare sai CS aka mata toh kafin ta farfado an kaita dakin hutu suma jariran an gyarasu sai shigowa akayi aka nemesu dukka aka rasa abin al'ajabi"

"Ya Subhanallah,Innalillahi was inna ilaihi raji'un"

"Hmmm kede bari munga tashin hankali ranar don gabadaya asibitin nn hargitsewa yayi"

Wani irin ajiyar zuciya Fahima ta sauke,mmk ne ya cikata

"Su waye suka kawota asibiti ranar?"

"Ita da mijinta King suka zo, shiya kawota don bazan taba mantawa ba"

"Tho shi yana ina lokacin da abin ya faru"

"Nide bayan ta haihu naga wucewarsa har nake tambayarsa yace min ta haihu,cikin sauri ya fice daga asibitin tho tun daga nn ban sake ganinsa ba don koda abin ya faru bangansa ba haryau kuwa sai labarin dawowarsa da naji kwanakin baya"

"Su kadai suka zo asibitin knn,anya bbu wanda ya biyosu?"

"Gaskiya de bangani ba don kinga duk wani mai shiga da fita ina gani tunda desk dina na kan hanya inde mutum ya shigo maternity ward tho tabbas zan ganshi"

"Hmmmm Allah ya kyauta"

"Ameen yarabb"

Shiru sukayi na kusan 2mins

"Nasan bazaku rasa CCTV ba?"

"Ehh akoi"

"Zan iya samun bayanai na 2015 please"

"Chap,aiki jaa ama bari na hadaki da wani wanda zai taimaka miki akan wnn"

"Yawwa nagode sosai,Allah ya saka da alkhairi"

"Babu komai,anything for you"

_ABIA STATE_

Su 8 ne a zaune a parlor wasu na shaye²n su wasu daga cikinsu kuwa sai busa sigari suke,3 daga cikinsu hausawa kuma musulmai ne sai 5 kana ganinsu kaga iyamurai

"See yau ne rana ta karshe,kuwa da kake gani anan yayi nasa kai kadai ka rage gwanda karka batawa kanka lokacin kaje kayi kawai don gobe za'a mikawa ODUBARIBA ita"

Tsaki yayi cikin takaici yace

"I seriously hate dis bazaka gane bane Gboy"

Dariya suka kwashe dashi dukkansu banda wani iyamuri daya da kana ganinsa kasan baya cikin nutsuwarsa damuwa shimfide a fuskarsa

"Dude what's wrong,u look so worried"

"Ina cikin damuwa David"

"Kar kacemin akan sacrifice dinka,C'mon uchenna yarinyar da bakwa tare ma bbu wani shakuwa tsakaninku I think dat will be so much easy for you"

"Bazaku gane bane,she's all I have dukda bama tare ina kaunarta sosai"

"Karamin da iskane kai uchenna muda muka bayar da namu ance maka bama sonsu ne"

Daya daga cikin hausawan ya fada tareda jan tsaki ya mike yayi hanyar wani daki,tana kwance a kasa da jen zani a jikinta an mata daurin kirji dashi iyakar guiwarta

"Kee.."

Ya daka mata tsawa wanda ya sata razana da mike ta sauri take hawaye ya fara ambaliya a fuskarta,Wani irin shock da firgita yayi lokacin da ya kalli fuskarta

"Who are you"

Yana pointing dinta da yatsa,itde sai karkarwa take tana kuka daga tsaye

"How comes,I said who the hell are you?"

Comments and share fisabillah🙏🏻
[1/6, 9:07 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

ELEGANT ONLINE WRITERS

22

A kid'ime ya fito daga d'akin,yanda ya bugo kofar ne ya jawo hankalinsu David kansa duk suka tsura mishi ido yanda ya wani firgice yana wani irin numfashi kofofin hancinsa duk sun bude har jijiyoyin kansa sunyi rad'a²

"No,this is not possible. Tayaya hakan ya faru,garin yaya"

Gboy ne ya taso kusada shi ya rikeshi yana tambayarsa da Hausa

"Meyafaru ne AA,koh ta mutu ne?"

Girgiza kansa kawai AA yakeyi yana

"Ba ita bace,wallahi ba ita bace"

"Kamarya ba ita bace,ban gane ba?"

"Wnn ba Dija bace,wnn ba matar King bace she's really not the one"

Dukkansu saida suka shiga shock suka fara kallon junansu

"What do you mean she's not the one AA,wani irin magana kake ba kai ka kawota da hannunka ba?"

Cewar David duk sun k'ura masa ido suna neman karin bayani

"Yes nina kawota da hannuna,nina fito da ita da yaranta daga asibitin ama tun ranar ban sake shiga inda take ba sai yau.Kuna nufin wnn ce a gidan nn tun ranar dana kawosu?"

"Itace mana AA,itace ka kawo da hannunka ama tayaya zakace ba matar King bace?"

Gboy ya tambayesa

"Tabbas ba ita bace,kaina ya kulle ina buk'atar ganawa da ODUBARIBA ayau don komai zai iya faruwa"

Tsaki Uchenna da nasa damuwa ya isheshi shima yaja ya mike yana

"Stupidity, you destroyed evrtin AA and am sure u'll face the consequence for that"

Yayi ficewarsa daga parlor,kwalbar giya dake kan center table AA ya dauka ya soma kwankwada har saida Gboy ya rike kwalbar a hannunsa

"Calm down,it's not too late evrtin will be fine ka kwantar da hankalinka"

Hannu AA yasa yana bubbuga kansa idonsa yayi jajir

"Aahhhh,urghhh No...bazai taba yiwu ba after all this long ace aiki banza kawai mukeyi"

Daya daga cikin iyamuran mai suna Samuel ne ya matso kusada AA ya dafashi yace

"Easy Man evrtin will be fine,am sure ODUBARIBA will find a way out"

Hanyar underground suka nufa inda DAKIN DUHU yake don zuwa ga ODUBARIBA,cikin ladabi, gushewar imani,toshewar zuciya da kwakwalwa suka zube a gabansa suna mishi sujjada.Cikin wata kakkausar murya mai tsoratarwa ya fara magana

"You destroyed evrtin AA KAITA so you're the only one to fix it"

"Tuba nake ODUBARIBA,nima bansan garin yaya hakan ta faru ba"

"For all this while our cults is waiting for the KING to RETURNED, our success and progress relays on RETURN OF THE KING"

"Meyasa Kunqiya tafi buk'atar King kawai ODUBARIBA"

David ya tambaya kansa a qasa

"Sbd lokacin sauka na yayi kuma muna bakatar mutum mai tarin nasara,farin jinin jama'a yayi taking over.Kaf cikinku bbu wanda ya cancanci wnn kujerar sama dashi snn matarsa da yaransa sune mafarin aikin kafuwar shugabancinsa"

Cikin tsawa ya Kira sunan AA wanda har saida ya razana

"This is the second time you're failing akan aiki kunqiya don haka dole ka kawo jinin matarka cikin gaggawa snn kasan duk yanda zakayi cikin kwana biyu ka kawo mana King ta kowacce hanya"

Bayan ya dawo gida,master bedroom dinsa ya wuce direct sai kai kawo yakeyi ya rasa wani tunani zaiyi,ya rasa me yake masa dadi ta ina zai fara.Taimakawa kunqiya ta samu King na nufin rasa kujerarsa ta Governor,King zai zama shugabansa both zahiri da bad'ina.Idan yaki kawo King kunqiya nn ma yasan hukuncinsa don kunqiya bazata taba tallafa mishi harya samu cin takara ba,Wata irin tsanar King yakeji na daduwa cikin ransa,irin tsanar da baisan ya zai misalta ba.

Tunda ya hadu da King shine mutum na farko a cikin abokansa da yake samun nasara da cigaban rayuwa sama da shi tun suna jami'a ya fishi komai,ilimi,farin jinin jama'a,kyau,nutsuwa da kamala wanda hakan ba karamin ciwo yake masa ba shiyasa ya tsanesa tun farkon haduwarsu bai tabajin son sa a ransa ba kawai de yana mu'amala dashi ne sbd wani dalili nasa

Abubuwan da suka faru a cen bayane ya fara dawo masa sabo

_*WASU SHUD'AD'D'UN LOKUTA*_

_UNILAG_

A dakinsu na hostel AA KAITA na zaune kan katifa yana duba wasu text books,King ya fita sai David da Samuel roommates dinsu suna hira tsakaninsu.David ne ya d'ago ya kalli AA yana murmushi ya dawo kusada shi kan katifar da yake da badir din kudi en dubu² ya mika masa.Da mmk AA yabi kudin da kallo yana had'iyar yawo dama shi mayen kudine

"David wnn fah,ina ka samu kudi mai yawa haka?"

Dariya David yayi ya dafa kafadarsa yace

"Wnn naka ne AA,take"

Zaro ido AA yayi yace

"Nawa kuma bangane ba?"

"Yes naka ne,na baka"

Warce kudin AA yayi da sauri yana zabagawa David godiya

"Karka damu,kaide abinda nakeso dakai kayi shiru kawai koh King karka fadawa"

Sai washe hakwara yake

"Chap ai ba saika fada ba,wnn weekend din a club zanyi ma zansha shagali na"

Dariya suka sa mishi Samuel yace

"Inde club ne bakada damuwa basai ka kashe kudinka ba zamu kaika"

Hakasu David suka dinga bawa AA kudi a boye suna jan ra'ayinsa har ranar suka mishi tayin shiga kunqiyarsu inda zai dinga samun makudan kudade yana kashe harkokin gabansa ba tareda ya wahala ba.Ba tareda wani tunani ba AA ya amince sbd son abinda duniyarsa koh tambaya wani irin kunqiyace baiyi ba.

Ranar su David sukace mishi ya shirya za suje inda za'a sashi a kunqiya, koh fadawa King beyi ba sai nemansa yayi ya rasa ya kira wayarsa kuma a kashe daman su David gaisuwa ne kawai yake hadasu tunda al'adansu da dabi'unsu ba daya ba shiyasa baya shiga harkarsu.

Nan suka kai AA har garin Abia wani gida dake bayan gari sukaje nn fah AA ido ya fara raina fata, saima da suka shiga cikin gidan ya kuma rud'ewa don tun a parlor dake red and black ya fara kakkarwa yana makalewa jikin Samuel sbd kallon da guards din suke mishi har kayan cikinsa yaji suna kadawa.Wani lungu suka bi daga cikin parlor sai yaga wani waje kamar rami an mishi steps daga kasa haka yaga David dake gaba yabi,Samuel dake rike dashi yace

"Relax dude"

Ya riko hannunsa suka sauka kasan underground din,inda suka shiga wani daki mai duhun gaske.Suna shiga yaga wasu candles sun kawo wuta daga kan da zeyi ya hada ido da wani irin halitta mai tsoratarwa take ya saki fitsarin tsoro don shi bai dauka mutum bane

Nan yagasu David sun zube a kasa suna

"ODUBARIBA....

Kamo hannunsa Samuel yayi yana masa alama daya durqusa shima haka ya bisu shima yayi,gabadaya ya gama tsorata ya firgice.Wani irin dariya ODUBARIBA ya kece dashi,dagowa sukayi suka mayarda hannayensu baya tareda sunkuyar da kai haka shima AA ya bisu yayi yanda yagasu David sunyi

David ne ya fara magana

"Here is the boy we told you about ODUBARIBA"

Wani irin dariya yayi yace

"Come closer boy"

Samuel dake kusada shi ya radamishi akan yaje gabansa ya durgusa,jikinsa na rawa ya karasa gabansa ya durgushe kan guiwuwinsa.Bude hannayensa ODUBARIBA yayi yace

"Welcome to our cults,we received everyone with an open arms here"

Cikin in'ina AA yace

"Thannnkkkk....you"

Dafa kansa yayi yace

"Repeat as I say"
Chapter 19 · 0% Book details