← Book details The Return Of The King Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 36

Sashe 13

The Return Of The King Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau da gobe tafi karfin wasa don duk kulafici,taurin kai da kafiya irinna Dada saida ta hakurewa kanta don kusan wata kenan bata taba cin karo da abin 6atanci ba a gidan King ba,sunyi fresh fatarsu da kalar tayi kyau sosai sbd nutsuwar zama waje daya da samun ingatattun abinci masu lafiya da gina jiki ga ra6ar AC ga rashin shiga rana.A cikin wata daya ba Wanda zai gansu yace sune masu yawo kwararo² sako²
'Suna bara suna karuwa' ba,dukda Allah ya karesu ba'a taba karuwar dasu ba 😂

DIJA an fara d'an gane Hausa ana kwakkwab'awa don irin yaran nn ne masu karambani da son koyan abu ashe rashin sakewar Dada ne yasata ta zama wata sukuku lokacin, gashi ta fara zuwa makaranta gand'an² a primary 4 both boko da islamiyya King ya sata dukda wahalar da karatun na bata wahala yanda komai tayi a aji sai yara sun mata dariya a makarantar baya sata losing hope hakan nn take dagewa ta kwab'o abinta koda za'a dariya ita koh oho abinda tasa a gabanta kawai takeyi itama tanaso ta zama er gayu kamar yanda take ganin Zee yana bata sha'awa a koda yaushe.

Zee ma na iyakar kokari akanta don sun saba sosai tana qoqarin fahimtar daita yanda zata kula da tsaftar jikinta dan dija ba Arabia bbu boko ko jinin haila batasan yanda zata kula ta tareshiba balle akaiga zancen wanka ranar da jinin yazo zee tana nan ita takoya mata yanda zatasa pad aekuwa ranar haka ta dinga tafiya tana kwale² Jim kadan sai ta tafi toilet ta leka in taga jini koh d'an diss ne sai a chanza wani,a takaice de kan tayi wanka saida aka karar da pad yakai leda 6.Zee kuwa tana cin dariya

Bra kuwa da Zee ta siyo mata masu shegen kyau ta nuna mata yanda zatasa,suna zaune a parlor da Dada sai ganin Dija sukayi da fito ba riga

"Dija ya haka ina rigarki kuma ya zaki fito parlor haka?"

"Ai wollah wnn riga mai cheu din bani rufeta,Zee am kinga yanda tamin cheu kuwa"

Haba Zee mai zatayi banda dariya,Dada kuwa ta shak'a tace

"Kai Zoo karuwa zaka koyawa bingel am,koda ban bari tayi karuwa ba sai yanxu zakizo ki fara koyamata yawo tsirara shiyasa har yanxu ban gama sakewa dake ba don daga ganinki kema karuwa ce Aradun Allah"

Cikin fullanci ta cewa Dija ta wuce da kuma ta saka rigarta,turo bakin gaba tayi tana tattaka kafa irinna shagwaba.Ana cikin wnn drama saiga King ya shigo da sallama idonsa ya sauka kan kirjin Dija,a guje ta koma daki sbd tsananin kunya ita tama manta da zai iya shigowa.

Zee CE ta bashi lbry abinda ya faru ya ka'da kansa kawai ya fice don ba karamin harbuwa yayi ba har junior na bashi sign 🙈

Ranar wata Saturday,Driver ya d'auko Dija daga islamiyya around 12 ta wuce flat dinsu da gudu SBD yunwar da ta kwasu don batayi breakfast ba,a parlor ta yarda hijab din islamiyyar da dankwalinta tayi kitchen ama bata samu komai ba don Dada ta fitar da breakfast din Sanin za'a kawo lunch kuma tasan Dija kota dawo bazata ci ba.

Dakinsu ta shiga ta tarar da Dadan na bacci dama ta baro Babaji a wajen bandarawonsa,yasa mai zatayi tayi gashi har kamar ji takeyi manyan hanjin cikinta na had'iye kananan,fito tayi ta doshi flat din King for the first time.Bata samu kowa a parlor ba ta danyi dube² koh zataga wani ama shiru sai kawai tayi hanyar steps da tagani

Kofar farko da bude a hankali Wanda yake parlorn King inda bedroom dinsa yake,tayi sa'a kua YANA parlor a kwance yana kallo jin bude kofar yasa shi kallon bakin kofar

Yayi mamaki ganinta don basu ta6a shigowa flat dinsa ba,tashi yayi ya zauna yana kallonta cikin shigar uniform dinta sky blue riga har guiwa da wando Wanda ya fito da asalin kuruciyarta kanta ba d'ankwali ga gashinta a tsafe yasha gyara don Zee na kula mata da kan sosai.

Bai taba noticing changes dinta ba sai yau,ta mishi matuk'ar kyau sosai harya kasa dauke idonsa akanta.Ji yayi yawun bakinsa ya qame ya kasa furta komai kawai ya kafeta da ido sai saukar muryarta yaji tana

"Don Allah zakici buyoti?"

Kasa gane me take nufi yayi kuma ya kasa kara tambayarta,ita kuwa duk ta soma galabaita don batada jimirin yunwa sam yau ma don tayi latti ne ama bata fita bata karya ba.

Cikinta ta fara nuna masa snn ta mishi in kiya dasu hannuta a baki alamar abinci sai lokacin ya gane tana nufin

"Don Allah zanci bread" kenan

Hanyar kitchen ya nuna mata don shi kam har lokacin jikinsa a mace yake dama kwana biyu ya kasa gane kansa tun ranar daya ganta bbu riga. Da sauri ta wuce kitchen din saide tana shiga ta tsaya turus don bataga komai a sarari ba sai kawai ta durkushe a wajen tasa kuka

Jinta shiru² bata fito bane yasa King tashi ya bita kitchen din,tun kafin ya karasa ya hangota a durkushe a kasa tana kuka shame² koh ganinsa batayi ba

Cikin sand'a ya koma baya yana gintse dariyarsa ya dauko camera sa dake parlor don dazu ya game duba wasu pictures daya dauko,dawowa kitchen din yayi ya tsaya inda bazata gansa ba har lokacin kuka take iya karfinta ga majina da hawaye har bakinta yayi snapping dinta..............

_CIGABAN LABARI_

Knocking kofarsa ne ya dawo dashi daga cen shudadden duniyar daya tafi na tsawon lokacin da bai sanma ya bata ba wajen

"Come in"

Yace dakyar don murya koh fita dakyau batayi kuma yasan Zaki ne,budewa yayi ya shigo da sallama King ya amsa ciki²

"AA KAITA da matarshi suna jiranka a kasa"

"OK ina zuwa"

Share and share fisabillah 🙏🏻
[1/6, 9:03 PM] +234 708 603 7570: *RETURN OF THE KING*

16

K'arar spoons ne kawai ke tashi akan dinning table din,kowa ya maida hankalinsa kan abinci yayinda suke having dinner a nutsuwa da burgewa.Cikin zukatansu kuwa tunani ne da sake² kala² kowannensu keyi

AA ne ya fara ajiye spoon din ya d'au tissue ya goge bakinsa,d'an gyaran murya yayi dukda King ya jisa baisa ya d'ago ya kallesa ba ya cigaba da aikin cin abincinsa.Zee kuwa juya spoon din kawai take ama hankalinta sam baya jikinta ta rasa dukkan nutsuwarta ganin wani irin kyau mai daukar hankali da King yayi,gashi k'ananan kaya ne a jikinsa don kafin ya sauko saida yayi wanka yasa wata iri armless da three quarter trouser wanda ya k'ara fitowa da ainihin mazantakarsa ga kamshin turarensa daya gama tafiya da nutsuwarta.

"I must say it's good to have you back again after a while"

Ba tareda ya d'ago daga cin abincinsa ba yacewa AA

"Thanks"

Murmushi AA yayi cikin son basar da abinda King din yayi na nuna halin koh in kula akansu daga shi har Zee din yace

"So,wani irin taimako zan maka yanxu"

"Akan me kenan?"

"Your upcoming gubernatorial election, naga yanxu baka da komai baka da abinda zaka tsaya campaign dashi and I know baka da wani dan uwa da zai tsaya maka bayan ni"

Ajiye spoon din shi king yayi ya kalli AA yana masa murmushi yace

"When a King's palace is burnt,a more beautiful one is rebuilt. Kar ka damu I need no one help,kaji da naka campaign din.I can do and undo as I wish"

Tashi tsaye AA yayi shima King ya tashi suna fuskartar juna kowannensu da murmurshi a fuskarsa ita kuwa Zee kawai binsu take da ido kamar an kafeta a wajen haka Zaki ma na tsaye daga gefensu,AA ya mikawa King hannu yace

"Allah ya Bawa mai rabo sa'a,best of luck Man"

Rike hannun AA yayi still smiling yace

"Ameen ya hayyu ya qayyum,thanks so much Old friend"

Sallama sukayi AA yayiwa Zee da ta kasa furta koda kalma daya magana akan ta tashi su wuce,har wajen motocinsu King ya rakosu ya daga musu hannu yayinda suke fita a gidan.

Dakin da Fahima take ya wuce direct inda ya sameta a bakin gado tana kwance kan praying mat tana kallon ceiling, she's deep in her thought har bataji shigowarsu King da sallamarsu ba.Sautin gyaran muryar King ne ya dawo da ita hayyacinta,ganin King a zaune ya sata mikewa da sauri ta zauna tana kokarin hada kalmomin bakinta ama ta kasa sbd firgici don bataji shigowarsa ba sam

"I inaaa kwa..kwana..

Ta fada kamar mai koyon magana,sarai ya gane yanda ta firgita sai kawai ya basar ya kara hade fuskarsa tamau yace

" Dukda abinda ya faru dake nasan you'll still eager to know much about me koh?"

Cikin dan tsoro Fahima tace

"No no Sir"

Daga mata hannu king yayi alamar tayi shiru ya cigaba

"Nasanki Fahima Aliyu,nasan nacinki da son bin kwakwafinki akan aiki kuma nasan kowanni irin hali zaki shiga bazai saki qara jajircewa akan aikinki ba and I like that,keep it up.Inaso ki cigaba da aikinda kika fara a kaina but this time around ya zama kanki da kasarki kike yiwa aiki ba don buqatar wasu ba"

Idonta ne ya tara kwalla jin abinda king yace,tho koh Zaki ya fadamishi tambayar da tayi masa ne dazu.Ama kuma menene bazata zubda mukamanta ba,tabbas yanxu ne ma take qara jin wani irin karsasshi akan aikin nata

"Ama yarona fah?"

Ta fada idonta na kawo kwalla,dauke idonsa yayi daga kallonta yace

"He'll be safe,kema zaki koma gidanki ki cigaba daga inda kika tsaya"

"Kana ganin zasu kyaleni?"

Tashi king yayi ya juya ba tareda ya kalleta ba yace

"You're free and safe insha Allah" yayi ficewarsa a dakin

************************
A durgukushe suke gaban wani k'aton bak'i mummunan mutum wacce halitta ta rikid'e ta chanza ta koma kamar wani dabba mafi muni da tsoro,zaune yake kan wata k'atuwar kujera wacce kafin ka hau ma sai ka taka wani steps uku dake jikin kujerar daga kasa.Kujerar da kanta abin tsoroce don kan zaki ne daga hannayenta sai kan mutum daga samanta an mishi ado da wani kyalle red and black kamar yanda komai na dakin yake bak'i sai ratsin ja²,dakin da suke kira da
'ROOM OF DARKNESS' (DAKIN DUHU)
Chapter 13 · 0% Book details