← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 95

Sashe 9

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

EPISODE 5️⃣
Ahankali yake bude idanunshi kadan kadan sama sama yaji ance “Son” dudda idanunshi akulle but ahankali bakinshi ya furta. “Momm” shafa mai kai matan tayi ta duko ta manna mai kiss agoshi cikeda tsantsan so tace “gani nan yarona open yourself Riyad no one is gonna hurt you again” gently yake bude idanunshi kafin ahankali ya saukesu akanta gently ya yunkuro ya shige jikinta kaman dan karamin yaro yace “Mommm” bayanshi ta shafa tana murmushi tace “meya sameka what happen? Who did this to you”? Murya chan kasa yace “wasu mutane wanted to kill me….” Kankameshi tayi sosai tace “babu wanda ya isa ya cutarmin dakai ko yadauki rayuwanka as long as ina raye, u are safe already ana investigating abun sai inda karfina yakare” takara kankameshi kaman dan karamin yaro tace “I love you Riyad kaine kadai sanyi idanuwa na”lumshe idanu yayi saikuma ya yunkuro yatashi daga jikinta yakalleta da muryanshi da bata fita sosai yace “Baba”? Kallonshi tayi saikuma ta sauke dan ijiyan zuciya tace “tashi kaje kai wanka ka shirya kafito ka gaggaisa da mutane idan zaka iya, sannan kaje kama Babanka addu’a a makwancin sa” dan runtse idanu yayi abin yamai ciwo yaso Ya sallaci mahaifinshi, fuskanshi Mom ta taba hakan yasa yabude idanunshi dasukai ja yakalleta murmushi kadan tamai tace “nasan yanda kakeson mahaifinka but he’s in a better place yanzu trust me, all abinda yake bukata awajenka is addu’a, jekai wanka za’a kawo maka kayayyakin dazakasa” gyadamata kai yayi agajiye yace “Mom please ke kikawomin banson hayaniyan kowa” tsayawa tayi ta kalleshi ahankali tace “tom zan kawo maka da kaina” dagoshi tayi yatashi tsaye ahankali yawuce bayin dake nan bedroom din, girman bayin yayi girman wani gida, wanka yayi yayi brush yadaura towel yafito yana kallon saman gadon inda tundaga kan takalmi har zuwa kan agogo an jeramai akan gadon tsaf dazai saka wasu kayan sarauta ne masu kyau sunsha aiki, anatse yake komi ya shirya cikin kayan da aka musu aikin royalty ya feffesa turare yadan juya yakallo kanshi amadubi yayi wani irin kyau na ban mamaki hulan dayasa yasake maidashi wani cikakken mutum bude kofa yayi yafito daga bedroom din wasu bayi ne ma’aikata a falon suna ganinshi suka duka dukansu. “Takawanka lafiya Yarima Riyad, taho a sannu dan kwalisa abin begen Sarauniya Maryama, barka da fitowa, Allah yakara maka lafiya, makiyinka fadawanka, duk wanda yaja dakai ya shirya yasha kasa….” Wucewa yayi fuuuu yafita danshi bayason wayan nan surutun nasu, da Munir yaci karo yana kokarin shigowa flat dinsu hakan yasa ya tsaya yahade rai kaman suna fada Munir yace “katashi, are you feeling better can you walk”? Gyadama Munir kai yayi yay gaba kawai, Munir yabishi abaya direct inda aka binne sarki yayi yana zuwa ya shiga wajen batare da an hanashi ba yayi shiruuuuu idanunshi sukai ja, almost everyday indai Mai Martaba baida wani uzuri saiya kirashi da daddare yaji yayake ina kuma yake, kullum cikin fada yakemai daya daina yawon kasashe yakan yawan cemai yanda yake gudunma gidan nan da alamu shine wanda gidan nan zai rike kuma gam, ana cewa sarakuna basu da lokacin yaransu shidai mahaifinshi nada lokacinshi, Baba ya fara koyamai business how to make 1naira yakoma billions, Baba guides him through everything, duk business dazai fara saiya kira Baba, sai Baba ya amince zai farayi, kuma bai taba takura mishi ba, hawaye yaji sun taru a idanunshi da sauri ya runtse idanun yana fuzar da iska dan baiso suma zubo but he’s deeply hurting, da ace yasan Baba zai rasu dabaiyi tafiyan nan ba, sosai yama mahaifinshi addu’a sannan yafito Munir yagani awajen da Kabeer dasu Shaibu yan uwanshi dukansu yajiki sukamai ya amsa sai kallonshi suke Kabeer yace “kasha magani kuwa you still look sick? Ko zaka koma ka kwanta ne”? Gyadamai kai yayi ahankali yace “nasha, I’m fine thank you” dannewa Kabeer yayi ganin yanda yakemai magana kaman alfarma yakemai dayake amsashi yadai daure yace “to mutafi fada” atare dukansu suka wuce fada, sauran yayyinsa da yan uwansa natamai hira da uhm a’a kawai yake amsasu cus gashinan ne kawai, gaida mutane sukayi sai yima Riyad gaisuwa ake ana kiran sunanshi shi baimasan ya akayi akasanshi hakaba dan baicika zama ba, su Waziri dai duk suna kallon komi, kowa yazo saiyamai gaisuwa amai yajiki, yanda ma ake kallonshi sai abin yasa yaji sabon zazzabi na nema ya lullubeshi.

Mom nazaune afalonta tana jan charbi ita dawasu kawayenta wanda suke mata Sarkin daga wasu garin dasuka kawo mata gaisuwa aka shigo flat din Matan Waziri ne da babban diyarta Haleema da ake kira da Lims, tana sanye da doguwan riga abaya black ta yana gyalen akanta, tanada tsayi da dan jiki kadan duka duka bazata wuce 24, 25 ba, tana shiga dasauri tawuce wajen Mom kafinma Mamanta tai gaisuwa tace “Mom ina kwana” takalli sauran matan wajen cikeda girmamawa tace “ina Kwanan ku” amsawa sukayi Mom tamata murmushi tace “Halima ba kina school ba yaushe kika dawo”? Mahaifiyarta tace “nima ganinta nayi agida da safen nan ta iso daga London wlh na aika driver yaje yakawota tunda taji rasuwan Mai Martaba hankalinta yakasa kwanciya” sosai Mom ke kallonta akunyace Haleema ta sunnar dakai Mom tace “school fa idan kikai missing exam ko test fa” Maman ta tace “project ma fa takeyi this month zasu gama komi da komi” babu wasa kan muryan Mom tace “kibi first available flight ki koma school gobe kinajina” gyadama Mom kai tayi ahankali tace “to Mom” Mom bata sake cewa komiba tacigaba da magana da manya, ahankali Haleema kebin dakin da kallo gabanta na faduwa addu’a take Allah yasa suhadu ta ganshi, Allah yakawoshi side din nan dudda tasan ba lallai yadawo ba barinma yaji da baki adakin amman tasan inhar yana gari yafi zama wajen Mom da bangarensu na samari.
Kallonta Mamanta tayi tace “tashi kije wajen su Batul mana” juyowa Mom tayi takalleta tace “tashi kije wajen yan uwanki” batai musu ba tashi tayi tawuce tafita Matan Madaki tabita da kallo tace “yarinyar akwai natsuwa ga kunya ga kawaici ta dace da Riyad sosai yanda shima baida maganan nan” wani kalan dadi Matan Waziri taji Mom tai dan murmushi batace komiba.

Ahankali take tafiya ita kadai tana danna wayanta kamshin turaren dataji yasa ta dago kanta dasauri Riyad tahango yafito daga fada yana shigowa nan compound din Mom wlh kusan duka yaran sarki tasansu da yaran yan uwa dan afadan nan aka haifeta anan ta girma bata taba ganin yaro mai kyau da farin jini da aji irin Riyad ba kap gidan nan babu wanda yakaishi kyau, ga tsayi ga gayu ga jidakai ga miskilanci ga kudi kudinshi na kanshi bawai kudin Baban su ba dan babu wanda yakaishi kudi a yaran sarki, gashi Mai Martaba na sonshi, ga kakanshi na bangaren Mom Attorney General yafi kowa tsatso mai kyau da gata ayaran sarki.

Faduwa gabanta yayi sosai amman tadaure ta tsaya awajen jikinta har bari bari yake, tahowa yayi wajen batare daya kalle inda takeba zai wuce dasauri tace “Yarima Riyad!” Tsayawa Riyad yayi chak batare daya juyoba dasaurinta Halima taje ta gabanshi ta tsaya adan kunyace tace “ina yini ya hakuri?” Dan kallonta yayi trying to remember waye ita, shifa wasu kannin nashima ba saninsu yagamayi ba dan baya shiga lamarin gidan nan baison komi game da sarautan, dauke kanshi yayi ganin yanda take murmushi tana kallonshi, kaman ance dole yayi magana yace “who are you”? Wow the way he talks is super adorable, da kyar ta iya controlling zuciyanta dake neman fitowa ta danne kome takeji tace “Haleema” dan kallonta yayi irin kallon okay but still baigane ta ba and he doesn’t care din nan yajuya zai wuce dasauri tace “Ya Riyad sabida kai nazo gobe zan koma school” dan tsayawa yayi wannan karan yajuyo kalleta da kyau shifa har yanzu bai santaba and sabida shi tazo? Akan wani dalili? Are they related in anyway? Infact baida karfin bude baki ma yayi all this questions hakan yasa yadan tabe baki yace “thanks” kawai yawuce ya shiga flat din Mom……

Jin akwai baki abangaren Mom yasa yajuya yagazaya ta baya yashigo gidan yaje ya kwanta.
Chapter 9 · 0% Book details